← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 58

Sashe 6

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*11*
Babu yadda na iya haka naja jikina cikin tsananin tsoro nabar cikin ɗakin namu direct ɗakin umma na shiga sabida naga toilet ɗinmu ummi ke alwala acikinsa nima alwalan nayo tare da zuwa kusada amira na tayar da sallah ina idarwa nai addu,ata na shafa dan harta niman tsari da dukan ya Hydar seda na roƙa sannan nai saurin tashi tare da nufar part ɗinsa dan bani son ya dawo ya iske ban jeba da sauri na karasa shiga cikin falon nashi samun waje nai akan center carpet ɗin falon na zauna tare da rafka tagumin zaman jiranshi.

         Nafi ƙarfin minti goma a zaune dik raina ya ɓaci amman babu ɗuriyansa bare alamunsa, bini-bini naja tsaki tare da duba agogon falon cikin kallon danake idona ya hango wani ɗan frame ɗan ƙarami a gefen kujerarsa da sauri naja jikina tare da nufar inda na hango frame ɗin cikin sauri na miƙa hannuna na ɗaukesa hoton wata budurwa nagani babu laifi kyakykyawace ta ajin farko daga ganinta kasan ta fito daga gidan masu shi kuma ba wata babba bace dan ko zata girmeni ma baifi da shekara guda ba gaskiya babu laifi tana da kyau na fitar hankali wani ɗan rubutu naga anyi daga gefen frame ɗin wanda sekai da gaske zaka gane mai aka rubuta ajikinsa da azama nakai idona ga rubutun gani nai an saka  _my beautifull wife_  iya abinda idona yagani kenan ajiki.

Dariya na sauke tare da furta "oh lallai wannan kin cika ƴar baiwa da kikai wuff da zuciyar wannan bakin mugun".gum nai saurin rufe bakina tare da saurin komawa na zauna jin ƙarar ƙofar falon alamun ya shigo kenan.

Sallam yay cikin ƙasa da murya wanda ba lallai mutum yaji miya cebama nima ban amsa mashi yadda zejiba na kama bakina na tsuke tare dajan hijabina na rufe har tafin ƙafata bai tsaya a falon ba direct bedroom ɗinsa ya wuce.

Minti kaɗan segashi nan ya fito sanye da cofeen jallabiya mai yankakken hannu baƙa ramin kyau taima white skin nasa ba.

Zama yay akan É—aya daga cikin seatern falon tare da É—aukar remote control a hannunshi yana serching channel.

Batare daya kalli side É—in danake zaune ba, seda naga zaman ya fara isata ga sanyi yana damuna yasa nai saurin kai duba na garesa boll yake kallo hankalinsa kwance.

"Ya Hydar gani fa tun É—azu nake jiranka" nafaÉ—a muryata kamar zanyi kuka!

Kamar baiji ba haka yay min banza yacigaba da kallonsa.

"Ya Hydar maganafa nake"! nafaÉ—a cikin tsananin jin haushinsa.

Juyowa yay ya kalleni da narkakkun idanunsa masu fisgar hankalin ma,abocin kallonsa batare daya ɗauke idonsa akaina ba yace "Zonan" jan jikina nai kaɗan na ƙarasa gabansa daf da ƙafafunsa waɗanda suke zube bisa carpet.

Tsiramin ido yay yana kallona kafin yace "Ɗazu mina ce maki?" rau-rau nai da idona batare dana ce mashi komai ba se can kuma nace masa "Dan ALLAH kai hakuri wallahi aikine yay min yawa" naƙarasa faɗi ina murguɗa bakina gefe guda.

"Dan kin rainani shine bara kimin abin da na sakaki ba dan tsabar baki da hankali to wallahi se ranki yayi mugun ɓaci yau ɗinnan" yakai maganar kamar bashi yay taba saboda yadda muryansa tai ƙasa sosai.

"Bafa haka bane nagaya maka wallahi aiki ne yay min yawa kasan fa umma bata nan ga yara suna makaranta" nakai maganar cikin jarumta.

Matsowa yay sosai gareni har ƙafarsa tana haɗuwa da jikina da sauri naja baya tare da saka hannuna nai tagumi ina kallonsa.

Bantaɓa ƙare ma sa kallo kamar nayau ba gaskiya ya haidar baƙaramin kyau ALLAH ya basa ba lallai wannan dole ma yay wulaƙanci da jin kai dik da dai ban misalta yadda kyan nasa yakeba amman nabarwa makaranci ya ƙisma da kansa domin kyansa shi akewa laƙani da asalin kyau ɗan gaske mai shiga rai da zuciya da kwanciya a ɓargon jiki.

"Ki wuce bedroom na ki wanken tiolet malama kinzo kin sakani agaba da wannan banzan fuskan naki" yana kaiwa nan naji wayansa taÉ—auki ringing! wani shu'umin smile ya saki akan face É—insa tare da É—auka yana karawa a saman kunnensa.

Tsaki naja araina ina cewa "wlh bazan wanke banÉ—aki da wannan magariban ba salon wani aljanin ya shigeni abanza da wofi.

Banajin mi suke faÉ—a a wayar amman daga gani maganar love sukeyi duba da yadda naga yanata lumshe idanunsa.

Tsaki naja kaÉ—an a raina sannan na mike na nufi hanyar waje.

"Ke dan ubanki ina zakije?" na tsinci muryarsa akaina yana maganar.

Batare dana juyoba na tsaya cakk ina faman tura bakina gaba.

"Ke zonan" nakuma jin muryarsa akaro na biyu yana min magana.

Jan kafata nai tare da nufar wajansa ina faman tura bakina gaba.

Tsugun nawa nai tare da cewa "nidai kayi hakuri bazan iya wankin bayi yanzuba darefa yayi" nakarasa fadar maganar ina tura bakina gaba kamar zan saka kuka!

Ƙaro handsfree ɗin wayar yay tare da ajeta agefensa sannan ya dubeni "FATIEMAH! yafaɗa dawani irin jan sunan kamar shi ya raɗamin shi batare daya jira mi zance ba ya cigaba da cewa.........

"Miyasa kike da taurin kai ne?" ya ƙarasa maganar cikin wani irin yanayi "nifa yaya ba taurin kai nai maka ba iya gaskiyata na faɗa" kiff ya kaimin duka a gefen fuskata "dan uba nki waike kam wace irin banzar yarinyace ne?" dan bakida mutunci ina magana kina magana ni sa,ankine!! jada baya nai tare da saka hannu na dafe wajan ina sakin wani irin kuka.

Da sauri na tashi tare da barin falon aguje na nufi waje ina ihu!

"fatie!! fatie! fatie!!! inajin yana faman kiran sunana nikam nai mashi banza tare da fita daga falon aguje!!

Abakin famfon wajan wurin na tsaya na wanke fuskata sannan na nufi cikin gida ina ƙunshe dariyar iskancin dana shuka masa ai wallahi babu gardin dazanwa wankin banɗaki yanxun nan haka kawai salon nabar umma da yawon gidajen masu magani.

Da sauri na faɗa cikin falon umma ina haki cikin sauri na gyara nutsuwata tare da ƙarasawa cikin falon ina cewa.

"La MOZA yaushe kika dawo?" dayake yawanci sunan danake gayawa umma kenan idan ina cikin nishaÉ—i.

Kallona umma tai tsaff kafin tace "kekuma daga ina haka?" "au umma basu gaya maki ba daga fa part ɗin ya hydar nake nai masa gyaran ɗakinsa" nakai ƙarshe ina zama agefenta hannuna na miƙa gefenta na ɗauki agwaluma guda ɗaya ina kokarin ɓareta.

"Sannu uwata keki ka aiken da zaki daukarmin baki tambayenba" ALLAH ya baki hakuri moza tuba nake" nakai maganar ina sakin dariya.

Danni yau komai za,aimin baxanji haushi ba coz abin da ABDUL yagayan É—azu shiya barni cikin wannan nishaÉ—in.

Umma ce ta dubeni tare da cewa "jaririya yau abinda kikaimin naji dadi ALLAH yay maki albarka" ameen umma" nabata amsa ina kai agwalumar bakina bayan na bareta.

"Yawwa nace ranar asabar zamu tafi abuja zaku zauna anan ne koko zakuje gidan zainab?" haÉ—e raina nai tsamm "umma mezaki acan É—in?" kayan lefen ALIYU zamu kai gidan minista kinsan bikin fa sauran sati biyu É—azu ake gaya mana" au haba amma umma ko labari?" dariya umma tai tare da cewa ai labarinne bai zoba tukunna amman yanxu ai gaya nan kinji.

"To ALLAH ya sanya kairan"

"Ameen"

"Umma zamu zauna anan É—in kawai"

"Toshikenan ALLAH yakaimu ai yau sauran kwana biyar ma"

Haka dai mukaita hirarmu muda umma gwanin sha,awa har abba ya dawo yau abba harda tsokana ta.

Ban bar É—akin umma ba se wajan goman dare.

Dakinmu na koma dik su ummi sunyi bacci nima sallah nai tare da kwanciyata.

Washe gari ban fitaba seda na tabbata daya fuce office sannan nai wuff naje kicin nai abin da zanyi na bar kicin É—in.

Tunda yamma umma ta akeni gidan anty zee naje na kai mata wasu kaya anan muka hadu da ABDUL muka kuma tattaunawa har bayan magariba sannan nayo gida.

Yauma seda nasha faÉ—a wajan umma amman nikam ban damuba sabida burina ya kusan cika

Yau kusan kwana uku kenan da faruwar komai muna waya sosai da ABDUL harda ma mahaifiyarsa da ƙannensa.

Kuma sosai muke maganar kawo kudin aurena yace sunata shirye shirye a bangaransu.

Ya hydar kuwa haryau naki yarda mu hadu dashi amman shi ina ganin ma ya manta dani tunda ta hidimar auran sa yaketayi dan yau yana kano ne gobe yana abuja duk haka yake wannan zaryar.

Yau asabar tun safe umma ta shirya ta yakasai ta wuce sabida zasu tafi da matan su alhaji ƙarami gida ya rage sauran mu da abbanmu dan shima angon ya wuce tun jiya ƙilama kuma se bayan bikin nasa zezo kokuma yama tafi shikenan oho masa tunda naga ya dauki manyan jakunkunan sa tare da kayayyaki sosai harsu hanif naga ya kira ya babbasu abubuwa harda kuɗi da yawa sannan ya rufe part ɗin nasa.

Harkokin mu mukeyi acikin gida kuma bama wannan faÉ—an kamar da munyi waya da umma wajan sallar magariba lokacin harsun sauka daman umma a bangaren mama take sauka domin momy bata kaunarta shiyasa bata sauka anata bangaren.

Kwanan su biyu suka dawo anan umma kece mana an saka biki sati mai zuwa zaro ido mukai muna mamaki lallai abin se son barka nan umma ta zauna tana bamu labarin dukiyar da aka lafta alefen.

Hoton less É—in dinner umma ta nuna mana tace gobe zata bawa anty zee taje kasuwa ta sai mana.

"Ni dai umma banda ni wallahi bana so nifa baxani ba gidan iya zani na zauna ko gidan anty zee" akanme baxaki ba kinsan abbanku ma baxe bari ba ko dan iskanci dik yan uwanki zasu taru zakice baxaki jeba" shuru nai mata amman araina na kudiri aniyar wlh babu inda zani ana igobe zasu tafi zan gudu gidan anty zee.

Danni bana son wulakanci shiyasa nake gujema inda ake yinsa.

Kwanci tashi babu wuya wajan ALLAH yau alhamis tun safe su umma suke shirinsu na tafiya har É—inkunan mu sun karbo nidai da ido nake kallonsu.

Ƙarfe goma saura nabi ta bayan kofa nabar gidan bayan na saka kayana a yar akwatina.

Seda naje gidan anty zee sannan mukaiwa umma waya lokacin suna tare da abba nan umma taita faÉ—anta tare da cewa senaci ubana idan ta dawo.
Chapter 6 · 0% Book details