← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 58

Sashe 28

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baccin minti talatin kawai ya samu ƙarar wayarsa ya farkar dashi cikin zafin ciwon kai yaja tsaki tare da ɗaukar wayar tasa dake jikin bedside drower duba wayake kiran nasa yayi ganin abokinsa najeeb yasa ya ɗira daga kan gadon.
Jikinsa sanye da singlet baƙa irin ta kakin soja se farin 3qrt daya tsaya masa iya ƙwaurinsa.
Toilet ya shiga ya wanke fuskar sannan ya koma gaban gadon ya zauna ya É—auki wayar ya shiga kiran najeeb É—in tunda wanda najeeb É—in yay masa ya katse.
Sunkai good 20 minutes suna tattauna maganar auren najeeb ɗin da,ayi nan da wata biyu sannan ya katse wayar ya miƙe.
Cikin sauri ya zira silifas a ƙafarsa ya nufi hanyar waje.
Bai tsaya a faloba kai tsaye ƙofar fita ya nufa tare da ɗaukar hanyar part ɗin momy yana addu,ar kada ALLAH yasa abinda yake tunani bai tabbata ba.
Aikam yana tura ƙofar ya hangota kamar marainiya ƙudundune cikin tsakiyar cinyar da alama ma ko kuka take! yamutsa sumar kansa yayi da hannunsa tare da jin babu daɗi cikin wani irin sanyin jiki yaja ƙafarsa zuwa gareta durƙusawa yayi gabanta batare datasan yay hakan ba ya zuba mata ido yana kallonta zuciyarsa na zafi najin kukanta!
Cikin kukana naji saukar hannun mutum a fuskata da sauri na ɗago idona wanda yake sharɓe sharɓe da hawayena na ɗorasa akan fuskarsa wanda yake tsugunne a gabana da alamun fushi agaresa.
Cikin daƙilewar murya naji yace.
"Me akai maki kikewa mutane wannan kukan kamar wadda akama duka?"
Matso wani hawayen nayi tare da kallonsa sosai.
"Yaya yunwa fitsari zazzaɓi tsoro duk su suka kamani wallahi yaya tunda ba zauna anan babu wanda nagani anan ɗinfa".
Naƙarasa ina kuka!!
Sunkuyar da kansa naga yayi kafin kuma naga ya miƙe cikin sauri naga ya shiga ƙofar hannun damarmu.
Batare dayamin magana ba.

Momy zaune akan tumtum na pillow se maryam a gefenta wadda take faman zuba abinci mai rai da lafiya acikinta.
Na'eem da Raudah yaran momy ƴammata da basuyi aureba kwance a kan ƙafarta kowaccensu da waya ƙirar iphone 11pro a hannunsu wanda da alama charting sukeyi cikin farin-ciki babu damuwa ko kaɗan atare dasu kana ganinsu kaga ƴan madara ƴan ajin tubarkallah top class ƴan gayu ajebotar.
Kamar anjefoshi ya faɗo ɗakin yana muzurai cikin ƙufula.
Ko sallama baiba ya tsaya agaban momy yana watsawa su rauda harara.
Cikin sauri momy ta É—ago tana binsa da kallo kafin tace.
"To dogari meke tafe dakai?".
Kallo É—aya ya watsawa su rauda tare da kauda kansa gefe ya furzar da zazzafan hucin zafi.
Da sassarfa naga sun miƙe tare da shigewa bedroom ɗin momy.
Hatta ita ma maryam É—in yana juyowa ta mike tabar wajan yarage dagashi se momy.

*50 - 51*

Cikin kuzari ya rage tsahonsa a gaban momy tare da É—ora hannunshi akan tumtum É—in da momy ke kai ya kafeta da jajayen idanunsa yana kallonta dasu.
Cikin dashewar murya mai cike da tarin ɓacin rai ya dubeta.
"Hajiya kiyiwa ALLAH da manzonsa kitayani riƙon amanar da aka damƙa min,hajiya! kituna da cewa ɗana kowane idan har akaiwa rauda ko na'eem ko hafsa ko zubaida ko mamy nasan baxakiji daɗiba tokema mai yasa zakima ƴar wasu haka?"
Yakai maganar yana tsareta da ido.
"Hajiya kituna da maryam da fatiemah duk a yanzu matana ne to maye na zaɓar ɗaya kibar ɗaya tun kafin akai ko'ina har kin fara ban bantasu,yanzu kun shigo nan kunbar ƴar mutane awaje ni wallahi momy gwara na tattara na tafi da ita lokojan dan bazan iya kallon abba da idona ba idan har wani abu ya samu gudan jininsa....."!
Yakai maganar yana kallon idanun momy.
Cikin mamaki momy ta saki baki da hanci tana binsa da kallo saka hannunta tayi tana goge idanunta kafin ta sami damar magana cikin firgici.
"ALIYU! takira sunansa a karo na farko a rayuwarta.
ÆŠaure rai tai sosai sannan ta cigaba da cewa.
"Wallahi! tallahi! har abada bazan taɓa son wannan yarinyar ba kai barima kaji bada ban ubanka yay min kurari da igiyar aurena ba da tuni yanxu maganar saki ake ba wannan ba nikuwa mai yaymin zafi haɗa zuri,a data Aisha".
Takai maganar tana jan numfashi sama sama.
Kallon mamaki yakebin mahaifiyar tasa dashi batare daka gane a wani yanayi yake ba.
"Hajiya ALLAH ya huci zuciyanki, awani É—akin zata zauna?".
"Bangama tunanin hakan ba tafara zama a B.Q kafin nagama shawarata".
Zaro manyan idanunsa yayi cikin É—umbin mamakin LAFAZIN mahaifiyar tasa sannan yace.
"Hajiya B.Q fa?" cikin maids ɗin gidanman ina hajiya kiyi haƙuri iyalina bazata zauna anan ba kiyiwa ALLAH bani ba kirufawa mutuncina asiri kijanye wannan LAFAZIN naki hajiyata".
Yakai maganar yana jin zuciyarsa babu dadi akan maganar hajiyar.
Tasan halin É—an nata da kafiya da taurin kan tsiya dole seta rage takurarta agabansa idan tana son gudanar da komai cikin sauki.
Murmushi ta saki tare da cewa.
"Kardai kacemin kafara sonta kenan?"
Tajefo masa tambayar babu zato.
KaÉ—a kafaÉ—unshi yayi alamun ko ajikinsa sannan ya saki wani shu'umin murmushi.
"Hajiya kin taɓa ganin mutum yaƙi jininsa ai ko babu so akwai ƙauna ta jini a tsakanina da ita".
Yana kai maganar ya miƙe tare da cewa.
"Bara na kaita wancan É—akin na kusa da danasu raudah hajiya ko abinci baki bawa yar takiba".yafaÉ—a yana sakin dariyar tsokana.
'Daukar pillow tai ta jefo masa tana faman masa masifa kamar zata ari baki.
"Wallahi sena miƙe tsaye dan naga alamun baba yafara zarmewa babu wani ƙaunar jini kota hantace sena raba ni ba ruwana, dannasan halin baba matukar yafara son yarinyar nan kashina ya bushe".
Momy ita kadai keta faman zubar gadon wannan maganar kamar wata zautacciya.
Cikin yanayi na nishaɗi ya ƙarasa falon sabida yadda momy ta basa dariya ita watakan da gaske take bata son fatimah shifa yanzu abinma dariya yake basa lallai da sauran kallo a nan gaba.
Gabanta ya ƙarasa har yanzu tana raɓe a inda ya barta batayi ko motsiba.
Gyaran murya yayi wadda ta jawo hankalina garesa na É—ago ina kallonsa tare da jiran daga garesa.
"Taso ki biyoni" abinda yafaɗa kenan naga ya nufi cikin falon ƙofar ƙarshe ya tura wadda daga ita se wadda zaka futa daga falon baki ɗaya.
Shiga cikinta yayi wanda nima ya bani damar bin bayan nashi.
Babban ɗakine mai dauke da toilet ɗinsa aciki dannaga ƙofa wadda nake da tabbacin ta toilet ɗince se ƙatuwar katifa tare da wadrov a gefenta amman babu madubi.
Iya abinda ke cikin É—akin kenan.
Ja yayi ya tsaya ajikin wadrov É—in ya ji ngine jikinsa da bangonta yana kallona na minti É—aya sannan ya kauda kansa gefe.
Adaƙile naji saukar amon muryarsa.
"Ga É—akin ki nan ki samu kiyi abinda zaki kafin su kawo maki abinda zakici".
Yafaɗi hakan yana ƙoƙarin juyawa ya fita daga dakin.
Mayar da hawayena nayi sannan na É—an biyosa a baya.
"Yaya hydar zazaɓi ke damuna, sannan kuma nace maka ina su anty zee kaimin banza ko basu ƙarasoba".
Kamar bazece komai ba naga ya ƙarasa gaban ƙofar tare da saka hannunshi ya kama handle ɗin sannan naji yace.
"Idan ma zaki nutsu ki nutsu idan banda shirmanki waye ze rakoki ai ko kaza baza,a haɗota dake ba bare kuma mutum, keda ganin su ummi harse kinyi hankali, ga gayanki can driver ya kawo zansa ashigo maki dasu and kuma bana buƙatar inga ƙafarki koda a bakin gate ne wallahi kikai hakan sena ɓallaki"!
Yana kaiwa nan yaja handle É—in tare da ficewa daga É—akin.
Mamaki fargaba takaici baƙin ciki sune sukai min caa!
Da sauri naja jikina na faÉ—a kan katifar gwanin tausayi na rungume pillow ina kuka!!
Ashe daman wayo umma taimin dan kar na É—aga hankalina yasa akaimin shigo-shigo babu zurfi har aka saka anty zee tazo ta kwana?
Ashe daman duk hirar da umma takeyi da anty zee danna zata zasu biyoni ne?
Wallahi inda nasan hakane da tuni zakara yabani sa,a nayi gidan iya wani haushi ne ya kamani watakan horon daza,amin kenan shikuma wannan É—an rainin hankalin wai senai hankali zani gida.
Juyawa nai ina kallon É—akin nan danan naji kewar Æ´an uwana tayi mugun kamani"wayyo ummi amira"nafaÉ—a a fili.
Ƙarar buɗe kofar danaji ita ta dawo dani daga tunanin danake ganin ƴar budurwa agabana tana turo kaya a babbar bags ɗita ya bani tabbacin maganar dayay min gaskiyace.
"Anty gashi nan inji oga" cewar yarinyar tana rissinamin.
Batare da nai far,aba nace mata"to" tare da juyawa cikin jin haushin kowa....!!

Fita tayi wanda naji ƙarar! buɗe ƙofar tata ko kallon kayan banyi ba na miƙe zaune tare da cire hijabin jikina na cire ɗankwalin kaina nai zaman dirshan akan katifar ina sakin kuka! mai fitar sauti.
Ƙarar ɓuɗe ƙofar na kuma ji da sauri na ɗago kaina ganinsa nayi ya juya baya yana rufe ƙofar yasa nafara ja dabaya.....!!

52-53

Jada baya nasomayi ina faman raba idona ni duk atunani wannan maganar ta ɗazuce ta sakasa jin haushi yazo ya huce takaicinsa akaina amman unexpected sena gansa akaina a tsaye batare daya saki muryanshi ba naji yace,"Malama dallah matso kici abinci ga drugs nan kisha maza kafin na dawo kiyi sallah" yana gama faɗamin haka naga ya dire ledar dake hannunsa ya fuce daga cikin ɗakin, ɗan zamo da jikina nayi tare da ɗaura ɗan kwalina sannan na jawo ledar cikin zaƙuwa nasoma kai abincin cikina wanda babu ko tamtama na siyowane cikin mintinan da basu wuce biyarba nagama ci sannan najawo ledan drugs ɗin na ɓalla gami da watsasu bakina na kora da ruwa miƙewa nai tare da shiga cikin toilet ɗin dake manne acikin ɗakin babu laifi yanada ɗan girmansa se ƙaramin towel ajikin ƙarfen, haka na tari ruwa a famfo nasoma alwala ina kammalawa na fito waje na shimfiɗa sallaya na tayar da sallah ban tashiba seda naji ana kiran sallar isha'i sannan na mike gami da mayar da ita, bayan na idar nai addu,a na shafa sannan na koma na ƙara ɗaukar ragowar take away ɗin naci sannan na haye kan katifar na ƙudundune, wallahi wani irin tsorone ya kamani amman babu yadda zanyi haka na rufe ilahirin jikina naja pillow na kwanta sabida yadda naji gidan yayi wani mugun shuru.
Chapter 28 · 0% Book details