Sashe 27
Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*48 - 49*
Cikin nutsuwa motar tamu ta kutsa cikin harabar gidan wanda yake ɗauke da motoci birjik ga kuma irin manya manya dogayen bishiyu masu tsananin kyau, dai dai ta parking yayi daga gefe kafin ya kashe motar cikin lokaci kaɗan kurtun sojan ya zagayo aguje tare da buɗe side ɗin da ya hydar ike zaune sannan yaja baya ya ƙame.
Dazafin nama nima na saka hannu naja marufin gefen danake tare da fitowa waje miƙa nayi tare da salati sannan na godewa ALLAH.
Rufe idanuna nayi gam tare da karanta addu,a bayan na gama na roƙi ALLAH daya sadani da dukkan alkairin dake wannan gida yakuma yimin tsari da sharrin cikinsa.
Wannan kuma bawai wanine ya sanar dani hakan ba face mahaifiyata.
Ina bude idanuna naga su ashe har sunyi nisama sunkusan kaiwa part É—in tsakiya wanda nake tunanin shine na momyn.
Cikin yanayin gajiya nima nake ɗaga ƙafafuna waɗanda sukaimin tsami sabida zama tare da nufar inda naga sunyi.
Adai dai bakin É—an matsakaicin gate É—in daze sadaka da cikin part É—in na sake tsayawa wannan karon addu,a nayi mai tsaho tare da neman tsarin ubangijina akan zamana da momy sabida yadda naji gabana ya faÉ—i.
Kuma cikin ƙudurar ALLAH ina gama addu,ar bayan nashafa naji na sami nutsuwa acikin jikina da zuciyata.
Cikin azama naja ƙafafuna na nufi cikin nima ina godewa ubangijina domin dama indai bawa ze roƙi Allah to shikuma ALLAH ze amsa masa sedai idan bawan mai sakacine tabbas yazama dole na yarda son jikina in miƙe indiga ibada ina kaiwa ALLAH kukana domin shikadaine ze kawomin ɗauki a hannun momy dama sauran dukkan lamarina.
Ganin wata babbar ƙofa mai adon zaiba a buɗe ya bani tabbacin nance ƙofar dazata sadaka da ainihin cikin ɓangaren batare da wani duhun kaiba na ja jikina har zuwa bakin kofar tare da saka ƙafata ta dama nai bisimillah sannan na shiga.
Ƙatuwar harabace mai ɗauke da fulawowi masu kyau wanda naga ƙofofi a ƙallah zasuyi huɗu da sassarfa na ƙarasa ƙofar farko ina neman inda zanyi na shiga falon tunda ni duk a tunanina ba haraba zan tarar ba falo zan tarar amman se aka samu akasin hakan.
Gashi kuma ni tuni na nemi ya hydar na rasa sam nakasa gane inda suka shiga domin kuwa ni sun ɓacemin ɓatt!
Tura ƙofar farkon nai da sauri kuma na saketa nayo baya sabida yadda naga tsakar gida dawasu ɗakunan dana kasa gane kona miye.
"Baiwar ALLAH lafiyarki kuwa?"
Dasauri naÉ—ago kaina ina duban wadda taimin wannan maganar, dattijuwace dan daga gani ba yarinya bace dan ta manyanta amman kallo guda zakai mata kasan aiki ma take ta taso gareni.
FaÉ—aÉ—a far,ata nai tare da saurin tsugunnawa.
"Baba dan ALLAH ya hydar nake nema ban san inda yay ba".
Cikin mamaki wadda na kira da baban tace.
"A,a Æ´arnan kardai kice uban É—akin nawa har yashigo gidan".tafaÉ—a cikin farin ciki.
"Ai tun ɗazu muketa taya hajiya girkin uban gidan namu kice har ya shigo shida hajiyar,amman dai ke baƙuwace bakisan takan gidan ba?"
Ta kuma jefomin tambayar a karo na biyu?
"Eh ni baƙuwace yau na biyosu to kuma nazo sena nemesu na rasa".
"Ayya ALLAH sarki jikata kinga nan kicin ne da store anan duk ƴan aikin hajiya momy muke zaune,waccan ƙofar ta yamma itace ta momyn da yaranta waccan ta tsakiyar kuma itace ta alhaji idan yana gari.waccan ta hagun kuma itace ƙofar Aliyun shida matarsa inda ya taɓa.zama farkon aurensa kafin subar gari amman yanzuma naji ance zasu ɗan zauna anan ɗin kafin matar tasa ta haihu.
Sukuma sauran matan alhajin suma part É—insu yana daga gefen namun amman sekin futa waje haÉ—e yake dana mazan gidan".
Takai maganar tana min murmushi
"To jikata maza fito na sadaki da ƙofar ɓangaren hajiyar kafin muzo kwasar gaisuwa".
TafaÉ—a tana fita daga cikin kofar binta nayi abaya ina jinjina maganar matar amman kuma daga gani tana da kirki sedai magana datake da ita sosai.
Tun kafin ma mukai ƙofar momyn na hango giftawar ya hydar kuma kamar yana saurine se can kuma naga ya nufo inda muke.
Cikin sauri wadda na kira da baba ta ƙarasa gabansa.
Rissinar da kanta tayi tare da furta.
"Yallaɓai barka da zuwa ya hanya?".
Ga mamakina senaga ya saki fuskarsa yana cewa.
"A,a baba harira sannu da gida ya aiki dafatan nasameku lafiya?".
"Lafiya ƙalau ɗan albarka munata ganin hidima mungode ALLAH ya ƙara ɗaukaka....!! ya katseta ta hanyar ɗaga mata hannu alamun tabar gaisuwar.
Juyowa tai ta dubeni.
"To jikata gama Alhaji alin nan kya karasa tare dashi kinji ko"
Murmushi na sakar mata jin yadda ta shiga raina tafarar É—aya sannan nace.
"Tom kakata nagode senazo cin tuwo".
Nakai maganar tare da jan ƙafata na taka gabansa.
Seda baba harira ta ƙule sannan naga ya dubeni.
Tare da ɗan rage tsahonsa gabana cikin wata munafukar murya wadda tai ƙasa sosai yacemin.
"Ina kika tsaya?"yafaÉ—i maganar a dake tare da shan kunu.
"Kawar dakai na nai gefe cikin basarwa nace.
"Natsaya mu gaisa da waccan tsohuwar ne sabida naga suna aiki yasa naje nai musu sannu".
Na tsinci bakina da faɗin hakan sabida nasan nace masa ɓata nai yanzu seya yarfani.
Tunda ta fara magana ya tsirata da mayun idanunshi yana bin bakinta dasu yana kuma jin yarinyar tashi ɗaya ta burgesa danshi arayuwarsa baya ƙaunar wulaƙanta ɗan adam musamman babba wanda ya girmeka shiyasa data ce masa hakan yaji tayi mugun burgesa ba kaɗan ba.
"Kin kyauta maza wuce muje".
YafaÉ—a tare da wucewa bayana ya sakani a gaba har cikin kofar wadda ta kasance kamar ta ruwan glass.
Adai dai bakin step ɗin dazaka taka kashiga ƙaton falon naja na tsaya sabida wani sanyi danaji har cikin ɓargona.
Juyowa nai domin na tambayesa su anty zee aikuwa karaf muka haÉ—a.ido dashi yawani matso gaf dani kamar ze hau gadon bayana.
Tsareni yayi yana bina da kallo fuskarsa babu walwala nima basarwa nai sannan na dubesa.
"Yaya su anty zeefa?"
Matsowa yayi kamar ze haÉ—eni tare da É—ora hannunshi a gefen danake tsaye tare da bina da kallon dana rasa na miye.
Cikin fargaba naja baya kaɗan ina raba idanuna gefe tare da yin ƙasa da kaina.
"Fatie.....!naji yakira sunana cikin ƙasa da murya sosai, baijira cewata ba ya ɗoramin"fatie wallahi inda ba abba ne ya haifekiba senace a ƙauye umma ta ɗaukoki,miyasa baki san yadda zakinawa mutum maganaba,nidai kinga ba mazauni bane bare na dinga karɓarki wajan momy sabida haka ya kamata ki gyara tun wuri".
Yakai maganar yana É—ora hannunsa akan kirjinshi ya tokare.
Cikin sanyin jiki dana zuci na ɗago ina binsa da kallon tsana jin yadda wani haushinsa ya kamani waishi ba mazauni bane bare ya karɓeni awajan momy,sekace jaka aka ɗauko musu.
"Indai ALLAH ze kareni ai bana jiran karbar waninsa kayi ƙoƙari wajan zuga momynka ta kasheni kotaimin illa tanan ne kaɗai zan gane cewa kuɗin maƙiyana ne"....!!!
Ina kaiwa nan na wuce fuww nabarsa a wajan a dashe.
Babban falone wanda ya haÉ—a manyan kujeru babu abinda bai haÉ—aba na dangane da kayan more rayuwa da jin dadi.
Tsakiyar center carpet naja na zauna tare da ɗora hannuna a kuncina na zuba tagumi sabida da alama.anty dasu ummi basu ƙarasoba.
Shikam cikin mamaki da wani irin yanayi yaja ƙafarsa yabar wajan baima shiga part ɗin momyn ba kawai seya koma da baya ya nufi nasa part ɗin.
Mamaki fal ransa yake nanata maganarta acikin zuciyarta tome take nufi dasu maƙiyanta ne?
Shikam ko a farce baya jin sonta a matsayinta na mata garesa sedai yana jin sonta a matsayinta na ƙanwarsa.
Koda kuma ace É—aukota yayi daga gaban abba ya kawota nan baxe bari aci zarafinta ba,bare kuma yanxu datake a matsayin matarsa wanda hakkinta da dukkan wani nauyinta ya rataya a wunyansa tabbas baxe bar wani abu marar kyau ya gifta garetaba sedai idan baya wajan.
Shidai akankin kansa idan tai masa ba dai dai ba ze hukuntata hukunci mai zafi amman bai yarjewa wani yaci zarafinta ba.
Yama kuma.gayawa momy É—azu kafin ta shigo yace komai tai a gaya masa shidai baya son aci zarafin ta sabida amanar ALLAH ce awajansa dakuma amanar zumuncin ALLAH dakuma ta aure.
Wannan furucin daya ma momy ɗazu kafin ya fito shine ya harzuƙata hartaji haushinsa ta miƙe taja maryam ɗaki suka bar falon.
Da wannan tunani ya karasa part É—insa wanka yay tare dayin sallah sannan ya nufi kicin ya haÉ—owa kansa tea yasha ya kwanta duk da acikin satin nan ma yana da tafiya, da tunanin tafiyarma bacci ya kwashe sa.
Nafi ƙarfin minti ashirin zaune acikin tsananin sanyi A/C kuma ikon ALLAH har yanzu babu mahalukin danaga giftawarsa acikin falon gawani irin zazzaɓi dayake neman kamani wanda nasan bana komi bane ba face na tsantsar sanyin danake ji haɗi da yunwa.
Gashi ya hydar ɗinma daya sakoni gaba naimasa rashin kunya yaji haushi ƙila ya koma, tur nai da maganar dana masa ɗazu wadda nasan inda ban masa ba da tuni yanzu ya cikani da abinci naci na hantse.
Amman nan dan tsabar wulaƙanci jibi ko tsuntsuma ban ganiba bare ataimakamin da inda zan rage marata tare da cin abinci kuma.
Jan jikina nayi ina sakin wani marayan kuka mai cin rai tare da saka hannuna na rufe fuskata na cigaba da kukan danake.