← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 58

Sashe 16

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dawani irin firgici mai tsananin gaske maryam ta juya cikin ɗakin,ragwaf ta faɗa kan gado tana mai dafe saitin zuciyarta tare da sakin wani irin ɗan banzan kuka! mai taɓa zuciya sosai take kukan tana kuma sake mamakin abinda Hydar yay mata wanda ko a marfaki bata taɓa kawowa Zemata hakan ba.
Kai itafa har yanzu gani take abun kamar abun a mafarki yake yau ita maryam akaiwa kishiya duka-duka auran nasu yaushe ma aka yisa bare ace har an ɗauko mata wata da sunan abokiyar zama, wata irin tsanar mahaifin mijin nata taji atake wadda take ganin kamar dan ya ƙuntata mata ne yasaka yay hakan sosai take gursheƙen kuka a cikin dakin ahaka wayarta ta kuma yin wani ringing! ɗin a karo na barkatai da sauri ta jawo wayar cikin tashin hankali take danna wajan ɗauka tare da karawa a kunnenta.
"Hellow mamy na kimin boking jirgi wallahi gida zan taho.ina cikin tashin hankali mamy na waini yau Hydar ya gayawa magana akan wannan shegiyar yarinyar wallahi mamy bana zaman gidansa.
Seda mamy taɗan nisa daga nata bangaren sannan tace "to maye na wannan kukan! haka kefa dadina dake hauka kinsan idan kika sake kika dawomin gida a yanxu dadynki ze ɓata mana raine dagani harke, sannan kuma abinda nakeso dake shine ki kwantar min da hankalinki duk abinda yake faruwa hajiya zainab ta bugo ta gayamin wannan dalilin nema yasa naketa zabga miki waya tun ɗazu amman baki ɗaukaba.
Daman ke idan kina cikin tashin hankali sam bakya control mind ɗinki to a kull ɗinki kada ki sake kice zakizomin gidana a wannan lokacin ban lamunta ba, ke wacece da baza,ai miki kishiyaba? shin waike wace irin shu'umar yarinyace ne daman idan mijinka yana neman aure koyayi aure so ake ka ɗaga masa hankali? Wallahi wannan haukan da wasu matan suke shine yake ƙara harzuƙa wasu mazan akan ƙarin auren da sukai ko suke nema.
Ace tsakani ga ALLAH wai dan kina mace dan mijinki yana neman aure ko yay miki kishiya seki ɗagawa kanki hankali kiƙi nutsuwa bakisan a wannan lokacin shikuma mijin yake sake jin shauƙin yin auren ba.
To bara kiji ni mahaifiyarki ce iya gaskiyata zan gaya miki idan kin ɗauka kanki idan baki ɗaukaba keki ka jiyo nina san ko a ƙiyama ALLAH baze kamani ba.Idan zaki riƙe mijinki da kishiyar ki ku zauna lafiya to idan kuma baxaki riƙeshiba babu abin da ya shafi aminatu.
ALLAH yayi miki luɗufi yabaki miji ɗangaske miji nagari mai sonki ɗan mutunci wallahi kikai wasa ya kufce miki kekika jiyo babu ruwana ni anan shawara ta rage gamai shiga rijiya idan zaman gidan kikeso gaki gashi nan kina kallon mahaifinki tunda ya faɗi a zaɓen nan lafiyarsa tai ƙaranci kinfison kixo ki zauna mu haɗa kai a ɗaki kishiyoyi na mana dariya daman suna bakin cikin auran dakikai to idan haka kikeso bisimillah ALLAH ya baki sa,a bada aminatuba".
"Ai daman nina san haka zakice wallahi mamy idan kina min wasu abubuwan senaga kamar bakya ƙaunata yanzu ace aiwa yarki kishiya amman ki gaza ɗaukar wani mataki se wannan maganar to wallahi zanbi yadda kikace na zauna amman wallahi sena jagulawa wannan yarinyar rayuwarta sena hanata zaman lafiya dan tayi ƙarya in haɗa miji da ita" takai maganar tana jan numfashin ta.
Salati mamy taja cikin sauri cike da tsananin mamaki tace "amman maryam wannan ba halina kika ɗauka ba tabbas sedai daga wani wajan kika dauki wannan ɗabi,ar kina kallo acikin gidannan sedai ni su cuceni nai hakuri amman yau ke ki kecewa zaki ɗagawa ƴar mutane hankali tokiyi a hankali dan kada reshe ya juye da mujiya garin kallon ruwa gwaɗo yay maki ƙafa, sannan ki dinga tuna abu ɗaya tak!! har yanzu a matsayin MATAR HAƊI kike a wajan Aliyu ba MATAR SO ba agabanki mahaifiyarsa tazo gidanmu ta rokeni akan idan ina da ɗiya na bawa ɗanta ya aura sabida ita tun a aikin hajji data haɗu dani taji tana son haɗa zuri,a dani sabida kyawawan halina tana tunanin idan ɗanta ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴana zata samu xuri,a ta gari kuma cikin ikon ALLAH data turoshi ya ganki yaji yana sonki har ALLAH ya kaiku ga aure to ina son jan kunnenki da kada kiyi watsi da damarki a wajan ɗa mai alkunya mai tarbiya mai daraja surukansa ki taka a hankali nidai iya shawarata a gareki kenan nabarki lafiya".
Mamy tana dire wannan maganar ta katse wayarta. Barin maryam tayi da sakin baki wadda ko kaɗan kalaman mahaifiyar tata bai ratsata ba,bare taji wani ɗar aranta illa ma wani mugun nufin data ƙara ɗasawa acikin ranta. Cikin wani irin yanayi mai cike da saƙe-saƙe kala kala a ranta ta miƙe tare da nufar kofar futa cikin fushi dole ta nuna masa ita macece wallahi seta ɗauki mataki akan batula dan baxata zauna da wannan mai baƙar fuskar a matsayin matar tsadaddan mijinta ba sam hakan baxe yuwuba.
Tana futa ALLAH ya taimaketa ta samu mai napep seda tai da gaske sannan ta gane gidan aminyar momy sauka tai sannan ta dauko naira dubu ta bawa mai napep ko sauraran canjinta batai ba haka tai cikin gidan cikin sauri a falo ta tarar da hajiya turai suna lissafi itada da Æ´arta sannu kawai taiwa hajiya tare da shigewa É—akin dataga momy ta aje musu kayansu jiya.
Dagudu ta ƙarasa Cikin dakin tare da faɗawa kan momy tana kuka! cikin tashin hankali momy ta ɗagata tare da cewa "lafiyarki meke damunki?" ta jero mata tambayar a jere "wani abun wannan yaron yay miki?"
"Momy Aliyu ya cimun mutunci yau" Sosai ta zauna tana gayawa momy ƙarya da gaskiya wanda yayi tsananin tasiri acikin zuciyar momy Cikin fushi ta jawo wayarta tare da danna masa kira sanin halinsa na bakar zuciya yasa taɗan sassauta fushinta sabida idan har ta nuna masa maryam ce ta kawo ƙararsa tofa kashin maryam ɗin ya bushe shiyasa ta sassauta fushin nata.

Seda tai kusan minti biyar tana kiran sannan ya ɗaga daga jin muryarsa kasan akan titi yake "Assalamu alaiki hajiya ya akai?" "Kana ina baba?" saninsa mutum marar ƙarya ko boye boyen magana yasa yace mata "gani a gadon ƙaya lafiya?" zaro ido tayi waje tare da cewa "mekaje yi acan ɗin?" adake yace mata "naje wajan abba yana son ganina gani acikin napep"muskutawa tayi kaɗan sannan tace "to kabar zuwa can kazo nan court road gidan hajiya turai ina son ganinka".

Lumshe idanunsa yayi tare da kallon agogon axurfar dake daure a tsintsiyar hannunsa sannan yace mata "Afuwan hajiyata insha ALLAH da zarar na gama da nan É—in zan samu nashigo komin dare,Wallahi na riga nama kai kawai shiga cikin layin nashi zanyi".

Zare wayar tayi daga kunnen ta tare da kallon sunan tabbas Aliyun tane wannan ɗan nata maijin maganarta marar son ganin ɓacin ranta marar son saɓa maganarta wanda baya ƙetare dukkan wani sharaɗinta amman yau shike bata hakuri akan zeje gidan maƙiyanta.

Shikam daga nashi bangaren yanata "hellow!! hellow!!" jin shuru yasa ya katse wayar tare da mayar da ita aljihun sa.

Itama da sauri ta mayar da wayar kunnenta jin shuru yasa ta ƙara mayar da idanunta kan screen ɗin wayar sedai kash ya katse da sauri ta zabura "nashiga uku ni zainab mai yake shirin faruwa dani"........!!!

*28 - 29*
Chapter 16 · 0% Book details