← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 58

Sashe 56

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsitt yay na Æ´an sakanni sannan ya fara magana......

*99*

"Fatie"! yaja sunan cikin fitar sauti! mai É—an qarfi sannan yaja fasali kana ya cigaba da min magana cikin dakushashshiyar muryarsa mai kama data wanda ya farka daga bacci.

"Kinsan dai yadda kukan! ki yake fasamin kirjina ko? shin yaya kikeso nayi da rayuwata?.da abinda kikaimin koda bakin cikin abinda maryam tai man koda rashin É—iyata koda abinda mahaifiyata tayi? ke kaÉ—ai nake tunanin zaki tausayamin ki kuma bani nutsuwa adai dai wannan lokacin, amman keÉ—in ma kin juyan baya! tayaya zanji dadin rayuwa kinganni a gadona manne da pillow kamar maraya yau É—innan nakeson na wuce legos wajan wani aiki gwara nai nesa da kowa tunda bakwa sona" yakai maganar yana sauke numfashinsa a sama.

Wani kukan ne mai qarfi ya zomin a wannan karon da sauri na faÉ—a bayi na rufe tare da zaman dirshan qasan bayin ina dafe bakina "yaya yanzu tafiya zakai kabarni kaima kaji haushina kenan kamar yadda umma taqi min magana tun jiya sabida ina kukan rashinka kusa dani, yaya dan ALLAH kayi haquri a wannan karon bazan iya ganinka a damuwa ba wallahi ko wancan karonma yaya ina sonka kawai bakin cikin abinda momy takemin ne yasa aurenka ya ficen araina" nakai maganar ina ya tsina fuskata jin yadda amai yake kokarin tahomin sakamakon warin omon da amira ta wanke pant É—inta dashi ya bugi hancina.

Toshe bakina nai tare da saurin danne mugun yawun daya tahomin sannan na cigaba da magana "Dan Allah yaya kai wani abu akan auranmu na komo É—akina nidai ina sonka umma ma kasan bacin rai ya saka ta É—auki wannan mataki amman bada ban haka ba umma bata da matsala, sannan kuma kasan abba bai saka baki ba yace shikam babu ruwansa.

Lumshe idanunsa yay tare da qara matse pillow É—in a kirjinsa yana lalubar lips É—insa yana tsotsa cike da jaraba nan take idanunsa ya kaÉ—a jawur sakamakon kukan datake masa wanda yake kokarin tayar masa da tsuminsa.

"Shi!! kimin shuru malama! yay maganar a dake kamar bashi ke cikin shaukin sontaba, "mike damunki kunje asibiti?" yay maganar a jere idanunsa a lumshe.

Jan numfashi nai tare da cewa.
"Nima ban saniba daga jiya dai zuwa yau zazzaɓi ke damuna kullum dashi nake kwana se yawan jin miyau abakina sannan kuma ina jin amai yana tasomin" nakai maganar cike da kuruciya.

Ture blanket É—in daya rufa dashi yay tare da cilla pillown gabansa can nesa sannan ya miqe cikin matsanancin farin ciki sunanta ya kira a comlpt a wannan karon.

"FaÉ—ima! bai jira mi zatace ba "ALLAH nagode maka ALLAH kasa hasashena ya zama gaskiya dole yau zan aje komai nazo kano komin dare ki ajan kanki ni zan kula dake kuma zan koma dake É—akina"

"Fatina mugodewa ALLAH ina tunanin ubangiji ya mayar mana da alkairinsa ya azurtani da samun É—a ko Æ´a ajikinki fatina ciki gareki dan ALLAH kimin tattalin kanki ki kulamin da kanki nikuma ina nan zuwa kano senaga abunda ya turewa buzu naÉ—i" yana kaiwa nan ya katse wayar tare da dira daga kan gadon ya nufi bathroom ya dauro alwala dan yay nafilar nuna farin cikinsa ga ALLAH.

Cike da rashin É—aukar maganar sa da muhimmanci na aje wayar tare da sakin dariya hmm wai ciki sekace wasa daga yin abu sau uku shine ze wani ce ciki.

NafaÉ—a ina dariyar maganar tasa.

Can kuma sena kai kaina gaban rariya wasa wasa senaji amai yatahomin mai yawa aikuwa haka na soma aman wanda zuwa wani lokaci na wahala.

ÆŠago kaina nai jin an bude kofar bayin na kalli wanda ya shigo a wahale Umma ce tsaye akaina ta haÉ—e ranta katamau tana zabgan harara

"Da waya kike waya?" watakan ke bakyajin magana ko baxaki tsaya a karɓar maki ƴancinki ba keme miji harda daukar wayan abbanki ki kirasa ko? waini kam yaushe ma kika fara sonshi? umma ta jeron tambayar bayan ta saka hannu ta ɗauke wayar dake Yashe a qasan tiles.

Ban iya bata amsaba sema mayar da kaina qasa danai ina cigaba da maka aman daya zomin.

Da sauri amira tayo bayin aguje ta taro ruwa ta kora aman sannan ta wanken bakina ta É—agani mukai ciki mukabar umma tsaye cikin mamaki.

Kwanciya nai akan gadon ummi sannan na rufu da bargo wanda kafin wani lokaci zazzabin ya kuma kamani.

Abba ne daxe fita aiki ya shigo danya ga jikin nawa ganin ina rawar É—ari yasa ummi ta É—agani na saka hijab sannan muka fita waje.

Umma ya kwaÉ—awa kira sannan yace ta É—auko mayafinta haka tafito yace muwuce asibiti, wani asibitin dake kusa da gidanmu É—an karami na kuÉ—i aka kaini seda mukai É—an zaman jiran likita bayan yaxo muka yanki kati sannan yace wa umma ta shigo dani.

Zama nai a kujerar dake fuskantar likitan sannan ya soma min tambayoyi bayan ya gama yacewa umma naje nai fitsari a wata ƴar kwalba, bayin dake kusa da ɗakin muka shiga seda umma tai min tsawa sannan na tsugunna nai fitsarin ta karɓa ta kai masa sannan muka koma inda abba ke zaman jira muma muka bi layin zaman.

Mintuna kusan 30 sega nurse ta fito tace muje likita nason ganin mu haka muka koma office É—in zama mukai sannan likitan ya farawa umma bayani tare da bata shawarwari kana ua miko mata wata farar takarda.

"Masha ALLAH hajiya Æ´arku tana É—auke da juna biyu na wata É—aya ciff fatan alkairi ALLAH ya inganta" likitan ya gayawa umma haka.

Ga mamakina senaga umma ta sunkuyar da kanta a qasa tana murmushi amman bata amsawa likitan komai ba da alama kunya taji.

Nikam wata irin kunyace ta rufeni waini keda ciki watakan ranar daya fara kusantata tun alokacin na samu cikin kawai wannan masifar ita ta hana mu fusancin hakan.

A Sunkuye nabar office É—in ko amota saka kaina nai a cinyata fafur naki kallon su abba, itama umma bata iya masa bayani ba illa takardar data basa, sukam maxa basuji irin kunya kamar ta mata haka abba ya saka umma agaba yana tsokanarta "a,a lallai su indo angirma a,a za,a É—auki jika haka abba yayta wa umma tsiya wadda tai kamar zata balle murfin motar ta gudu!

Waya ya dauka ya kira baban abuja ya shaida masa sannan ya katse yana faman zabga murna "a,a yauni zanga É—an fatina lallai yawan rai yawan gani" haka abba yayta murna kamar me.

Muna shiga gida na balle motar na gudu ɗaki ina jiyo sautin muryar abbanmu cikin zolaya "kenifa karki jamin bariki da kanta da bataliyar yaqi kiyi masa hankali da ciki kidaina wannan gudun kada ki ɓari kijamana tashin hankalin rikitaccen mijinki" dariya nai ban magana ba daman shi abba yanada barkwanci nasan yanxu fa na shiga uku a wajansa.

Ina shiga É—aki na mayar da numfashi na faÉ—a gado minti uku segasu ummi sun zagayeni suna tsalle kamar wasu yara wannan nacewa ita zata dinga koya É—an wannan nacewa itace nidai ban masu magana ba haka naja bargo na kwanta se bacci.

Wajan azahar naji sautin muryar umma tana min magana sama sama ina bacci "fatima tashi ga abinci kici" tashi nai ina tura bakina sekuma na saka kuka!

"Ni umma baccina nakefa mai daɗi kika tayar dani" sakin baki umma tai tana kallonta sannan ta fara magana cikin lallami "haba faɗimata tun jiya baki kai komi fa bakin kiba maza taso mutumin naki nai maki ɗan wake taso na wanke maki baki kici kinji ɗiyar abba" ture ture na soma da qafata cike da shagwaɓa "nifa umma bana sonsa nafison fate tun jiyafa naketa ce maki fatan zan sha amman bakimin ba" ina gama faɗin haka se kuka.

Cike da É—umbin mamaki umma ta fara magana "to naji tashi ki wanke bakin ki sallah kafin nan nagama seki sha da wuri" tana gama faÉ—in haka ta fita daga É—akin cikin mamakin wannan yarinya tata.

"Nikam ALLAH ya kawo mijinki ku haÉ—a kutafi badani ba wallahi baxan iya ba kije can ku qarata, nidaman can badan ki zauna na daukoki ba dan na nunawa uwarsa nima na isane yasa nai haka amman badan wai na quntatawa hydar yaron kirkiba bare kuma yanxu da zuriya zata shiga ai dole a sulhunta ashe dai wannan aure rabone" Umma takai maganar a fili sannan ta nufi kicin ta dora mata fatan.

***************

Yana idar da sallar bai tsaya shiryawa ba ya dauki keyn mota yay gidan momy akicin ya tarar da ita tana girki duk jikinta yay sanyi babu wannan faÉ—an tsugunnawa yay ya gaisar da ita sannan ya É—ago.

"Hajiya kinji fatima....sekuma yay shuru yana sunne kansa a qasa alamun jin kunya.
ÆŠagosa tai ta kara ajikinta "baba miya sami fatiman kagaYamin dan ALLAH?" ta jero masa tambayar cikin É—imuwa.
Ganin duk ta kiÉ—ima seta basa tausayi "baba kagayamin miya sameta wallahi baba yanxu a shirye nake dana riqe fatima kamar É—iyata ina sonta da zuciya É—aya zanje har kano nabawa aisha haquri na bawa fatima haquri ko hakan zesaka naji sanyi a rayuwata" takai maganar tana kukan zuci.
Rungume mahaifiyar tasa yay yana jin kaunarta mai yawa acikin ransa.
"Hajiya ALLAH ya azurtamu da samun É—a ko Æ´a acikin fatima hajiya fatima tana da ciki" yakai maganar da sauri tare da sake rungumar momy cike da kunya.
Baqaramin mamaki momy ta basa ba ganin yadda take faman murna kamar batan taɓayin jikaba.

Seda ta gama murnarta sannan ya gaya mata yau zeje kanon.

Cike da bada goyon baya momy tace itama zata bisa dan ta baiwa aisha da fatima haquri harma da abba.

Sosai yaji dadin hakan sannan ya miqe yay gida ya shirya yaje yay masu boking na jirgi sannan ya zo ya tafi da ita wadda itama ta shirya jiransa take.

Qarfe É—ayan rana suka tashi inda ya baiwa driver keyn motar da sukaje airport da ita

Jirginsu ya É—aga kano shida momy wadda ta cika da tarin nadama.......!!

*100*

Basu suka sauka a kanoba se wajan qarfe biyar na yamma cike da tarin gajiya momy da hydar suke sauka daga step É—in jirgi.

Babu wanda yasan sun taho shine dalilin dayasa ya fita ya samo masu abin hawa kai tsaye gadon qaya suka nufa gidan abban gadan qaya, baban batula.
Chapter 56 · 0% Book details