← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 58

Sashe 21

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*36 - 37*
Shasheƙar kuka nake ajikinsa ina ƙara cusa fuskata a kirjinsa ina shaƙar wani shu'umin ƙamshi daya kusan zautar dani.
Munkai kusan minti biyar a haka kafin naji saukar hannunshi akan ƙuguna.
Da sauri nai wani zullo tare da ja da baya kaÉ—an ina faman tura bakina gaba.
Batare kuma dana ce mashi komai ba,taku ɗaya biyu ya ɗan biyoni kaɗan yana ƙara kawo hannunshi jikina da sauri naja baya tare da maƙurewa ajikin bango jikina yana rawa.
Hucin numfashinsa ne yake saukar min akan fuskata sabida yadda kusancin mu ya daÉ—u dana junanmu.
Sosai nakejin yadda idanunsa ke yawo akan fuskata.
Ƙara runtse idanuna nayi ina faman sakin ajiyar zuciya cikin kirjina kuma yana bada wani irin sauti mai fitar amo!.
Ƙara matsoni yayi sosai har jikinmu na gugar na juna.
Cikin wata iriyar fisgar murya wadda seda yayi da gaske kafin ya fisgeta sannan naji yace.
"BuÉ—e idanunki ki kalleni mara kunya".
"Wallahi idan na kuma magana sena ɓallaki anan wurin".
YafaÉ—a da É—an sautin faÉ—a-faÉ—a kaÉ—an.
Da ƙyar na fara buɗe idanuna kaɗan kaɗan ina saukesu akan fuskarsa.
Wani irin kyau naga yayi min mai haɗe da mugun ƙwarjini na fitar hankali.
Da sauri na kuma mayar da idanuna na kulle gam harda saka hannuna guda biyu na rufe fuskata dasu ina sakin wani irin kuka wanda na rasa na miye ne.
Silalewa nai tare da zama a ƙasan tiles daɓas ina cigaba da kukana.
Ban tsinke da lamarinsa ba se da naga shima ya biyoni ƙasan amman shi tsugunnawa yayi irin na ƴan ƙwallon ƙafa yana ƙara bin fuskata da wani irin shu'umin kallo dana rasa na miye.
Ta cikin tafin hanuna nake kallon yadda yake watsa min wata iriyar harara tare da wani irin kallo kona miye oho?
"Fatie!".
Naji ya kirawo sunana a É—an tsawace kaÉ—an.
Baijira mi zance ba ya É—ora da.
"Ni ba sa,an wasanki bane ina jan kunnenki da kishiga hankalin ki kitattare duk wannan daƙiƙancin naki wuri ɗaya idan ba haka ba ko hmm ya ƙarasa yana ƙwafa!!.
Da mugun tsoro na ɗago kaina a karo na farko dana kalleshi tare da sabga mashi harara nima tare da mayar da kaina ƙasa ina cigaba da kukana.
"To waini yaya dole ne auren a fasa tafiyar dani mana dan ALLAH kabarni anan in shiga fce idan na gama na tafi can ɗin kafin nan na ƙara girma ma".
Da kallo naga ya bini tare da kauda kansa gefe yawani cije baki wanda naga kamar al,adarsa ce hakan tare da sakin wani shegen murmushi.
Hannunsa naga ya ɗaga da sauri naja nakuma raɓewa jikin bango duk tunanina taɓani zeyi senaga ashe akan sumar kansa ze ɗora.
ÆŠorasa yayi yana shafa sumar kansa kaÉ—an-kaÉ—an.
"Fatie!".
"Ke a tunaninki wani abun zaki ƙareni dashi har yasa na karɓi auranki?".
Wani murmushin ya kuma saki mai futar sauti tare da cewa.
"Keba tsarata bace bare na nuna miki true colour É—ina, but amman ki saka aranki bakin rijiya ba wajan wasan yara bane ba nonsense kawai!.
Yafaɗa yana miƙewa daga tsugunnon daya yayi agabana.
Ɗan ranƙwaɓowa ya kumayi gabana kaɗan har yana huromin hucin bakinsa mai ƙamshin mint.
Saka hannunsa yayi ya tallemin bakina kaÉ—an.
Wani ihu na saka na shagwaɓa tare da ƙara matsawa jikin bango ina sosa bakina da yatsun hannuna hawaye na shatata kamar famfo a idanuna.
"Banza mayyar maza".
Na tsinci muryarsa ta daki dodon kunnena.
Da sauri na É—ago ina kallonsa tare da jin wani irin takaici acikin zuciyata.
"Kima aje wannan jarabar taki niba sa,anki bane ba.kuma ki sani dik wannan kwandon balagar taki ni ALIYU bazan É—aukaba kisan yadda zaki ki aje rashin kunyarki idan ba haka ba kullum zan doke wannan banzan bakin nakine".
Yana gama faɗan haka ya fice yabarni da shu'umin ƙamshinsa manne akan hancina.
Tun kafin inga ya ɓace daga ɗakin na saka kuka mai sauti!.
"Ni wallahi bazan bi mugu ba kuma ALLAH seya saka min".
Cikin sauri nakai maganar tare da shigewa cikin Cavet É—in umma na buya ina zaro ido waje.
Murmushi ya saki akan fuskarsa tare da nufar falon umma batare daya jiyo ya kalleta ba har yanzu yasan tana da kuruciya ganinsa ya tsaya biye mata se girmansa ya zube abinda baya fatansa kenan daga gurinta har abada.
Tun kafin ma ya kai ga zama maryam take aiko masa da wani irin kallon tuhuma mai tattare da zargi kala-kala acikinsa.
Dayake shiÉ—in namijin duniyane ko takanta baibi ba haka ya zauna yana mai dafe manhood É—insa jin reaction É—insa na neman sauyawa.
Cikin haka abba ya shigo da sauri ya risina yana gaisar da abba amman itakam maryam seda ya maka mata harara sannan ta gaida abba tana mai jin wata irin tsanar kowa na gidan.
Cikin minti kaÉ—an Su ummi suka cika musu gabansu da kayan abinci kala kala wanda umma ta sarrafa musu.
Sauko da jikinsa yayi zuwa ƙasan carpet bayan abba ya basu waje su ɗan ci abinci kafin a gyara musu part ɗin nasu.
Tea ya haÉ—a batare daya saka madarar dake gabansa ba, da zafinsa yake kaiwa cikin bakinsa har wani lumshe idanu yake jin yadda jikinsa yake wani irin mutuwa. bakaramin dadin tean yajiba sabida daman idan yana cikin wannan situation É—in tea ko coffee kaÉ—ai ne ke É—an basa realief.
Yakai kusan minti biyar yana shan tea É—in sannan ya kammala ya aje cup É—in a gefensa batare daya kula tulin kayan abincin dake gabansa ba.
ÆŠora kansa yayi akan kujera yana jin sa a takure.
Ko kallon maryam baiyi ba bare yace mata ta sakko ta karya ai cikinta ne idan taga dama taci baze mata dole ba.
Ganin babu sarki se ALLAH yasa maryam saukowa babu kunya ta fara zuba abincin har tana haÉ—iyar miyau babu ji babu gani take kai loma ko spoon bata saka ba abinka gamai juna biyu.
Seda ta gama tsaff sannan ta hau kokarin hawa kujera ta zauna.
"Malama ki tattare masu kayansu ki fitar mana".
Taji muryarsa ta daki kunnenta ganin babu alamun wasa atare dashine yasa ta haÉ—e kayan tafitar zuwa kicin tana tafe tana gunguni.
Ko kallon umma wadda take mata sannu bataiba haka ta dire kayan har tana fasa musu filet.
Tsaki ummi taja tare da bar mata kicin É—in tana maijin tsananin haushinta.
Daman can ita ummi bata son matar nan bare kuma yanzu datake jin kishin yayarta a wajanta.
Da mamaki maryam tabar kicin É—in har ta koma wurin Hydar dik jikinta babu daÉ—i.
Zama tayi tare da kallonsa.
"Beby ya kamata fa muÉ—an shiga can É—in wallahi am not comfortable anan wajan".
TafaÉ—a tana kallonsa taji mi zece mata.
"Ai nan ma wajene ba daji ba".
Taji muryarsa ya bata amsa idanunsa a lumshe kamar mai bacci.
Duk da shima ɗin baijin gamsuwar zaman falon umma yafison ya ga ya keɓe da ita, amman danya nuna mata mahimmancin gidan kawun nasa yasa yabata amsar haka.
"ALLAH ya baka haƙuri".
TafaÉ—a tana mayar da fushinta cikin ranta babu yadda ta iya haka ta mayarda hankalinta ga kallon t.v'n dole dik tana jin babu daÉ—i.
Falon tsitt ya ɗauka kowa yana saƙa abu acikin ransa.
Shi anasa ɓangaren yana jin yadda abarsa take harbawa babu abinda yake buƙata kamar yaji ɗumin mace ajikinsa wannan dalili yasa ko idanunsa ya gaza buɗewa.
Itakam maryam ta cika tam kamar zata fashe dan tsananin haushin yadda ya watsar da ita amman tana tsoron masa magana yanzu ya yarfata.
Sallamar umma ce ta katsewa ko wannensu tunanin shi.
Amsa mata maryam tayi ganin yadda ya ɗago ya maka mata harara da jan idanunsa waɗanda tsananin buƙata ya mayar dasu hakan.
ÆŠaki umma ta nufa tare da tsayawa a gaban batula.
Cikin sauri na miƙe ina kallon ta tare da saka hannu na toshe bakina sabida daman kuka nakeyi.
"Mina ce makine batula?".
Cewar umma tana zafgan harara.
"Umma yanzu daman zanje na gyarafa idona kemin zafi".
Nafaɗa tare da saurin miƙewa nabar ɗakin gudun kada ta kawon maka.
Dashi na fara cin karo zaune akan carpet yawani miƙe mana ƙafa kamar falonsa kansa jingine ajikin kujera komai yake ahakan oho?
Kafin kuma naga anty maryam ta juyo tana haÉ—a ido dani ta kauda kanta tana jan tsaki.
Nima tsakin naja tare da maka mata harara da jan idona wanda ya kumbura sosai sabida dukan da umma taimin É—azu.
Na wuce cikin fushi nabar falon ko takan matsiyaciya banbi ba.
Duk abinda sukai yana kallon ko wacce ta wutsiyar idanunsa tare da mamakin tsaurin idon batula kuma seya taka mata burki dan matarsa ba sa,arta bace ba ƙwafa yayi wadda ko maryam ɗin bata jita ba tare da mayar da idanunsa ya lumshe.....!

*38 - 39*
Chapter 21 · 0% Book details