← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 58

Sashe 38

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari bayan nai sallar asubahi ina lazimi sega sakon momy haka na mike naje kodanaje cin zarafi kala kala tai min sannan ta hadani da gyara cavet dinta.
Wunin ranar ban sakasa a idanuna ba nima ban saka akaina ba sabida wahalar danasha ranar tafi ta koyaushe ban sami kaina ba sedare kum ikon ALLAH yau tabani abinci naci amman dai bautar aikice dai nashata danma dai su rauda sun faki idanunta sun tayani wani aikin.

Har dare ban gansaba haka nai sallah na kwanta abina washegari da sassafe baccine ma akaina naji alamun shigowarsa ya tsaya akaina jikinsa sanye da kayan sojoji magana can kasa yakemin bayani zetafi lokoja shida anty maryam zasuyi sati uku ko wata sabida haka na kula da kaina duk abinda nake bukata naiwa momy magana bai kuma yarda na fita ko wajeba idan na fita kuma bai yafe ba yana gama fadin haka yasaka kai ya fita.
Kuka nasaka qasa qasa tare da komawa baccin bakin ciki sabida ai koba komai yana tausayamin dan wallahi adan zamana dashi na fuskanci mutum neshi mai tsananin tausayi.
Baifi minti goma da barin gidan ba sakon momy ya zogareni haka na fita wajan bauta.
Yauma wuni nai abu guda ban samu kainab se dare dakinsu rauda naje na'eem ta hadamin ruwa nai wanka sannan nai sallah na kwanta agadonsu banyi aune ba se baccin wahala.
Kwanci tashi babu wuya wajan ALLAH yau kimanin satina uku kenan agidan momy kuma haryau su yaya basu dawoba bani da labarin gida sabida babu waya a hannuna daga azabar momy kuwa yanxu tafi tada idan k ganni baxaka taba cewa batulan umma bace sabida makarantar momy ta mayar dani silent girl marar son hayaniya ko tsiya sam yanzu babu wannan atare dani yanxu babu abinda na tara se É—an banxan tsoron momy wanda ko tari tai jinsa nike har raina..
Zamana dasu rauda kam ya koyamin gayu fiye dana da ya koyamin tsafta wadda ta ninka tawa danni yanxu duk wannan son jikin babu atare dani.
Shikam yaya hydar baki ɗaya ma na manta dashi dan wata katuwar ƙiyayyarsace take yawo araina gani nake duk wannan bala,in danake ciki shiya sakani tunda inda bai amimce da aurena ba ai da tuni ina gaban iyayena amman yanxu idan ban da bauta mai nake haka wataran idan na tuno gida nai dariya wataran kuma nai kuka!

Yau watana guda agidan momy kuma babu alamun dawowar yaya ayadda najima ance wai yanxuma baya can garin an ƙara turasu wani garinne domin kwantar da tarzomar datake faruwa ga wasu yankuna na kauyukan garin da aka turasun kuma duk wannan labarin daga wajan kannensa nakeji domin ni momy bata bani wayama mugaisa bare naji labarinsa hmm base naga fuskar hakan maba.
Idan ka ganni yanxu naÉ—an fada kaÉ—an amman kuma fatata taÉ—an kara murjewa na sauya sosai tundaga kan halina har zuwa jikina.
Yau tunda muka tashi muke girke girke baban abuja ze dawo daga tafiyar dayayi wanda tunda akai aurenmu baya garin seyau ze dawo.....

*************************
Abdul kam sedai muce sam barka domin yanxu kimanin sati biyu kenan da fitowarsa daga asibitin kuma babu laifi ya dangana da ALLAH ya fitar da tunanin fati aransa sabida jin labarin aurenta dayayi yasan tai mashi nisa daman haka akeson bawa mai yarda da qaddararsa sedai kuma zaman kanone yaji yayi masa kunci saboda missing sahibarsa dayayi babu shiri yasa dady ya nema masa transper zuwa babban asibitin abuja tunda daman likita ne.
Cikin sati É—aya abdul ya haÉ—a tarkacensa ya nufi birnin tarayya tare da fawwalawa ubangiji lamarinsa dakuma mayar da hankali akan aikin dake gabansa bawa alumma taimako da iya karfin da ALLAH yabasa.....!!
Wannan kenan.

62 - 63

Yau gidan na hajiya momy da hidima muka tashi na dawowar baban abuja daga qasar waje wanda tun bayan bikinmu dayabar kasarnan bai kuma waiwayarta ba se yau dayake shirin dirowa sosai momy take faman zirga zirga tashiga nan tafita can babu abinda takeyi sefaman haÉ—a masa kayan abinci masu daÉ—in gaske wanda bata yarda dako masu aiki sun shigar mata kicinba a wannan ranar.nikam daman part É—inshi ta turani wai naje na gyara masa tare da fitar da duk dattin da part É—in yayi cikin mamaki naja qafafuna na nufi part É—in ina mamakin halin momy na sonkai duk Æ´aÆ´anta me suke dabazata turasu ba seni haka dai na karasa har cikin babban falon nasa ina mamakin wannan lamari.
Ƙarasawa cikin bedroom ɗinshi nayi na sharosa gami da sauya zanin gado sannan na karkade kurar dayayi kana na nufi bayi nanma wankesa nai tas sannan na haɗa ruwan goge tiles ɗin nan na hau faman mopping wanda shiya batamin lokaci ba kadanba ina gamawa na kunna turaren wuta wanda ta bani nakoma falon nan ma nahau gyarasa cikin mintunan da basu wuce gomaba nagama da falon tunda baya da datti shi sosai.
Ina kammalawa na haÉ—a tarkacena na nufi part É—in momy ahanya naci karo da mama abokiyar zaman momyn wadda tunda nazo gidan banga Æ´aÆ´ansu ba kuma suma ban gansuba sabida banga fuskar dazan tambayi zuwa gaidasu É—inba.
Da sauri na tsugunna nagaida ita cikin ladabi ina sunkuyar da kaina qasa.
Itama cikin kulawa take amsamin gaisuwar tawa sannan da ɗora da cewa."Oh nikam fatimah kinyi ɓatan dabo ace tunda kikazo gidannan baki leqo garemu mun ganki ba, koda yake jeki ba laifinki bane ALLAH yi maki albarka" ƙwallace taɗan tahomin ta ɓacin rai batare dana ce mata komai ba naja jikina na nufi part ɗin momy ina lissafin maganganun mama,wato dai duk ƴan gidan sun san halin momy kuma babu babbar matsalar cikin gidan kamarta.
Tun daga bakin parloun momy na tsinkayo muryarta cikin ɗan sauti kaɗan tana tsaye daga ɓangaren karamin kicin ɗinta na cikin falon ludayine a hannunta wanda da alama ina tunanin juya wani abun ma take.
"Zonan ke! abinda ta gayamin kenan tana nunoni da ludayin hannunta da sarsarfa na qarasa gabanta tare da tsugunnawa a qasa ina sunkuyar da kaina"momy gani" nafada muryata tana rawa sabida azabar tsoronta daya kamani danni yanzu mugun tsoro momy take bani.
"Dan qaniyarki kedawa naganku a tsaye a waje kardai da munafukan gidannan kika soma hada kai to wallhi bazan dauka ba tun wuri ma ki sake"! takai maganar cikin hargagi! "momy wallahi ALLAH ban tsaya da kowa ba mama..."! bankai ba ta kwadomin ludayin hannun nata a fuskata wanda ya dauki zafi zau kamar wuta! da wani irin ihu naja jikina na hantsila nai baya ina kuka! "wallahi momy ni ban mata magana ba" "rufemin wannan banxan bakin naki munafuka mai bakar fuska wallahi baxaki zamemin alaqaqaiba dan haka na kuma ganin koda haqorinki ne gawani É—an can gidan wallahi sena illataki" takai maganar tana shureni da qafarta.
Sekuma naga fuw tai cikin kicin É—in tana mita kukana na cigaba dashi tare da mamakin halin momy yanxu Æ´an part É—in su mama sune Æ´an can gidan.
Da azama na mike tare da nufar bedroom ɗina na faɗa katifa seda naci kukana na more sannan na kwanta duk da azaharce amman aina huta tunda rabona da barci tun asubahi ina wajan kwakwa😭
Tunani kala kala sune suka É—arsu acikin zuciyata gefe guda ga kewar gida ta addabeni wallahi ayanxu hanya kawai nake nema zakara yabani sa,a matuqar nasamu hanya sena gudu gida sedai ko yankani umma zatai tayi dana zauna anan amayar dani kamar baiwa.
Chapter 38 · 0% Book details