← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 58

Sashe 52

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juya akalar komawar tasa yay tare da nufar part É—in momy, zaune ya tarar da ita gefenta su hafsat ne se maryam wadda take sanye da hijab kana kallonta kasan tana cikin tashin hankali kallo guda yayma side É—in datake ya kauda kansa batare daya tankataba.

Zama yay akan qafafunshi yana mai dafe kansa da hannayenshi wanda yake barazanar rabewa biyu sabida tsabar tension É—in daya masa ca! É—ago rinannun idanunsa yay waÉ—anda suka kaÉ—a sukai jawur! ya É—ora akan momy batare daya tankataba.

"Baba nasan kaji duk abinda yake faruwa, a gidannan amman ni abinda nai shine dai dai dan wallahi sena bi duk yadda zanyi abimana hakkin jininmu, se abu nagaba mahaifinka yace nabar masa gidannan to babu komai zan tafi amman nasan da xarar gaskiya tai halinta ze neman ne da kansa dan haka seka san inda zaka kaini dan goÉ—ai goÉ—ai dani baxan nufi maiduguri da sunan sakiba" takai maganar tana kallonsa.

Adaqile ya furta "Allah ya kyauta" batare daya tanka maganarta ba, sannan ya kuma cewa"ki koma gidan dake gwarumfa tunda clean yake" daman yana da wani gida acan É—in shiyasa yace ta koma can...

Yana gama gaya mata haka ya miqe yana rintse idanunsa duk duniya babu wanda ya isa yay masa wannan cin mutuncin sannan ya zauna inuwa guda dashi idan ba itaba domin mahaifi yafi qarfin wasa yaya ze da ita duk tsiya mahaifiyarsa ce.

"Baba! takira sunansa ganin zebar wajan "maryam baxata koma gidansuba abisa umarnina ban amince taje ko ina ba yau zata koma part É—inkama kuma ko kallon banxa ban amince kai mataba dan dame zataji idan banda rashin imani a kashe mata Æ´a sannan ace ta tafi gida ubanka zatai maka agidan nasu!! takai maganar cikin masifa.

Ko qala bai ce mata ba haka yaja qafarsa yabar falon, bai koma part É—in nasaba kawai seya dauki mota yabar gidan wajan wani abokinsa yaje wanda yay masa jagora wajan wani lauya wanda ze tsaya amatsayin lauyan batula duk wani abu seda hydar ya sanarwa da lauyan mai suna br.saddiq sannan sukai sallama akan gobe zezo ya É—auki, hydar É—in suje can wajan batulan danya mata wasu tambayoyi.

Itama momy sun É—auki nasu lauyan batare kuma datai shawara da kowaba haka xalika aranar ta É—aga tabar gidan baba inda baba yace kada ta tafar masa da É—a ko É—aya. haka ta wuce gidan hydar na gwarumfa batare da ko kare yay mata rakiyaba.

Maryam kam ta koma part É—in hydar amman har yanzuma bata saka sa a idanuntaba, sannan ga mamy mahaifiyarta taqi zuwa kuma ta hana kowa yazo tace babu ruwanta tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan duka.

Haka ta zauna a part É—in sukuku duk jikinta babu daÉ—i ga bakin cikin rashin É—iyarta.

Bai shigo gidanba se bayan sallar isha sannan yay wanka ya kuma fita, wani wajan siyan abinci yaje yasai abinci da lemo da ruwa ya nufi sitation É—in officern yay ma waya ya basa kayan abincin sannan yabar sitation É—in ya kuma komawa gida, kai tsaye É—akinsa ya wuce ya kullo kansa ya zauna ya saka kuka! kamar wani yaron goye, babu mai rarrashinsa shikaÉ—ai yasan yadda yakeji acikin ransa.

Babu yadda ummi batai da umma akan su wuce gidan, baban abuja ba amman umma taqi tace wallahi ita yanzu bata kaunar kowa na gidan sabida haka zata sauka agidan wata qawarta anan É—in har zuwa sanda zataga abinda ya turewa buxu naÉ—i sannan hydar ya sakarmata Æ´a tai gida da ita, dan ita a ganinta kowa na gidan yana da laifi tunda suka bari aka tafi da batula batare dasun tsayar ba.

Agidan qawartan kuwa suka sauka kuma matar mai kirki da Æ´aÆ´anta sa,annin ummi nan aka bawa umma da ummi É—aki aka basu abinci da komai matar qawar umma mai suna anty habiba mace mai kirki ita taita baiwa umma haquri akan tabari se gobe saji yadda abin yake, abincin dai se ummice taci amman ita umma ko ruwa bata iya shaba haka tai alwala ta kalli gabas tana miqawa ubangiji lamarinta.

Suma su abba baxu zoba se wajan goman dare cikin mamaki baban abuja ya taresu anan suke shaida masa cewar mama ce ta kira take gaya masu cikin faÉ—a ya dinga magana yace mai yasa aka shaida musu mezasuyi subarsa mana ai ze dauki dukkan matakin daya kamata seda abba ya shaida masa ai magana ta cika gari harma umma taji sun taho sannan kuma aka shiga tambayar ina umman take.

A,a koda baba ya tura cikin gidan mama ta shaida masa umma bata zoba tuni hankalin abba ya tashi ganin ai sun rigasu zuwa, seda ya kira anty zee sannan ta shaida masa ummi takirasu tagaya masu sun sauka agidan qawar umma, karɓar number yay awajan anty zee sannan ya adanata yana ayyana akwai dramar kenan gaba!

Cikin dubara ya nuna wa Æ´an uwan nasa cewar umma ta sauka agidan qawarta ne sabida yafi kusa kuma sungaji amman bai nuna cewar wata matsalace ta tsaida ita acan É—inba.

Cike da bakin cikin lamarin suka kwana wanda umma hydar batula yadda sukaga dare haka sukaga rana, inda ita batula tsoro bargaba ga ciwon da hannunta yake mata sune suka hanata bacci ga tashin hankalin datace ciki.

Shikam hydar tunanin sahibarsa da halin datake ciki sune suka hanasa rintsawa.

Da asuba suka haÉ—u dasu abba amasallaci, cike da É—umbin mamaki hydar ya qarasa gabansu suka gaisa cikin kunyar abinda mahaifiyarsa tai yake bawa abba haquri tare da É—aukar alwashin komai zezo cikin sauki da yardar ALLAH.

Sannan ya shaida masu da safan nan za,a fara zaman kotu sabida yafison ai shari,ar da wuri shine dalilin dayasa ya É—auki lauya sabida bayansa ta daÉ—e a cell.

Murmushi abba yay sannan yace masa ai su basuga laifinshiba dan kuwa baima ƴar uwarsa komaiba illa mahaifiyarsa wadda suke fatan ALLAH ya gaggauta bayyana gaskiya sannan kuma wannan abun baxe taɓa saka zumuncinsu ya lalaceba.

Haka suka qarasa gida shikam qarfe bakwai yabar gidan dagashi se jallabiya fara, ya nufi wajan lauyan da aka haÉ—asu jiya br.saddiq, seda suka gama sannan shi yay gida br shikuma yay kotu dan kai report.

*92 - 93*

Bai break fast ba haka ya watsa ruwa a gurguje! sannan ya fito kaya masu sauqin nauyi ya saka ajikinsa tare da É—aukar makullin motarsa ya nufi cikin gidan.

Abakin falon baba ya tsaya ya amsa wayan br.saddiq sannan ya katse ya nufi cikin falon kiciɓus sukai dasu abba waɗanda suke shirin fitowa suma, haka suka ɗungumo zuwa haraban gidan, amotarsa ya ɗauki baban abuja, inda sauran ƴan gidan suka hau babbar motar siyana sabida yau ɗin za,a fara zaman kotu yana da kyau kowa ya halacci wajan.

Maryam da sassarfa tazo zata buÉ—e motar dayake ciki, bayan baban abuja yana gidan baya dama gidan gaba kuma emty ne, hararar daya maka mata ita ta saka taja jikinta tabar wajan kafin shima yaja motarsa ya baÉ—eta da qura.

Tafiyar mintina kaÉ—an takaisu babbar kotun daxa,a gudanar da shari,ar bakuma su daÉ—e da shiga cikiba sega motansu abba nan itama kotun tafara cika babu laifi dan seda aka gudanar da wata shari,ar kafin afara shirye shiryen tasun.

Cikin mintuna kaÉ—an itama momy ta shigo bata zauna wajan ko da Æ´aÆ´anta ba seta nemi gu can ta zauna ita É—aya kafin lauyan nata yazo su miqe su fita wadda nan da nan maryam tabi bayansu itama.

Cikin bakin ciki hydar ya sada kansa a qasa yana jin takaicin abinda momy take wanda ko wajan su abba batazo ta gaidasu ba, wannan abun ya daurewa kowa na wajan kai hatta ga Æ´aÆ´anta.

Bayan wani lokaci mai shari,a ya nemi Æ´ansan dan kotu dasu je station É—in da aka rufe batula wanda yake kusa da kotun domin su kawota sannan br saddiq ya miqe ya kaiwa mai shari,a record É—insu da komai sannan ya dawo ya zauna.

Zamansa da kaÉ—an suma su momy suka kuma dawowa cikin kotun sannan suka zauna.

Shigowar umma ita ta É—aurewa hydar kai daman taxo bayanta ummice wadda sukai waya da abba É—azu a wayan anty habiba yay masu direction É—in kotun, bayan ummi anty habiba ce da mijinta.

Da qyar umma ta gaisa da baban abuja da sauran mutanan wajan sannan tanemi gu nesa dasu ta zauna tabar ummi tana gaisawa da sauran mutan gidan.

Kallo guda zakaiwa umma kasan akwai amtsala ganin kamar bata gansaba yasa ya tashi yaje gareta ya durqusa ya gaishe da qyar umma ta amsa masa tare da kauda kanta gefe.
Cike da É—umbin mamaki hydar ya koma domin bai saba ganin hakan garetaba.

Tsakaninta da momy kam se kallo da watsa harara daman ance mai haquri bai iya fushiba sosai yadda umma ta share kowa yabasu mamaki shikam abba dayake yasan halin matar tasa idan Æ´an abunta suka motsa yaja bakinsa yay gum!

Shigowar Æ´an sanda mata biyu riqe da hannun batula wadda ta sada kanta a qasa bata kallon kowa shiya É—ago da umma cikin furgici ta nufi Æ´ar tata wanda kafin taje ummi da rauda sun miqe da zafin nama sun riqeta suna bata haquri tana kuka tana kiran sunan batula haka aka wuce da ita can kan abinda ake tsayar da masu laifi a kotu.

Shikam hydar harta wuce bai iya É—ago idanunshiba sema share wata qwallar takaici yake damma ya dakatar da duk wani É—an jarida akan halartar shari,ar tasu

Sosai umma take kuka! inda batula ta É—ago idanunta ta zuba akan mahaifanta baki É—ayama hawayen nata ya qafe haka aka fara gabatar da shari,ar.

Lauyan su ya hydar shiya soma tashi sabida sune suka shigar da qarar tun wuri kafin su momy.
Chapter 52 · 0% Book details