← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 58

Sashe 43

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rau rau yay da fuska kamar ze saka kuka tare da kaiwa kujerar naushi "haba hajiya haba hajiya akan me baxaki gayamin ba akan me baxakice tanemi izinina ba saraifa kinsa yadda garin nan yake babu lafiya" sakin baki da hanci momy da maryam sukai suna binsa da idanu cike da É—umbin mamaki.
"To ubana dakeni sabida nabar matarka ta fita ko oho ashe kai sontane maqure acikin ranka kai ko kunyar faÉ—an hakan bakai ba to idan ma dawani guntun munafurcin sonta aranka gwara tun wuri ka cire dan wallahi baxan yarda ba ni nai gaba qaryar aisha tai nasara akaina" takai maganar tana zuba uban huci.
Lumshe idanunsa yayi tare da warasu akanta "hajiya ta yaya wai zanqi fatimah alhalin itan ahalina ce jinina ce matata ce ta sunna wadda ALLAH ya haɗa aurena da ita batare dani na shirya hakan ba hajiya bafa musan mai ALLAH ya boye mana da hakan.....tas! tas! ta tsinkesa da mari akaron farko acikin rayuwarta sannan ta miqe! "wallahi tallahi ba,a isa anyi min haka ba ninasan bayin kanka bane asiri akai maka agabana zaka lissafamin wannan maganganun dagaske baba son fatima kake"tafaɗa tana cakumarsa kamar wata mahaukaciya "na shiga uku ni zainab walllahi baka isaba baxanga wannan baqar ranar ba" takai maganar tana saka wani mahaukacin kuka! cikin sauri naga maryam ta miqe tai ɗakin momyn itama tana wani irin kuka mai taɓa zuciya.
Saka hannunsa yayi akan kafaÉ—un momy murya cike da tarin damuwa "hajiya kidaina kuka akaina ALLAH ze fushi dani amman ina son ki nutsu momy mu É—auki qaddarar mu haqiqa aurena da fatimah darasine akanki dan ALLAH momy kibarni naji da abinda yake damuna Æ´ar da bakya so bakya son mahaifanta ita ALLAH ya jarabci É—anki wanda kika fiso fiye da komai a rayuwarki yake bala'in so wallahi momy akan fatima zaki iya rasani wallahi momy zan bar maki garin nan akan fatima momy zan dauketa mu gudu" yakai maganar kamar É—an maye.
Jada baya momy tai tana kara mutstsike idanunta can kuma ta kamo hannunsa ta É—ora akan kirjinta sekuma ta rungumesa tana sakin kuka "baba kada kaimin haka tabbas senaje an karya maka wannan sihiri wallahi baba asiri sukai maka bakai bane ba wallahi baxanga wannan baqar rana ba" daÉ—a rungumeta yayi yana jin wata iriyar masifffiyar soyayyar batula acikin ransa jiyake kamar ya zauce akanta.
Zame momy yayi daga jikinsa tare da zaunar da ita.
Ya tsugunna gabanta yana gaya mata kalamai masu sanyi cike da siyasa ya kwantar mata da hankalinta amman ransa yana ga fatimansa.
Miqewa yay momy tajawosa kaiwa ALLAH baba kada ka sake nakuma jin ka furta soyayyar wannan Æ´ar agabana sannan kada ka sake ko hannunta ka kama bare akai ga zance kwanciya.
HaÉ—iye miyau yayi sannan ya qaqaro murmushin dole ya maka mata hajiya karki damu indai dan wannan ne.
Yakai maganar yana ficewa a falon yabarta da zancen zuci.
Number raudah ya fara nema danya kira yaci uban fati yaji kuma wata tambaya ta fita batare daya bata damar hakan ba sama da awa uku suna titi......!
Ringing! wayar tasa ta shigayi amman shuru ba,a É—auka ba qwafa yayi tare da sake kira a wannan karon aka É—aga wayar.
Cikin rawar jiki raudah ta É—auki wayar tare da rissinar da kanta a qasa kamar yana gabanta.
"Assalamu Alaikum, yaya barka da rana?" lumshe idanunsa yay waɗanda suka cika da zallar ɓacin rai tare da furta "gidan uban wa kuka je"! yafaɗa cikin wata iriyar tsawa mai shiga jikin mutum! da sauri rauda ta haɗiye miyau sannan tace "yaya ai mungayawa momy wallahi gyaran gashi mukaje" takai maganar tana kallon su batula waɗanda duk sukai tsaye suna jin yadda sautin qarajinsa ya cika wayar.
"Nabaku minti goma ku dawo gida idan kuka ɗara wallahi se ranku yayi mugun ɓaci"! yakai maganar tare da qatse wayar tasa qitt!
Wata zubace takaryo ma rauda sannan ta sharce ta juya ta kalli su batula"todai kunji abinda yaya yace saboda haka kawai muwuce gida kada mu tsaya shiririta ya jibgemu" takai maganar tana kallonsu.
Nikam lumshe ido nai tare da ce mata "dan ALLAH barsa wallahi muyi zamanmu har mugama abinda zamuyi daga zuwansa zewani ɗagawa mutane hankali"  naqarasa maganar ina jan tsaki! zaro idanu na'em tai sannan ta kalli raudah "nikam kunga tafiyata wallahi bazan tsaya ya lafceni a iskaba itama rauda bin bayanta tayi tare da kamo hannuna "sis zomu wuce mana kin tsaya kingafa keyn yana hannunta kada ta wuce tabarmu  wallahi na'eem ba hankali gareta ba" takai maganar tana jan hannuna turjewa nai na tsaya "kinga dan ALLAH kuje kawai nifa sena koma wajan nan anyi mani kitso dan wallahi bazan tafi da kaina babu kitsoba dan gidanku babu wanda ya iya bare aimin" ɗan jimm tai sannan tace "to mu yanzu kenan mu wuce ko yaya?"  taqarasa tana kallona dan taji mezance mata ,kaɗa kafaɗata nai alamun ko ajikina sannan nace "kawai kutafi ai da ragowar kuɗi a hannuna zan gane gida na taho"  kamar zatai kuka haka taja jikinta ta faɗa mota na'eem ce ta dubeta "a,a yanaga sis ta tsaya lafiya dai?" gaya mata yadda sukai da batula tai jimm na'eem tayi sannan ta tayar da motar suka bar wajan.

Juyawa nai na nufi wajan da akai mana saloon É—in bayan na shiga muka kuma gaisawa da matar sannan na gaya mata abinda nake buqata, cemin tai na zauna naÉ—an jira agamawa wata mata sannan mufara.
Jarida ta miqomin wai na karanta sannan ta bani lemo da ruwa cike da farin ciki na karɓa nai mata godiya sannan na zauna ina nazarin jaridar hannun nawa kafin a soma min.
Cikin minti 30 aka kammalawa matar sannan nima na matsa aka soma yarfamin wanda na zaɓa qananu mai ɗan karan kyau.

Tafiyar mintuna goma takaisu gida abakin gate sukai horn mai gadi ya buÉ—e masu suka harba kan motarsu cikin gidan.
 
Bayan sunyi parking suka qarasa cikin gida seda suka kusan qarasawa part É—in momy sannan rauda ta dubi na'eem sis anya bamuyi mistake É—in barin sister acan ba?" alama tai da hannunta na ko'in kula sannan ta dubi rauda "nifa tsiyata dake tsoro wai ita yarinyace daba xata iya kawo kanta gida ba aidai munfuta haqqinta" takai maganar tana yin gaba abinta.
Tundaga bakin qofar falon momy suka hangosa yakai ya kawo da alamun kamar yana jiran wani abunne da sassarfa suka qarasa gabansa suka tsugunna "yaya mun dawo" yaji saukar muryarsu acikin kunnensa! juyowa yay yana bin kowannensu da kallo kafin ya dire idanunsa akan rauda! "ina fatie?" ya jefo masu tambayar batare daya amsa maganarsu ta farko ba.

Gabaki É—ayansu suka dafe kirjinsu sannan rauda tai qarfin hali "munce tazo mutafi gida tace ita setai kitso tana can HANAN SALOON mun barta acan" takai maganar tana sada kanta a qasa.
Waro idanunsa yayi yana ɗan shafa sumar kansa mai uban yawa sannan ya kuma dubarsu "dan kutumar ubanku wayace kutafi da ita uban waye yace kubarmin mata acan ehe!!! ya buga masu wata mahaukaciyar tsawa wadda ta amsa ilahirin gidan baki ɗaya, da gudu suka miqe suka fara neman hanyar ɓuya ganin yadda ya hauro kamar zedake su Cikin wani irin zafin nama wanda se sojan kaɗai yasan dashi sabida horo wajan training ya cafkosu suduka biyun ya haɗa kansu waje ɗaya yakai musu wani mahaukacin bugu! ahaɗe suka saka kuka suna basa hakuri amman ina ran ƴan mazan ya ɓaci seda ya dakesu iya duka ba maceci sannan ya gwarasu da bangon qofar ya haure ya bar wajan tare da qara gargaɗinsu akan kada koda wasa sukuma futar masa da mata waje.
Da wani irin gudu har suna gware suka bar wajan sukai ciki kai tsaye É—akin momy suka faÉ—a suna wani irin gunjin kuka kamar babu gobe....!
Da,azama momy tasaki maryam wadda take kwance bisa cinyarta tana aikin kukan abinda hydar yay É—azu, tare da qarasowa gaban Æ´aÆ´an nata har zaninta yana kwancewa.
"waya tabaku daga ina kuke?" takai maganar a hargitse!
Jikinta suka faɗa sannan suka fara labarta mata abinda ya faru cike da qufula momy ta dubesu "ina shi baban yake wata kan akan wannan baqar kadarar yakeson illata min ku to wallahi bara yaxo daga shi har itana se ransu ya ɓaci baxan yarda a illataminku ba"! cike da kuka na'eem ta ɗago "a,a momy bafa laifin anty fatima bane yaya ne kawai da zuciya amman maye abin duka anan" takai maganar tana sakin kuka!"
"Dalla can matsa waye babban munafuki idan ba itaba taje tai asiri anason haukata mun É—a shine zakice min haka bayan akanta yakeson illata mun ku" takai maganar tana daÉ—a matsesu ajikinta tare da É—aukar alwashi akan batula mai tsauri.
Tsaki maryam taja cike da ɓacin rai da kishi mai zafin gaske tabar ɗakin tana jin yadda ɗan cikinta yake juyawa sabida ɓacin rai.

Dawani irin sauri kamar banasa ba yabar gidan koda yaje parking space d  a zafin nama ya shige wata baqar mota yana dannan horn kamar ze kunna gidan da gudu aka bude masa motar yabar gidan yana wani irin mahaukacin gudu na fitar hankali.
Allah ne yakaisa lafiya danma titin abuja bakamar na nan ba da É—an qarancin motoci.
Abakin wajan yayi parking batare daya kashe motarba ya futa daga ciki ya nufi cikin HANAN SALOON É—in kasancewar wajan ba boyayye bane ba agarin na abuja.
Daga wajen wajan ya tsaya sabida wajene na mata sannan ya É—auki number mai wajan yafara nemanta a waya.
Cikin kamala matar ta ɗauka sama sama suka gaisa sannan ya gaya mata cewar ta turo masa matarsa yana waje tare dayi mata kwatancan batula  ɗan murmushi tayi tare da cewa daman angama mata kitson kuwa bara na turo maka ita.

Ina tsaye bakin qaton madubinta ina kallon yadda aka tsaramin kitson yay kyau sannan kuma ga yadda gashina ya kwanta ta gefe yay kyau...!

Matar data min gyaran gashi ce naga tayo gabana tana dariya"au ashe ke amaryace ai dana sani nai maki kyaran jiki toga ango can yana jira yakafa ya tsare" takai maganar tana dariya.
Chapter 43 · 0% Book details