← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 58

Sashe 30

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Ya daɗe a tsugunne dafe da kansa yanajinsa a wani irin yanayi sannan ya miƙe yabar ɗakin yana faman rangaji gami da haɗe hanya da ƙyar yasamu ya ƙarasa part ɗinsa duk jikinsa na wani irin rawa kodama yaje cikin bedroom ɗinsa baibi takan maryam ba kai tsaye cikin toilet ya nufa tare da zare kayan jikinsa ya tsaya ajikin bangon tiles ɗin bayin ya dafe bangon da hannunsa ya sakarma jikinsa ruwa yanajin yadda reaction ɗinsa ya sauya babu abinda jikinsa yake buƙata kamar body contact cikin tsananin azaba yake jan lip's ɗinsa yana taunewa kaɗan kaɗan kamar wanda yake cikin maye, idanunsa waɗanda suka rune kamar gaushin wuta ya dada matsewa yana fitar da numfashi sama-sama yakai kusan minti 40 acikin toilet ɗin yana faman abu guda kafin yaji ya ɗan samu _satisfying_ ya ɗauro alwala gami da ɗaukar wani pink towel ya ɗaura a west ɗinshi ya fito waje yana goge tulun sumar kansa da smoll one a hannunshi.
Gaban katafaren dressing mirrown sa ya nufa tare da ɗaukar cream ya ɗan goga sama-sama sannan ya ƙarasa wajan cavet ɗin kayansa wata black jallabiya ya ɗauka ya saka tare da shinfiɗa abun sallah ya tayar da sallah ra,aka biyu.sannan yayi sallama sosai ya zauna yaja addu,oi masu tsayin gaske yana shafawa ya ɗauko alqur'ani mai girma yasoma karatun shi cikin daddaɗar muryasar sa mai kama data larabawa, yakai wajan ƙarfe ukun dare akan sallayar yana kai kukan dukkan wata buqatarsa a wajan sarki buwayi gagara misali.
Naɗe abun sallar yayi tare da cire rigar jikinsa ya rage dagashi se singlet da ɗan wando ya haye gadon ya jawo maryam kirjinshi ya matse yana sakin ajiyar zuciya baƙaramin ƙoƙarin danne buƙatarsa yayi ba sabida yana tausaya mata a wannan yanayin bai dace ya kusanceta ba koba komai daga tafiya mai tsaho suka dawo sannan kuma ga lalurar juna biyu ajikinta.
Rintse manyan idanunsa yayi yana hango yanayin daya shiga a ɗazu wanda ya rasa tartibin mai yakaisa wannan ɗanyen aikin wannan ma ai salon zubda girmane cikin ƙasan leɓensa ya furta "damma bataga girmana ba da abin yafi haka"! murmushi ya saki mai fitar sauti tare da kamo ƙasan lip's ɗinshi yana faman tsotsa a haka bacci mai daɗi ya ɗaukesa.
Seda na tabbatar danaji ƙarar buɗe ƙofarsa sannan naja jikina na fito daga bayin da gudun gaske naje ga ƙofa na datse da key sannan na dawo bakin katifa na zauna ina faman jin zuciyata tana rawa nama kasa tunanin komai sabida yadda dukkan wani tunani na ya tsaya"shi mai yake shirin yimin kenan ɗazu?" sanin babu wanda ke kusa dani bare yabani amsa yasaka naja bakina na tsuke nidai bada ban bacci ɓaro baneba da bazan rintsa ba sabida tsabar fargabar data shigeni mai tarin yawa gaba ɗayama baccin seya koma min rabi da rabi daga nayi sena farka gani nake kamar ze iya kawomin cafka cikin daren gaya kuma senaji kamar hannunshi kemin yawo ajikina ahaka na tai wannan zubar gadon har akai kiran sallar farko sannan wani bacci mai dadi ya kwasheni.
Kiran sallar farko ya tada shi daga baccin daya faɗa baki ɗaya boxern dake jikinsa yagama ɓaci da ruwan s.p cikin mamaki ya gama duba jikin nasa tabbas babu koda tantama mafarki yayi wanda har yaja masa ɓacin jiki babu yadda ya iya haka ya zare maryam daga jikinsa ya miƙe gami da nufar toilet.
Baƙarami ɗumbin mamakine ya gama kashesaba jin yaddq yanayin sa na jiya yakeson dawo masa a daddafe yayi wanka ya tsaftace jikinsa sannan ya fito doguwar riga ya saka gami da nufar masallaci, jin anfara kiran sallar assalatu, abakin gate ya haɗu da ƙannansa maza su hafiz cikin ladabi da biyayya suka mara masa baya zuwa masallaci ajere sukai sallar sannan suka nufo gida bai koma nasa part ɗinba ya leƙa wajan mahaifiyarsa ya gaisa da ita sannan ya shiga ɗakinsu rauda ganinsu zaune akan sallaya suna azkar yasa ya rufe masu ɗakin yabar wajan yana jin dadin tarbiyar da baba ya basu ta rashin wasa da ibada wadda komai ƙanƙantar ɗa agidansu dole yabi jam'i wannan ɗabi,ar itace take bin duk wani ɗan cikin gidan nasu koda wasa babu wanda yake wasa da addininshi.
Ɗakin da batula ta kwana ya nufa yaja handle ɗin jinsa garƙame yasa ya koma da baya yana aiyana ko tana bayine tana alwala.
Part ɗin mama da anty ya leƙa suma ya gaisa dasu sannan ya nufi nasa part ɗin zaune ya tarar da maryam tana addu,a bayan ta idar ta tsugunna har ƙasa ta gaisar dashi, cikin kulawa ya amsa mata yana mai zare doguwar rigar dake jikinsa ya rage dagashi se dogon farin wandon yadin daya saka ta ciki yaja blanket ya rufe rabin jikinsa dashi babu jimawa bacci ya kwashesa.
Itama maryam tana gama abinda zatai ta tube kayan jikinta tabi lafiyar gado.
Basu suka farkaba se wajan ƙarfe goman safiya shima dan saƙon kiran momy ya iskesune wanda ta addawa hydar da waya akan yazo suyi break fast.
Ɗago idanunshi yayi tare da zubawa a farin bayan maryam tare da haɗiyar miyau sannan ya miƙe duk tsigar jikinsa a miƙe ya nufi bathroom brush yayo tare da ɗan watsa ruwa sannan ya fito bai wani tsaya bata lokaci wajan shiryawaba ya ɗauki wani black jeans & white t.shirt ya saka tare da fesa mayen turarensa wanda ya cika ɗakin nan take.
Gaban gadon ya karaso ganin maryam tana ta bacci har yanzu bata farkaba duk ƙarar wayar data damesu wadda har bude idanunta tayi yasa ya ɗago tare da nufar hanyar waje dan baya tasheta tana bacciba.
Tundaga bakin kofar falon momy wani uban kamshi ketashi na kayan abinci kala-kala da momy ta shiga kicin da kanta ta sarrafawa ɗan lelen nata shida iyalinsa lumshe idanunshi yayi yana shakar kamshin abincin mai dadi daman momy badai iya girkiba kafin ya nufi cikin tsakiyar falon yana baxa uban ƙamshi mai tsayawa axuciya.
Tana daga zaune akan daya daga cikin manyan kujerun falon taci kwalliyar goal da goal daman hajiya zainab badai iya adoba farar mace kenan alkyabbar mata babu abinda ke tashi se ƙamshin turarenta na ƴanmai duguri wanda ya cika ɗaukacin falon gakuma na jikinta ita daman momy batta da wannan faɗan nata amman indai akan ado da tsafta ne angama magana indai awajan tane.
Rauda da na'eem suma suna daga zaune agefenta sunci uban ado da dogayen riguna read mate ga manyan wayoyinsu riƙe a hannunsu suna dannawa babu abinda ya damesu.
Daga É—aya gefen mus'ab da yusuf da yaseer suma zaune suke suna faman doka game É—in lido a hannunsu duk kuma ko wannan su yaci uban gayu Æ´aÆ´an momy kenan Æ´aÆ´an madara babu ruwanku da rayuwar jagwal!!
Haɗe rai yayi sosai kamar bai taɓa dariya ba sannan ya ƙarasa gaban momy ya rage tsahonsa ya gaida ita, cikin azama suma sauran ƙannan nasa suka sauko daga kan kujerun suka zube suba gaisar dashi cike da tsoronsa acikin ransu.
Adaƙile ya kalli raudah "mina ce maki next time?" ya daka mata tsawa kaɗan raba idanunta tasomayi tana kallonshi "yaya kayi hakuri insha ALLAH wannan karon zanyi koƙari"....wani matsiyacin kallo ya bita dashi kafin ya kara hade rai tare da miko mata hannunshi fari tass wanda har wani ja yayi sabida hutu, da azama ta miƙa masa wayar hannunta tana faman rau rau da idanunta.
Kallo guda yay wa sauran yaran suka bar falon sannan ya dubi rauda wadda takusan sakin fitsari a wando dan tsoro tare da cewa "wannan yazama na ƙarshe dazan kuma kamaki da waya a hannunki and kuma dan ALLAH kada ki fasa kawo min last position a result ɗinki"!! yakai maganar cikin tsawa, dasauri rauda ta mike cikin gudu gudu ta nufi ɗakinsu tana kukan zuci.
Kallonsa momy tayi "nifa bakaxo ba tsiyata dakai takura idan banda abunka ai cin jarrabawa ta ALLAH ce" sake hade ransa yayi tamau kamar bai taɓa dariya ba sannan ya miƙe tare da zuba hannunshi a aljihun jeans ɗinsa tare da kallon momy, "Ina wannan yarinyar take?" yabasar da maganar data ke masa sanin momy bata kaunar laifin ƴaƴanta wanda bada ban shi yaywa rauda haka bama da tuni sunkai ruwa rana.
Kallonsa tayi kamar bata fahimci miyake nufi ba sannan tace.
"Waye haka kuma ?" kai tsaye ya bata amsa "Amanar ALLAH mana, naga duk waÉ—ancan yaran anan ne ita bangantaba hajiya momy" yakai maganar cikin basarwa.
"Au sekacemin matar cushe kake nufi" tajefo mishi wannan maganar cikin gatse. "Eh ita Hajiya" shima ya bata amsar cikin son ya kawar da doguwar maganar dazata É—auko masa.
"Oh wayasan tana ina nikam bammq sakata a idanuna ba".ɗan ɗaure ransa yayi "haba momy nidai kawai zata koma part ɗina tsakani da ALLAH yar mutane surukarki ace bakisan ta kwana ba bare kisan tashinta haba momy dan ALLAH ki gyara badan niba amman idan maganata ta ɓata maki rai ALLAH ya baki hakuri" yakai maganar cikin sunkuyar da kanshi a ƙasa.
Wani tunani momy tayi kaÉ—an sannan tace masa "to kaifa dadina dakai saurin tunzura ai nabarta taÉ—an hutane kasan fa kunsha hanya" takai maganar tana ayyana zakaci ubanka tinda so kake najata ajikina zakasha kallo aikuwa sena mayar da ita mai gyara mana ko ina na gidan nan badai kafison kaga tana yawo a tsakaninmu ba to zata kuwayi amman na bauta bana soba.
Shiya katse mata tunani da cewa "hajiya bara naga kotai sallah" yatafi batare dayaji daga gareta ba yabarta kuma da sakin baki bude lallai sena mike tsaye cewart.
Seda ya leƙa jikin ɗalinsu rauda ya zari key ɗaya sannan ya bude dakin da batulan ta kwana hangota yayi kwance tana ta faman vacci kamar babu gove.
Da sassarfa ya karasa gareta yaɗanja ƙafarta kaɗan!
Cikin mayen bacci na bude idanuna waɗanda sukai jajur sabida baccin bai isheni ba ɗan tura bakina nayi gaba tare da watsa mashi wata jahilar harara sannan na miƙe ina ɗaga hannuna ina miƙa gami da salati ganin rana ta fito yasa na ware idanuna sabida banyi sallah ba.
Kallona yayi batare daya saki face É—inshiba kuma kamar bashi yagama shamin baki jiyaba amman yanzu jibi yadda yazo yawani haderai nima ganin hakan yasa naja nawa ran harma yafi nasa hadewa.
Kamar wanda akawa dole seyace wani abu naji yace "Ai canake a bayin kika kwana"! da sauri na kara kallonsa ashe yana sane kenan jiyan bangama tunanina ba nakuma ji yace "kinyi sallah?" girgiza kaina nai alamun a,a "Why?" yakuma jefomin amsar duk inajin kaifin idanunshi nayawo ajikina.
"Makara nayi wallahi" nabasa amsa kaina duƙe dan baxan iya jure ganin wannan mayen idanun nashi ba.
"Kitashi kiyi sallah amma kafin nan kifara wanka"! yana gama faÉ—in haka ya mike daga tsugunnon dayay zebar wajan.
"Ni sanyi nakeji gaskiya baxan iya wanka yanzuba" na basa amsa kai tsaye.....
"Agarinku na ƙazamai ake sanyi wallahi fatie idan nadawo baki wanka ba sena shanyeki"!!!
Chapter 30 · 0% Book details