← Book details Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 58

Sashe 1

Ko Ba So Akwai Kauna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                       1

Ƙoƙarin zame hannuna nake daga cikin nasa duk da tsananin jin daɗin dana kasance dashi acikin wannan lokacin amman  bai saka na yarda dana shantake tare dashi ba har hakan yajawomin matsala babba............, Cikin tsananin shauƙin so yakuma jawo hannuna zuwa kan cinyarsa yana mai haɗe hannunsa danawa cikin sauri na kuma zamewa akaro nabiyu.

Tare da turo ƙaramin bakina gaba ina matso ragowar hawayen dasuka zubomin.

'Haba beby na har yanzu kin kasa sabawa dani kamar wani dodo haka kikemin yayin da muka kasance wuri ɗaya dake"   batare dana ce masa komi ba nafara kokarin buɗe marufin motar tasa domin nabar wajan.

Cikin tsananin mayen so yakuma kamoni har ina ɗan raɓar jikinsa kaɗan lock yasakama motar tashi sannan ya mayar da seater baya tare da kuma riko hannuna akaro na biyu"haba beby na yaya kike guduna nane sekace babu amana" wani tuƙuƙun haushine ya tokaremin maƙoshina har ina jin babu dadi acikin zuciyata.

"Amman dai kasan yadda mukai dakai ko ABDUL sarai kasan halin umma matuƙar ta leƙa ɗaki bata ganni ba yanzu seta haɗa min gayya akaina"naƙara faɗin maganar cikin alamun jimami!

"Nasani mana beby" yafaÉ—a yana kuma zura yatsun hannunsa cikin nawa da dubara na samu na zare hannuna acikin nasa tare da É—aukar Æ´ar jakata ina mai kokarin mika hannuna domin na buÉ—e lock É—in motar.

Bai cemin komi ba illah hannun sa daya mika cikin É—an akwatin aje kuÉ—in cikin motar tashi tare da É—ebo kuÉ—i masu yawa yana kokarin xuba min acikin jakata.

Harara na watsa masa tare da cewa....haba ABDUL sau nawa zan gaya maka nibadan kuÉ—in ka nike sonka ba dan ALLAH nake sonka akullum fatana ALLAH yabaka ikon fitowa kazo ai maganar aure.

Murmushi naga ya ƙago akan fuskarsa tare da cewa "haba beby sau nawa zan gaya miki cewar auren mu kamar anyi sa angama ne kawai kiɗan ƙaran lokaci insha ALLAH dady na dawo wa zakiji maganar mu soon.

Murmushi na ƙago akan fuskata tare da cewa "kai amman harka sakani nishaɗi cwt heart oh ni ƴasu ranar yaya zakaga murna" nafaɗa tare da waro idona waje.

"Amman mai yasaka kai baka son zuwa kofar gidanmu nasan wallahi abba ze barka tunda dai nai candy ai"  seda yay jim sannan yace "a,a beby ba haka bane boye neman mu nake bayan haka kuma kinga nan yafi mana sirri ga mota ga tintack waye ze gammu bare ya saka mana ido.

Seda nai tsuru sannan nace "tokai mai ya ruwanka da Æ´an saka ido kaida zamuyi aure?" bazaki gane ba beby amman nan gaba kaÉ—an zaki gane ammafin boyewar danake.

"To ALLAH ya jiyar damu alkairi"   amin yafaɗa tare da mayar da kansa ya sunkuyar akan kujerar motar.

Da sauri na bude motar tare da fita daga cikinta tsaki naja lokacin danaji ya miko hannun sa ya shafi mazaunai na, ban tsaya jin ta tasaba nai wuff na shige lunkun gidanmu ganin anata kiran sallar isha'i ne yasaka na mayar da ajiyar zuciya tare da hamdala sanin abba baya gida yanzu yay masallaci.

Jakata a hammata ta nai soron gidanmu kofar farko tana bude ta biyu ce a rufe cikin sanÉ—a na saka hannuna na budeta tare da kokarin shiga cikin gidannamu.a

Na kawo kai shima ya kawo kai ze futa ina tunanin masallaci ze tafi dannaga hannunsa ajiƙe sannan kuma yana ta kokarin ɗaura agogon hannunsa.

Karo muka kusanyi dashi cikin sauri na kauce tare da bashi hanya danya wuce tsaki naji yanaja kaÉ—an kaÉ—an tare da aikamin da kallon daga ina kike zakici ubanki!!!

fuww ya wuce cikin tafiyar sa ta jaruman maza masu jini ajika da sauri nai tsakar gida inafaman mai d numfashin tsoro domin nina san haÉ—uwata da *YA HAIDAR* bazata min daÉ—iba.

*2*

Da sassarfa na ƙarasa cikin gidanmu ALLAH ya taimakeni da ƙarar generator shiyasa umma bataji sanda na buɗe kofan ba, hamdala nai lokacin dana ƙarasa cikin ɗakinmu da kallo ummi ƙanwata ta bini kafin ta buɗe baki tace min. "Anty Batula Wlh yau sekinci duka dan abba sau uku yana leƙowa ɗakin nan bai ganki ba, yacewa umma kina ina tace tun aiken datai miki gidan anty zee tun wuri 3 na yamma amman baki dawo ba" Mayar da bakina nai na rufe domin da masifa ce fall cikinna ganin locar kayana a bude amman jin abinda ummita ta faɗa yasa nai wuff na zauna gabanta ina mai neman jin ƙarin bayani.

Ban idda zaman nawa ba sega ƙanwata ameera mai bin ummi itama ta fito daga toilet ɗin ɗakinmu ƙugunta ɗaure da towel itama gabana ta ƙaraso tare da cewa..."Wlh kam da gaskene hmm ai gwarama faɗan abba akan na Ya Hydar dan wallahi zuwansa uku ɗakin nan yana nimanki dan ɗazun ma gidan anty zee yace zashi se kuma naji ya fita a motansa amman yau ƴar nan kinshiga uku!

Zaro ido nai waje tare da zuƙar majinar data zubomin batare dana shiryaba cikin kaɗuwar ciki nace "to waini duk wannan surutun dakuke min dan uwarku ina ruwanku dani munafukan banza da wofi daman haka kuke jira ai!

Dariya ameera tai tare da mikewa tabar wajan sanin halina ni yanzu ba ƙaramin aikina bane a kwashi ƴan kallo nida su, itakam ummi da ike sakuwa tace se cemin tai "anfaɗa ɗin banza uwar ƴan yawo ko gidan uban wama kikaje oho? munafukar ALLAH" ai ban jira ta ida zancen taba nai kanta ko mayafina ban cire ba nai kanta da duka kafin wani lokaci se ga dambe ta kaure.

Da hijabin sallah da carbi a hannun umma tayo dakin namu aguje tabiyo bayan ameera wadda taje ta gaya mata cikin salati umma take rabamu tana cewa "yau nikam na shiga uku! yara kamar kaji musamman ke" ta jawoni tare da É—akamin duka ta hankaÉ—ani gefe.

"Wallahi nasara wannan jarabar taki tawa kika ƙwaso adangi kije can kisha yawonki sannan kidawo kina jibgar min ƴa da wannan manya hannayen naki kamar na doya" tukunna ma dan ubanki daga gidan ubanwa kike?"....tura baki nai gaba cikin kuka! tare da cewa....

"Nidai an tsane ni agidan nan tsakani da ALLAH kowa ya rainani amman babu wanda za,a tsawatar wa karshe ma sedai abani rashin gaskiya....hakama ɗazufa hanif wallahi wayata ya ɗauka yana danna min daga nai magana aka hau yimin faɗa" naƙarasa maganar ina shura ƙafata a ƙasa.

Cikin kuka! ummita tace "wallahi umma itace da tsokana bafa wani abu nai mata ba tahau jibgata" nasani ummi cewar umma' wannan kazar uwar ƴan dambe ai wallahi ALLAH ya shigomin da ALIYU zakici ubanki ne babu ruwana" umma ta ƙarasa faɗa tana kokarin daɗa kaimin wani dukan😭da sauri nai gefe waigawa nai naga ameera tana faman yimin dariya.

Dawani irin zafin nama nai kanta tare da danƙo gashinta nafara makata da ƙasa babu abinda kakeji se ihun! ameera tana niman taimako.

Salati ummammu ta ɗauka tare da yowa kaina tana ƙoƙarin ɗaga ameera, cikin tashin hankali umma ke cewa "na shiga uku ni Aishatu kekam batula mi kikeson zamane, daga wannan se wanna amman ALLAH ya shigo da ɗayan biyu"

Umma na rufe baki sejin ƙamshin mayen turaren sa nai ɗiff naji ɗakin ya ɗauka se amon muryar umma tana cewa..."ALLAH nagode maka gwara da ALLAH ya kawomin kai Aliyu"....da wani irin sauri na ɗago tare da sakin ameera.

Haɗa ido mukai da yayan namu yana tsaye ajikin ƙofarmu hannunsa harɗe akan kirjinsa yawani tsareni da mayun idanunsa yana bina dawani shu'umin kallo......!

Taku ɗaya biyu nai zanbar wajan babu inda nai waiwaye kamar cikin banɗakinmu kokarin shiga ciki nake na kulle sedai na makaro kafin nai wani motsi tuni yasaka ƙafarsa ya taɗeni na faɗi.

Saka ƙafarsa yay ya hankaɗeni wanda tuni su ummammu sunbar wajan hatta ga amera mai kuka itama tabar wajan waige nai naga dagani seshi adakin namu kuka! nake kokarin yi amman ina babu dama ganin irin mugun hargitsatstsen kallon dayake aikamin.

Cikin kakkausar murya wadda tafi kama da dirar alburushi acikin zuciyata naji yace "kisameni a ɗakina" bai kuma cewa komi ba yabar wajan tare da barin ƙamshin turarensa a ɗakin namu.

Kuka! tsoro tsana nadama takaici haushi baƙin ciki, susuka sakani kwanciyar ƴan bori awajan sanin wanene yay kirana hango irin baƙar azabar dazan sha a yanxun su suka saka nai wunzir na tashi tare da nufar bakin kofa dan zuwa amsa kiran DODON NAWA cikin tsananin bargaba.......!

*3*
Ko kallon gabana banayi haka nake nufar ɗakin ya hydar wanda abba ya ware masa shi daban acikin ɓangaren gidanmu na hannun hagu ban wani sha wahala sosai ba duba da yadda nake zuba sauri amman duk da haka seda ya rigani ƙarisawa.

Daga bakin barandar falon sa naja na tsaya batare danai yunƙurin shiga cikin ɗakin nasaba, gudun kada na kuma mistake irin na kwanaki da umma tace naje nakai mashi abincinsa ɗaki.

Da karan banina maimakon dana aje masa abincin falon nabar wajan ina ganin baya nan se kawai na hau kunna masa t.v tun kafin na gama haɗawa sejinsa nai akaina faɗin irin dukan dayay minma ranar ɓata bakine domin na daku ba kaɗan ba shiyasa wannan karon naiwa kaina faɗa tun wuri naja na tsaya anan ɗin.

Nakai kusan minti goma a tsaye har nagama wannan tunanin ya hydar baice na shigoba ga uban sauro na cizona ga yunwa ga kashin daya matseni duk abun duniya ya taru yay min yawa ni É—aya.

Seda nai kusan 30mnt sannan naga ya zuge glass É—in window'n É—akinsa tare da saka hannunsa guda ya yimin inkiya akan nashigo.

Cikin mutuwar jiki na ƙarasa shiga cikin falon nasa abakin ƙofa na tsaya na goge fuskata saninsa mutum marar son yaga hawaye na zuba a idanun mutum, kafin na karasa cikin ɗakin ƙamshine yafara min ziyara gawani mugun sanyin A/C dayay min ƙawanya acikin kaina sam bana son sanyi ni arayuwata dan haka naja wuri guda na takure ina makyarkayata!

Seda nai wajan minti biyar sega shi konace naji sallamar tasa watan ƙamshin mayen turarensa acikin hancina.....kafin na ɗaga idona na kalleshi sau ɗaya takkk!!

Sannan na kauda kaina, sanin halinsa na baya son kallo ku guda, Sanye yake cikin kayan shan iska farare tass se uban ƙamshi yake zubawa.
Chapter 1 · 0% Book details