Sashe 9
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sen ya fusata da jin kalaman Omar, ransa ya ɓaci sosai ya ce, "ƙarya ka ke yi, ƴata ta wuce ta fara soyayya da irin ka wallahi, sai dai aikin asiri. Kuma wallahi ka yi gaggawar sanar da ƴar uwarka inda ka ɓoye asirin, in ba haka ba kana gab da aikata aikin dana sani." Zai yi magana Didi ta riga shi ta ce, "Ku yi haƙuri don Allah, ku bani shi mu tafi zamu tattauna dashi zan yi iya ƙoƙarina wajan ganin an karya asirin."
Omar ya kalle ta da mamaki ya ce, "ki daina faɗar wannan maganar fa, babu abinda na aikata kin sani. Ita tazo har gida ta zube a gabanki tana roƙonki ki saka na sota, na ji tausayinta saboda raunin da take tare dashi har naji a raina zan iya taimaka mata na saurarenta..." ya faɗa yana kallon su Mum da suke kallon sa.
Ya sake kallon Didi ya ce, "Dan na taimaka mata na bata aron kaɗan daga cikin lokacina sai ya zama nayi mata asiri?. Didi kar ki damu dani, ai ba yau na fara shan wahala ba, ba yau aka fara dukana ba. Wannan kaɗan ne ba mai yawa ba, kar ki da wannan komai zai wuce. Amma na ƙara ilimi, na kuma ƙara sanin meye duniya, na kuma gasgata zancen da ki ke yawan faɗa min a kullum. Ko a nan zan gama rayuwata zan tabbatar miki da Omar ɗin da kika sani a baya yana nan, hatta shi Senator bazai manta da Tiger yana da rai ba."
Mum ta kalli Senator cikin ɓacin rai bata sake cewa komai ba ta fice shima bai yi magana ba ya fita. Omar ya yi murmushi dan so yake ya cusa musu haushi a zuciyarsu kuma ya yi, ya kalli Didi ya ce, "kar ki damu, babu abinda zai same ni zan kuma fito na dawo na zauna tare dake in sha Allah. Ki je kawai."
"Wahalar da kai suke yi ko Omar? Naga nan bai yi kama da gidan yari ba, Ina ne nan?."
"Ai daman ba prison suka kai ni ba, wani gida suka fara kaini kafin su kawo ni nan. Duk ƙarfin mulkin da suke ji dashi basu isa su kaini prison ba tare da laifi ba, in nayi laifin ma sai dai kotu ta tura ni prison ba dai su ba. Amma zasu iya yi min sharri in suka ga dama, ban san meyasa basu aikata ba har yanzu. Ki kwantar da hankalinki Omar ɗinki zai dawo." Hawaye ya share mata da hannayensa da suka yi duhu ga farce ya taru.
Didi kuka take yi sosai ta ce, "Duk yadda zanyi dan ganin na kuɓutar da kai zan yi Omar."
"Kar ki wahalar da kan ki Didi, ki kwantar da hankalin ki. Tare da wa ku ka zo?."
"Bashir da Tukur, Hajja ce ta bada mota aka kawo mu. Omar murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce, "shikenan ki je kawai." Didi ta ce, "Bana so na barka a nan Omar." Ƙarfin hali yake yi kawai yana yi mata magana saboda kar ya sakata a damuwa. Daƙyar ya ce, "Ki je Didi." Fita tayi tana kallon sa shima a lokacin suka koma ta inda suka fito.
Didi da ta fito bata ga motar da suka zo ba hankalinta ya tashi gashi bata san gari ba, ta fito bakin titi ga taxi nan tana yawo amma bata san Ina zata ce zata je ba. Allah ya taimake ta da waya a tare da ita ta kira Bashir ta faɗa masa, ta tura masa location ta whatsapp yadda zasu fi ganewa. Da yake driver Hajja ya san Abuja ba jimawa ya ƙaraso suka ɗauki Didi zuwa inda suka sauka.
[20/09, 4:25 pm] +234 906 075 3382: KRB2P005
Arewabooks@nanahaleema11.
Didi bata ɓoyewa su Bashir abinda ake ciki ba ta faɗa musu yadda suka yi dasu, gabaɗaya ta canja yanayin damuwa ta sake mamaye ta ba kamar in ta tuna halin da ta ga ƙanin nata sai zuciyarta karye ta fashe da kukan tausayinsa. Washe gari da wuri suka ɗauki hanyar Kano, da suka shiga cikin gari kai tsaye gidan Hajja suka shiga suka same ta a zaune da hijjabi ga kuma babban mutum a kan carpet a zaune yana gaisheta da matuƙar girmamawa.
A sanyaye Didi ta shiga falon Hajja ta bita da kallo haka Salma ma da take zaune. Abiy ya kalli wacce ta shigo, Didi ganin Abiy a zaune sai Didi ta gaishe shi a sanyaye ya amsa Hajja ta ce, “Aisha ce, Aisha maƙociyarmu, Yayar Omar.” Nan da nan fuskar Abiy ta washe zuwa fara’a ya ce, “Allah sarki, na gane ta yanzu. Ina Omar ɗin? Yana nan lafiya?.”
Hajja ta ce, “ba lafiya ba gaskiya, wata matsala ce ta saka har aka kama Omar ɗin a Abuja.” Abiy ya ce, “Subahanallah! A Abuja kuma aka kama shi?.” Hajja ta ce, “ƙwarai kuwa, hanyar da za a fito dashi ma muke so saboda bashi da laifin komai aka kama shi.” Abiy ya girgiza kai zai yi magana aka kira shi a waya ya kalli wayar ganin kiran mai mahimmaci ne sai ya kalli Hajja ya ce, “Hajja zan koma ana kirana, Amma zan saka a bincika maganar Omar ɗin in sha Allah.”
Hajja ta ce, “Allah ya yi albarka, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi.” Da amin ya amsa ya ajjiye mata kuɗi kamar ko yaushe, ya bawa Salma da Didi kafin ya tashi ya fita.
Kawai sai Didi ta fashe da kuka mai sauti Hajja ta riƙota ta ce, “Don Allah ki bar kuka ki huta tukunna sai mu yi magana. Jikinki ma ya yi zafi sosai Aisha da alama zazzaɓi yana damunki.” Salma ta ce, “Da gajiya ma a zazzaɓin da yake damunta Hajja, ta yi wanka ta sha magani ta kwanta zata ji daɗi.” Hajja ta ce, “kin ji abinda likita ta ce, don Allah ki yi shiru ki daina wannan kukan. Ba ki ji mahaifin Nayla ya ce zai san abinda zai yi ba? Na san zai yi, kuma daƙyar in bai san shi Sanata ɗin ba.”
“Hajja bazai amince ba, baza su bar Omar ba Hajja. Sun ce ya yiwa ƴarsu asiri shiyasa take sonsa har ta fita daga hayyacinta. Wallahi Hajja Omar bai nata komai ba, har gida tazo tana yi min kuka na saka Omar ya sota. Kuskuren Omar da ya bari ya fara sonta, kuskuren Omaar da ya je ne gidan Sen. Hajja kin ga yadda suka mayar min da Omaar? Kin ga yadda ya koma Hajja….?” Ta faɗa tana jan kalmar ƙarshe tana kuka sosai.
Hajja ta ce, “ki yi haƙuri komai zai wuce in sha Allah, ki daina tayar da hankalin ki kin ji.” Didi ta ce, “shi yake jawowa kan shi Hajja, a gaban su a jiya baki ji irin maganar da ya dinga yi ba, sam Omar baya riƙe maraicinsa, baya tuna matsayin da yake dashi. Na rasa wanne rashin tsoro ne haka da Omar bashi dashi, lamarinsa yana bani tsoro sosai. Kina ganinsa Hajja kin san yana cikin azaba, amma ya dake yana faɗa musu maganganu masu ciwo.” Hajja ta ce, “ni maganar ce bana so ki yi, ki je ki yi wanka ki huta kin ji?.” Ba dan ta so ba Hajja ta saka ta shan tea sannan tayi wanka ta sha magani ta kwanta ba dan tana jin bacci ba. Haka Didi ta kwana da zazzaɓi mai zafin gaske, sai da Salma ta yi mata allura sannan ta iya bacci a safiyar ranar jum’a.
Nayla ta shigo garin Kano a ranar ana gab da shiga masallaci domin yin sallar juma’a, gidan su na Kano wanda su Abiy suka sauka ta wuce ta ajjiye kayanta tayi wanka ko hutawa bata yi ba ta fito falo. Da Mama ta haɗu ita da Jidda a zaune ta kalli Mama ta ce, “Mama zan je gidan Hajja sai zuwa dare zan dawo tunda event ɗin yau sai dare.” Mama ta ce, “Baki huta ba fa Nayla, zuwan ki kenan kuma ki tafi gidan Hajja?.”
“Bana so lokacin masallaci ya yi a rufe hanya ban tafi bane shiyasa.”
“Baza ki yi makeup ɗin ba?.”
“Bazan yi ba gaskiya.” Twiny ta ce, “bara nazo na raka ki gidan Hajjan.”
A motar Twiny suka tafi gidan Hajja lokacin ana ta sallah a masallaci. Bata ɗauka zata tarar da Hajja ba dan tasan zuwa sallah duk sati da ita ake yi a masallaci, amma sai ta tarar tana nan ta tasa Didi a gaba tana ta rarrashinta. Shigar su falon ya saka Salma ta ce, “A’a Nayla, saukar yaushe?.” Duk sai suka kalle ta har Hajja, Hajja ta bita da kallo ganin ta yi wani iri itama kamar ba ita ba.
Fuskar Hajja ta washe ganin jikarta ta da kuma ƴar uwarta. Ta ce, “Hauwa’u da Jidda, sannan ku da zuwa.” Twiny tayi dariya ta ce, “Hajiya Hajja, barka da rana.” Hajja ta amsa fuska a sake tana tambayarta Maman ta Jidda ta amsa da kowa yana lafiya. Da Didi suka gaisa ganin bata da lafiya sai tayi mata sannu. Didi ta kalli Nayla ta ce, “ƙanwata Nayla ya kika tsaya?.”
Nayla ta ce, “Hajja Didi bata da lafiya haka shine ba a faɗa min ba?.” Hajja ta ce, “kema ai baki da lafiyar, kalli yadda ki ka koma.” Share batun Hajja tayi ta dawo kusa da Didi ta ce, “Didi sannu, me ya same ki haka?.” Didi tayi murmushi ta ce, “Zazzaɓi ne kawai Nayla, bayan shi babu komai.”
“Sannu Didi, Allah ya baki lafiya. Gabaɗaya kin rame.”
“Amin Nayla. Kema kin rame, na faɗa miki ki daina cewa zaki rage ƙiba, baki fa ƙibar kirki ki ce zaki rage? wallahi kin fi kyau da jikinki.” Nayla tayi ajiyar zuciya kafin ta kalli Hajja da take kallon ta sai tayi murmushi ta ce,”Hajiya Hajjata, na yi kewarki.”