← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 52

Sashe 39

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kar ki wahalar da kanki bana buƙata, bana so in kika yi ma zaki ɓata lokacin ki ne, ko wacece ita zaki ɓata mata lokaci da rayuwarta ne dan ni ban shirya aure ba. Gwara ki bari taje ta auri wani daban da dai ace ta aure ni, zaman aure da wacce babu ita a rayuwara tun farko babbar matsala ce. Na hutar dake, bance ina so ba, dan haka ki bar maganar nan."

"Baza ka iya kallonta a matsayin matarka ba saboda ni?".
"Haba Didi! Na faɗa miki ban so a bar maganar nan, in ma kina niyar yi ne kar ki yi na hutar dake bana buƙata, zama ni kaɗai baya damuna kinfi kowa sanin haka. Wacce mace zaki ɗauko ki kawota cikin rayuwata ba tare da sanina ba? Don Allah ki adana wannan tunanin, kar kuma kiyi wannan gangancin in ba haka ba zan ta ɓata miki rai, ki ƙyale ni!" Ya faɗa a kausashe yana kallonta dan ta katse batun shi ya gaji da wannan kalaman nata.

Ajiyar zuciya tayi ta rasa da wacce hanya zata yi masa magana ya fahimta, me zata ce masa ne wai? Ta ce masa mahaifin Nayla ya zo ya baka auren ta? To Akan wanne dalili ya aura masa ita? Meyasa yayi hakan?. Ganin ta tafi duniyar tunani sai taji ya murza yatsunsa a kusa da fuskarta sun bada sauti, ta kalle shi ya ce, "Ki faɗa min damuwar ki Didi!" Ya faɗa cikin kakkausar murya yana kallonta. Didi ta buɗe ido tana kallonsa ta ce, "babu komai na faɗa maka, zaman ka haka ne bana so, ya zama dole na nema maka matar aure koda baka so."

"Didi ki daina ƙoƙarin raina min hankali mana, na sanki na san halin ki kar ki manta da wannan. Wallahil azim akwai wani abu a zuciyarki, ki sanar dani damuwarki in kuma baza ki faɗa min ba kice baza ki faɗa ba." Didi ta kulle ido ta buɗe sai ta tashi tsaye ta ce, "Akwai abinda zan ɗauka a kitchen, na san ba amfani kake yi dashi ba ni kuma ina so. Gwara na haɗa kayan na ajjiye kar na manta" ta faɗa tana shiga cikin kitchen ta barshi a wajan yana kallon ta cikin tunanin abinda yake damunta.

Da ta fito ya fita bata sake ganin sa ba, dan ɗaki ya shiga ya kwanta saboda ciwon kan da yake damun sa. Sai da magriba sannan ya fito yayi alwala ya same ta a tsaye a tsakar gida ta kalle shi ta ce, "zan shiga wajan Hajja." Kai ya ɗaga kawai tazo ta wuce shi.

        Da sallama ta shiga gidan Hajja aka amsa mata, abinda ya bata mamaki bai wuce Nayla da ta gani a zaune ba tana yi mata oyoyo. Murmushi tayi ta zauna ta ce, "mutanen Kaduna, saukar yaushe?." Nayla ta ce, "saukar jiya, kuma gobe zan koma. Har gidan ki muka je ɗazu bakya nan." Jin hakan sai Didi ta bita da kallo da alama itama bata san da auren ba. To me hakan yake nufi wai? Meye dalilin Abiy na aurawa Nayla Omar ba tare da ta sani ba?.

Hajja ce ta katse mata tunani suka gaisa kafin ta kalli su Nayla ta ce, "naje gidan Kawu a can na yini sai yamma nazo nan, Meyasa baku yi min waya ba?."
"Muna ta kiran ki taƙi ta shiga shiyasa."
"Ayya, amma kun kyauta na so kun same ni." Nayla tayi murmushi ta ce, "zamu dawo wani lokacin."

Hira suka cigaba da yi da Hajja da kuma Salma dan ita dai Nayla tayi shiru bata magana. Didi ta taɓata ta ce, "Nayla ya dai?." Nayla tayi murmushi ta ce, "babu komai, anyi kiran sallah bara naje nayi sallah" ta faɗa tana shiga ciki duk suka bita da kallo.

Didi tausayi ma take bata wallahi, ko meyasa mahaifinta yanke hukuncin aura mata Omar oho, gashi da alama itama bata sani ba, meye amfanin yin hakan da yayi Allah ne ya sani. Duk tashi sukayi akayi sallah kafin Didi tayi musu sallama ta ce zata tafi, Nayla da Salma suka raka ta bar ƙofar gıda a nan suka ga motar AbdulHamid da alama ita yake jira.

Didi ta ce, "Don Allah kuzo ku taya ni ɗauko kayan a ciki, kayan kitchen ne wanda na san ba amfani dasu zai yi ba na tattaro kayana." Salma tayi dariya ta ce, "wallahi gwara da kika ɗauko" ta faɗa suna bin bayanta zuwa gida. Ƙirjin Nayla bugawa yake yi sosai ba kamar da suka shiga tsakar gidan, Nayla ta ɗauki leda ɗaya Didi ta ɗauki biyu Salma ma ta ɗauki ɗaya.

Daga falon Omar ya fito sanye da ƙaramar riga mai gajeren hannu mara nauyi, sai wando three quarter. Kallon sa tayi ta ce, "Omar sai da safe."
"Ki kwana Lafiya" ya bata amsa yana niyar wucewa ba tare da ya kalleta ba.
"Ya ciwon kan?" Ta tamabaya tana kallon sa. Juyowa yayi ya kalleta ya ce, "naji sauƙi."
"Baka ga su Nayla da Salma ba? Baka yi musu magana ba."

Kallon su yayi, Nayla dai kanta yana ƙasa Salma ce ma take iya kallonsa kamar zai yi magana sai ya fasa, ya ɗaga ƙafa da niyar barin wajan sai ya juyo ya kalli Didi ya ce, "na rasa meyasa kike son saka ni a abinda bai shafe ni ba" yana gama faɗa ya wuce ya barta a wajan.

Wani iri taji a zuciyarta, dan ita ta san yanzu Nayla matarsa ce shida ita ne basu sani ba, hakan da yayi ya tabbatar mata da karɓar Nayla zai yi masa matuƙar wahala, duk ganin da yake mata gashi bai saba da ita ba. Ita ta ɗauka ya saba da ita har zai iya yi mata magana, tunda shi magana da wanda bai saba ba babban tashin hankali ne a wajan sa.

Didi ta kalli Nayla bata ce komai ba sai Salma da tayi dariya ta ce, "Kema Didi ban da abin ki ina Omar inayi mana magana? Mu je" ta faɗa tana yin gaba duk suka bi bayanta Nayla dai kanzil bata ce ba.

Har motar suka saka mata kayan tayi musu godiya suka gaisa da mijinta sannan suka wuce gidan Hajja. Tunda ta shiga motar shima ya lura tana cikin damuwa mai yawa, ya kalle ta cike da kulawa ya ce, "Ya dai? Akwai abinda ya faru ne?." Didi ta ce, "Akwai wallahi. Kaga yarinyar nan da kuka gaisa mai blue ɗin mayafi?."
"Eh na ganta."
"Itace Nayla, itace wacce ta yi silar da aka fito da Omar daga wajan Senator. Ɗazu mahaifinta yaje har gidan Kawu ya saka aka ɗaura aurenta da Omar."

AbdulHamid ya ce, "Iyee! aure da Omar  kuma!?." Didi ta ɗaga kai ta ce, "wallahi, yanzu maganar da nake maka ita matar Omar ce wallahi."

"Ikon Allah, to garin ya haka ta faru?. Daman suna soyayya da Omar ɗin ne?." Didi ta ce, "ita dai tana son Omar, na ji da kunnena suna tattauanwa a ranar ɗaurin aurena da kai. Ta bani matuƙar tausayi, domin soyayya bata yi mata adalci ba da ta saka ta fara son Omar. Ita ba tsararsa bace, ta wuce ajinsa nesa ba kusa ba, ko masu gadin gidansu sun fi Omar matsayi wallahi. Abinda ya bani mamaki ya kuma ɗaure min kai shine; mata guda biyu kyawawa, masu asali da iyaye masu kuɗi da faɗa a ji a ƙasar nan, mata masu ilimi, aji da wayewa sune suke yiwa Oamar irin wannan soyayayar? Anya ta baki Senator ba asiri Omar yake yi musu ba kuwa?."

Abdul yayi dariya ya ce, "Wanne irin asiri ana zaune Lafiya? Kawai haɗuwar jini ce. Kin san mata suna son farin namiji kyakykyawa mai saje kamar Omar ɗin."
"Amma haɗuwar jinin su rasa da wasu haɗa jini sai Omar? Mata kamar su ace sune suke sonsa ba shine yake sonsu ba?. Har gwara Narma ita ya furta min yana so, to Nayla fa da take matsayin matarsa yanzu?."
"Ni maganar auren ce ta ɗaure min kai, haka kawai mahaifinta ya aura masa ita kamar auren ƴar tsana?."
"Wallahi nima ya ɗaure min kai, abin mamakin kuma a yanayin yarinyar na tabbatar da bata san da auren ba kamar yadda Omar bai sani ba. Meyasa mahaifinta ya aura masa ita?."

"Ko ya gano tana sonsa ne?."
"Dan ya gane tana sonsa kuma sai ya ɗaura mata aure dashi yau kwatsam? Gaskiya akwai lauje a cikin naɗi a lamarin nan." AbdulHamid ya ce, "yanzu shi Omar ɗin ya sani?."
"Waye zai faɗa masa? Kaf duniya ni kaɗai ce zan iya tunkararsa da wannan maganar, to nima ɗin na rasa ta wacce hanya zan faɗa masa. Jurwaye mai kamar wanka nayi masa, nace masa na kai matsayin na bashi mata ya zauna da ita, ka san me ya ce?."

Ya girgiza kai alamun a'a Didi ta ce, "cewa yayi zai iya karɓa tunda ni ce babu yadda zai yi, amma bazai iya kallonta matsayin mata ba, zai dai zauna da ita gida ɗaya matsayin wacce na ajjiye masa amma ba matarsa ba." Abdulhamid yayi dariya ya ce, "Wallahi Omar yana burge ni, yanayin ƙarfin guiwarsa da gaskiyarsa tana matuƙar burge ni a halayensa. Yanzu ya zaki yi?."
Cike da damuwa ta ce, "Dole dai ni zan faɗa masa, amma nima ban san ta wacce hanya ba."

"Zaki samo hanya, ki nutsu kawai, ai yana jin maganarki zai yi duk abinda kika ce masa." Didi ta ce, "hmm baka san Omar ba ne, a dai yi shiru kawai" ta faɗa tana kawar da kai zuciyarta cike da tunanin dalilin auren Nayla da Omar lokaci guda haka.
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P022

Narma tana tsaye a tsakiyar bedroom ta idar da sallah tana ninke sallaya Ashraf shiga yana binta da kallo. In ba da sexy dress ya ganta ba bata burge shi gabaɗaya, yana so ya ganta da kayan da suka bayyanar da surar ta, in ya same ta da hijjabi ko riga mai girma sai yaji haushi ya tokare masa ƙirji lokaci ɗaya sai yaji tana bashi haushi, amma da zarar ya ganta a yadda yake so sai yaji babu abinda yake so sama da kasancewarsa da ita.
Chapter 39 · 0% Book details