← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 52

Sashe 46

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na bar mu ku komai a hannunku akan wannan, ku yi duk abinda ya kamata, koda auren ku ke ganin za'a samu matsala wuƙa da nama yana hannunku, ku yanke hukunci ba sai an sanar dani ba." Abiy ya faɗa tana kallon Daddy.

Daddy ya ce, "ai aikin gama ya gama Alhaji Abdullah, amma duk da haka zamu ƙoƙarta mu gani. Allah ya shige mana gaba." Aka amsa da amin suka cigaba da tattauanwa kafin yayi sallama ya wuce dan Kaduna zai koma.
[24/09, 3:38 pm] +234 906 075 3382: KRB2P025
ArewaBooks@nanahaleema11.

Bayan fitar Abiy su uku suka cigaba da tattaunawa akan lamarin Nayla, amma basu da abinda zasu yi tunda shine mahaifinta yana da ikon yanke hukunci a kanta a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama. Kasancewar Hajja tana gidan Daddy gabaɗaya suka shiga suka same ta, a wajan Hajja suka samu ƙanwar su Mama Sa’adatu a tare da Hajjan.

Hajja ta kalle su ta ce, “Har ya tafi?.” Daddy ya ce, “ya tafi.”
“To ya aka yi?.” Basu ɓoye masa komai ba suka sanar da ita Daddy ya ce, “Kuma baya dana sanin aura mata shi ya ce har yanzu. Abinda na lura dashi ransa ya ɓaci sosai, ya yanke hukunci cikin fushi da ɓacin rai, kuma itama Nayla bata kyauta ba ban yi tunanin zata aikata haka ba. Amma mun sanar dashi zamu zauna da yaron, in ba a zauna dashi a san yana sonta ko baya sonta ba zaman gidansa bazai yi mata daɗi ba. Ya ce ya bar komai a hannun mu, mu yiabinda muke ganin ya dace.”

Mama Sa’adatu ta ce, “Gaskiya Nayla bata kyauta ba, amma ni ban ga abinda zai saka ayi mata aure irin wannan a maganar nan ba.” Hajja ta ce, “Koma dai meye shine ya haifeta, duk abinda zamu ji akan Nayla bayan a sa ne. Ku bar shi da hukuncin da ya yanke kawai, abinda zai faru mu yi mata addu’a kawai zai fi.”

Mama Sa’adatu ta ce, “Hajja aure lokaci ɗaya haka? Babu sanarwa, babu kuɗin aure ba lefe?. Kuma mijin ma ba wani na kirki ba, ai sai ace dan mahaifiyarta bata raye ne ya saka muka zuba ido akayi mata wannan auren. Yanzu in da ace tana da rai hakan zai faru ne?.”

“Koda tana da rai hakan zai faru tunda Allah ya rubuta, kawai a bar maganar nan mu yi mata addu’a. Yana girmama mu sosai, kar yaga kamar mun cika zaƙewa akan lamarin iyalansa. Mu yi mata fatan Allah ya sa hakan ya zama alkhairi.”

Duk suka amsa da amin ba dan hakan yayi musu daɗi ba sai dai babu yadda zasu yi ne, amma da suna da iko Nayla baza ta zauna da Omar matsayin mijita ba ko kusa.

Bayan Kwana biyu.

Har ranar laraba Omaar bai san da wannan labari ba, harkokin gabansa kawai yake yi domin kuwa Allah ya dafa masa a sana’ar da ya saka a gaba, sosai yake ganin alkhairi da kuma cigaba fiye da tunaninsa. Shiyasa ya mayar da hankali ya ke kuma ƙaro sani akan abinda yake yi.

Kamar yadda Mama tace ta turo da kayan gidan Nayla a gama ɗaura komai, hatta kayan kitchen a cikin kwana biyu an zuba gida ya fito yayi tar kana kallonsa ka san gidan amarya ne. Mama ce kawai take shagalinta a wannan ɓangare amma ko Abiy ɗin baya bi ta kai balle kuma Nayla da ta koma kurma saboda bata son magana.

A daren ranar larabar suna zaune ita da Jidda da ta zo Kaduna saboda maganar, ita Salma suna hira a kusa da Nayla, Nayla dai bata saka musu baki su ne suke hirar su ita kam abinda take tunani daban. Mama ce ta shigo falon da sallama suka amsa sallamarta, ta kalle su ta ce, “ya kamata ace an yiwa Nayla gajeren gyaran jiki, dan haka gobe mai gyara zata zo zata yi mata abinda ya samu, sannan zata yi mata ƙunshi tunda jibi ne tafiya Kano.”

Gaban Nayla ya faɗi har sai da ta runtse idanu bata kalli Mama ba. Jidda ta ce, “Haba Mama! Wanne irin gyaran jiki a cikin wannan yanayi?. Don Allah Mama ki bar faɗin haka wallahi bana son ji kwata-kwata. Ba ma fatan auren nan ya tabbata balle a dinga tunanin wani gyaran jiki ko ƙunshi.” Mama ta kalli Jidda ta ce, “ai kam dole za a yi, tafiya Kano ranar juma’a babu fashi ranar zata tare a gidanta. Haka za’a kaita babu wani gyara?.”

Jidda ta ce, “Haba Mama don Allah, ki daina faɗar haka mana. Auren nan fa ba so muke yi ba.”
“Kece bakya so, amma Nayla tana matuƙar son mijinta ko Nayla?” Ta faɗa tana kallon Nayla. Nayla bata iya buɗe ido ba saboda haushin Mama da ta fara ji a zuciyarta, tunda daga abinda tayi mata akan Abiy shikenan ta fara jin wani abu akanta wanda bata san meye ba.

Mama ta sake cewa, “ku dai shirya gobe zata zo” tana faɗa ta fita daga falon. Bayanta Jidda ta bi sai suka haɗu da Jawad ya taho duba Nayla ya kalleta ya ce, “ke kuma ina zuwa?.” Jidda ta ce, “Wajan Mama zan je Yaya J, abinda take yiwa Nayla gabaɗaya bai kamata ba, ana cikin wannan yanayi amma Mama tana zancen wai zata kira mai ƙunshi da gyaran jiki ta yiwa Nayla?. wallahi ban ji daɗi ba, sai ta dinga ganin dan ba itace ta haifeta ba shiyasa take faɗar haka.”

Jawad ya ce, “ke ni fa na lura kamar Mama murna take yi da auren nan, gabaɗaya itace abin bai dame ta ba.” Jidda ta ce, “nima dai na lura daga zuwana gidan nan zuwa yanzu, ko ba murna takeyi ba bata nuna ta damu akan hakan.”
“Ki ƙyaleta karki bita, kije ku cigaba da rarrashin Nayla ɗin a hankali.”
“Amma Yaya Jawad wallahi ban ji daɗi ba, Nayla ta kasa magana gabaɗaya, kuma ga cousin ɗinta Salma, zata ga kamar Mama ce take son auren nan.”

Jawad ya ce, “ki ƙyaleta ki je kawai, zan san abinda zan yi.” Jidda ta koma ciki jiki a sanyaye ta zauna kusa da Nayla da kanta yake kafaɗar Salma tana hawaye. Dafata tayi ta ce, “Twiny don Allah ki yi haƙuri da abinda Mama ta ce.” Nayla ta kalleta ta ce, “Twiny me Maman tayi?.” Zata sake magana ta ce, “ki bari bana so, komai Mama tayi tana yi ne matsayinta na uwa a gare ni, Don Allah karki sake cewa komai.”

Jidda ta ce, “Yanzu haka zamu zuba ido a kai ki gidan Omat ba tare da soyayyarki a zuciyarsa ba?. Ni bani da tabbacin ma ya san da auren nan, in ya sani ya karɓe ki ko bai karɓa ba?.” Salma ta ce, “abinda yafi komai tsaya min a rai kenan.” Nayla bata iya cewa komai ba idanunta na kulle fuskar Omar na gilma mata a ranar ɗaurin auren Didi da yake tsokanar Didi.

Washe gari ranar alhamis da safe suna zaune gabaɗaya a falo ana breakfast saɓanin Nayla da take a gefe a rakuɓe. Abiy ya kalle ta ya kalli Jidda ya ce, “kin gama shirya mata kayanta? Gobe zata tafi gidan mijinta in sha Allah.” Jidda ta kalli Abiy a sanyaye ta ce, “Don Allah Abiy ka sake bata lokaci, ko zuwa nan da bayan sallah ne sai ta tare. Amma yanzu ba a shirya komai ba ace zata tare a gidan wani?.” Abiy ya kalle ta ya ce, “Haka ta ce miki?.”
“Ko bata faɗa ba na san hakan ne a zuciyarta Abiy.”
“Ke dai haka ki ke tunani, amma Nayla ba haka take so a zuciyarta ba. Ki barta taje gidan mijinta tayi ibada, zata fi samun lada a watan Ramadan ɗin a can.”

Nayla ta ɗago ido ta kalli Abiy suka haɗa ido sai ta mayar da kan ƙasa bata ce komai ba. Abiy ya ce, “Ku shirya komai, gobe daga nan za a kaita gidan Hajja, daga nan Hajja ta kai ta gidan mijinta. Na sauke nauyin da yake kaina a matsayina na mahaifinta.”

Jidda tayi ajiyar zuciya, ta kalli Mama ta ɗauka zatayi magana sai taga abincin ta ma take ci hankali kwance. Sai daga baya Mama ta ce, “jiya nayi magana da Zaliha da take Kano, tana tambayata ya aka yi haka ya faru na ce ta tambayeka. Amma ta ce zata kasancewa a gidan Hajja a kai amarya da ita.”

Abiy ya ce, “Su Yaya Ashiru da su Kawun Zaria suna tayi min waya ban san waye ya faɗa musu ba, na ce duk na hutar da ku hidimar biki bana buƙatar ayi komai amarya kawai nake so a kai.”

Jidda ido ta ya ciko da hawaye ta ce, “don Allah Abiy ka amince ko walima mu yi a goben.” Ya kalli Jidda ya ce, “lokaci ya ƙure, inda kin san kuna da wannan shirin da kin sanar dani da wuri, gobe har yaushe aka gama walima aka tafi Kano? Kin san bana son tafiya in dare ya yi.”

“To Abiy a ɗaga tafiya zuwa ranar Sunday.”
“Ke Jidda! Ya Isa, kar na sake jin wannan maganar a bakin ki kin gane?” Ya faɗa yana kallon ta a tsawace. Kai ta ɗaga tana goge hawaye. Ta kalli Nayla da har lokacin kanta yake a ƙasa kafin ta miƙe ta hau sama. Jidda ma bin bayanta tayi dan bata ga amfanin zama a falon ba.

Nayla kasa kukan ma tayi ta zauna akan stool ɗin madubi tayi shiru. Jidda ce ta shigo ta dafata ta ce, “Nayla ki yi haƙuri, wataƙila wannna auren alkhairi ne a gare ki da rayuwarki shiyasa yazo a haka.” Ta kalli Jidda da idanunta da suke a kumbure ta ce, “ta ya zai zama alkhairi bayan mahaifina baya son auren nan? Ta ya zai zama alkhairi bayan mahaifina yan fushi dani?.” Salma ta ce, “Allah bazai kama ki da laifi ba, tunda ke kin san baki yiwa Abiy komai ba.”
Chapter 46 · 0% Book details