Sashe 23
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai motsa ba balle ya yi magana wani wajan daban yake kallo ta sake cewa, "Ina sonka, Ina ƙaunar ka, Ina so na rayu da kai. Shikenan kuma sai laifin iyayena ya shafe ni Faruk? Daman laifin wani yana shafar wani ne Faruk?. Ban ƙi ka ba, nace a haka Ina sonka, na ce zan bika mu dawo nan a ɗaura mana aure koda iyayena basa so amma ka ƙi ji. Ya kake so nayi da raina ne Faruk? Na mutu kawai?."
Ƙaramin numfashi ya yi ya ɗago idanunsa da suka fara komawa jajaye ya kalle ta. Zunbur ta miƙe ta ƙarasa kusa dashi tana kallon idanunsa tana kuka ta ce, "kalli yadda na koma, kalli kaga yadda soyayyar ka ta kayar dani, ka tambayi Najwa ko bacci bana iya yi, ko abincin kirki bana iya ci kullum cikin tunanin ka da son ganin ka. Iyayena basu san na baro London ba, kai tsaye daga can Kano nazo saboda kai Faruk, saboda kai kawai na taho tun daga London dan na ganka. Wallahi in na rasa ka zan iya mutuwa" ta ƙarasa faɗa a sanyaye tana sake zubewa a wajan tana kuka.
Najwa ce tazo ta ɗaga ta a inda take zube, ta riƙeta a jikinta tana kuka ta kalle shi ta ce, "Yaya Narma tana sonka, a da bana goyan bayan auren ka da ita, amma yanzu Ina goyan baya sosai. Don Allah ka taimaki Yayata ko iya waya da ita ne ka dinga yi kafin komai ya daidaita a wajan iyayen mu. Na tabbatar maka da zasu soka zasu amince da auren ku nan kusa, don Allah ka yi haƙuri ka manta da komai kar Yayata ta rasa tunaninta a dalilin ka" ta faɗa tana kallon sa tana hawaye.
Hasbunallahu wani'imal wakil shine abinda yake furtawa kawai a zuciyarsa, zuciyarsa bugawa take rauni ya mamaye masa jikinsa gabaɗaya. Tausayin Narma na tasiri sosai a jikinsa amma ya kasa ce mata komai. To me zai ce mata bayan shi ya riga ya ajjiye shafin ta a rayuwarsa?. Hannunsa Narma ta riƙe ta ce, "baza ka ce komai ba?." Zame hannunsa ya yi daga riƙon da tayi masa, domin in ta riƙe shi kamar haɗuwar wuta da ruwa haka yake ji a jikinsa. Kallon ta ya yi ido cikin ido kafin ya sauke numfashi ya ce, "Narma!." Luuu tayi ta faɗa jikin Najwa ta riƙeta sosai tana kallonsa.
"Ki manta da abinda ya faru, ki manta da abinda ya wuce ki bi umarnin iyayenki. Babu abinda zan iya yi miki a yanzu, na yi iya abinda zan iya yanzu komai ya ƙare!."
Narma ta bishi da kallo ta ce, "kenan kana nufin na manta da kai?." Ya ɗaga mata kai ta ce, "bazan iya ba, wallahi bazan iya ba. Ni kaina da ace na san inda zan ajjiye soyayyarka da na ajjiye na hutawa zuciyata. To ban sani ba Faruk, ban sani ba!"ta ƙarasa faɗa da ƙarfi tana kallon sa.
A kausashe ya ce, "ya kamata ki sani Narma, ya kamata ki sani!. Komai ya ƙare, komai ya wuce, bazan yaudare ki da kalaman da na san bazan cika su ba, bazan faɗa miki abinda na san bazan yi ba. Shiyasa nake faɗa miki gaskiya, kije ki bi umarnin iyayenki, sannan ki tafi!."
Narma murya na rawa ta ce, "na tafi kace fa?." Ya ɗaga kai ya ce, "eh ki tafi, babu abinda zan iya yi miki a yanzu, ki tafi kawai."
"Na tafi ka ce?" Ta sake maimaita tana kallon sa. A birkice ya ce, "eh ki tafi! Ki je ki yi abinda iyayenki suke so ki ƙyale ni!."
Kuka take yi sosai mai sauti na kusan minti biyu bata ce komai ba, ɗaga kai tayi bayan ta goge idanunta tace, "Farul ka san mutane ƙalilan ne suke samun kusanci da zuciyar mace? For examples iyayenta da ƴan uwanta, tunda tana tare dasu tana samun soyayya da ƙauna daga gare su tun tana yarinya. Kaima haka naji a kanka, na ji a raina kamar na tashi tare da kai tun ina ƙaramar yarinya Faruk, ji take soyayyarka ta shiga jinina kamar na jima da sanin ka. Tun daga wannan lokacin naji kawai so nake nayi rayuwata a tare da kai, ko kaso ni ko kar ka soni har abada bazan daina sonka ba Faruk, ko ka so ko kaƙi zuciyata saboda kai kaɗai take bugawa. Har yanzu ina sonka Faruk!."
Ta sake goge idanu ta ce, "zan tafi Faruk, amma ka sani zan dawo ko ban dawo ba duk abinda ya same ni ka sani soyayyar ka ce sila. Bazan taɓa daina sonka ba har a tashi duniya" ta faɗa tana fita daga gidan a guje.[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P014
Arewabooks@nanahaleema11.
An kai amarya gidan ta mai kyau ana ta yabon kyaunsa saboda ko ina a gidan yayi kyau sai dai babu mutane sosai a kusa da ita amma kyau kam gida ya yi kyau. Jinkirin auren ta bai tashi a banza ba ya zame mata alkhairi domin kuwa da gidanta da lefen ta komai ma sha Allah.
Su Nayla gida suka dawo suna sauka a ƙofar gidan Hajja suka hangi Omar a zaune a ƙofar gidan Didi akan farar kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana kaɗawa. Nayla murmushi tayi ta ɗauke kai ta shiga gidan Hajja bata sake kallon sa ba.
Shi kuwa Omar kewa yake ji sosai a zuciyarsa, ya rasa abinda zai yi ya ji daɗi. Ya san Didi kuka zata yi in suka haɗu shiyasa ya gudu bai bari sun haɗa ba dan baya son ganin kukanta. Gidan yake son shiga amma in ya tuna bata nan sai yaji babu amfanin shigarsa gwara yayi ta zaman a ƙofar gidan in yana ganin mutane zai fi jin daɗi. Bai san ya damu da Didi ba sai yanzu, bai san haka Didi take da tasiri a gare shi ba sai yanzu, bai ɗauka zai yi kewarta har haka ba sai ya tabbatar da bata nan.
A kan idanunsa su Nayla suka shiga gidan Hajja ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da zama a wajan. Sai sha biyu na dare sannan ya iya miƙewa ya shiga gidan, kewarta ta damu zuciyarsa sosai, haka ya zubawa ido yana kallo kamar zai ganta ko ya ji muryarta, ga tausayin Narma zuciyarsa. Tabbas yana jin tausayin Narma amma babu abinda zai mata in ba ya nisanta kansa da ita ba shiyasa ya aikata abinda ya aikata. Da wannan tunanin ya kwanta yana tunanin Didi bacci ya ɗauke shi.
Washe gari.
Nayla haka ta tashi da nauyin jiki tayi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atampa mai kyau. Falo ta fito wajan Hajja ta zauna a kan kujera ta ce, "Hajja Baba Salisu ya taho yazo zamu wuce gida." Hajja ta bita da kallon tuhuma ta ce, "Hauwa me ya ke damunki ne haka?." Hajja ta kalli Salma da ta fito tana shan tea ta ce, "Salma me yake damun ƴar uwarki?."
Salma ta zauna ta miƙawa Nayla cup ɗin tea Nayla ta karɓa ta ce, "na gode." Salma ta kalli Hajja ta ce, "Hajja bana ce ba, ni ma dai haka nake ganinta. Kawai ki ta yi mata addu'a." Hajja ta ce, "Me ya ke damunta? In ba zaku faɗa ba zan kira babanta na tambaye shi. Ya ina tambayar ku kuma ce min babu komai? Ina ganin duk wani motsin ku fa, yadda ku ke yin komai a sanyaye na tabbatar akwai abinda yake damunta." Nayla ta ce, "Hajja babu komai ba wani abun bane, shima Abiy ɗin haka yake cewa kuma na faɗa masa babu komai."
"Mu in baki faɗa mana ba ai Salma da Jidda sun sani." Salma ta ce, "Hajiya ni ban san komai ba gaskiya sai dai ko Jidda" ta faɗa tana miƙewa ta bar wajan. Hajja tayi musu banza bata sake magana ba amma tayi kuɗurin tambayar Abiy abinda yake damun Nayla.
Lokacin da Baba Salisu yazo sai da ta kai masa abinci kamar ko yaushe, ta dawo daga kai masa abincin idanunta ya sauka akan masoyinta yana tsaye suna magana dasu Bashir suna nuna masa wasu kaya a leda. Ɗauke ido tayi tana takawa a sanyaye ta shiga gidan Hajja ba tare da ta sake kallon sa ba dan gabaɗaya hankalinsa baya kanta. Bata jima da shiga ba ta gama haɗa abinda tazo dashi ta kai mota, Baba yana gama cin abincin ya huta tayi musu sallama Salma ta rakata har bakin mota ta shiga suka tafi.
••••••
Amarya Didi ta wayi gari a gidan miji cikin aminci da kwanciyar hankali, ganin abun take kamar a mafarki wai itace tayi aure bayan shekarun da ta kwashe ba tare da auren ba. Tana girmama ikon Allah da kuma lokaci da mutane suke faɗa sai yazo komai zai faru. Tabbas ta amince da aure lokaci ne, duk yadda ka kai ga son yinsa in lokacin yin bai yi ba baza ka yi ba. Kamar mutuwa ce, duk yadda ka kai ga yin jinya in lokacin mutuwar bai ba babu inda zaka je, amma da zarar lokaci yayi kamar ƙiftawar ido anyi an gama. Ita kam taga tasirin haƙuri, taga tasirin miƙawa Allah lamarinta, taga tasirin ƙin sanya damuwar rashin aure a zuciyarta. Gashi fa lokacin yayi har ta wayi gari a gidan mijinta kamar almara.
Tana zaune a falon ta gabaɗaya kewar Omar ta cika mata zuciya, AbdulHamid ya shigo falon da sallama ta amsa ya ce, "Omar ɗin kike tunani ko?." Didi tayi dariya ta ce, "wallahi, ina ta tunanin ko ya ci abinci." Ya yi dariya ya ce, "banda abin ki Omar ai ba yaro bane ba" ya faɗa yana zama kusa da ita.