Sashe 19
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin driver Hajja ya saka aka buɗe musu gate na farko a nan suka ajjiye motar. Bayan ya faka Salma ta ce, "Mu je ciki" ta faɗa tana fitowa tana ɗan jijjiga hannunta dan ta gaji da zaman. Omar dai bai fito ba yana zaune Didi ta kalle shi ta ce, "ka fito mana." Ya kalle ta ya ce, "Sai na shiga gidan mutane babu izini? Ku je dai." Didi ta saki baki tana kallon sa ta ce, "ikon Allah! Sabon salo."
Salma tayi dariya ta ce, "Didi mu je zai shigo daga baya." Didi tabi bayan Salma suka sake shiga wani gate ɗin a nan wani mahaukacin parking space yake mai bala'in girma wanda aka tanadi rumfuna daga can gefe na ajjiye mota.
Didi kallon gidan take tana girmama girmansa da kuma ƙarfin kirki irin na Nayla. Wanda ya fito daga wannan gida ba kowa ne zai yi mutunci har ya kalli na ƙasa dashi ba. Ciki suke shiga Didi ta ga sai tafiya suke yi kafin a buɗe wata babbar ƙofa su shiga sai gasu a wani babban falo mai bala'in kyau.
Babu kowa a falon sai mai aiki tana kunna turaren wuta Salma ta kalle ta ta ce, "Ina Mama da Nayla?." Ta ce, "Mama tana ciki, Nayla kuma tana sama bata sakko ba gabaɗaya." Mama ce ta fito tana cewa, "waye yake nema na?." Ganin Salma sai tayi murmushi ta ce, "A'a Salma, ke ce tafe?." Salma tayi dariya ta ce, "Ni ce Mama." Zama suka yi har Didi suka gaisa da fara'a kamar ta san Didi kafin Salma ta ce, "Didi ce Mama, na san kina jin labarinta a bakin Nayla." Sai Mama ta sake yin dariya ta ce, "ƙwarai kuwa in jin labarin Didi maƙociyar Hajja ko?." Salma ta amsa ta ce, "itace. Ta zo wajan Abiy ne."
Mama ta ce, "ai kuwa yana falon sa kuma fita zai yi, maza jeki ki rakata dan na ji yana cewa cikin Zaria zai shiga, kuma ya kai yamma ko dare bai dawo ba." Salma ta miƙe tana cewa, "Nayla fa?." Mama ta ce, "tana sama yau ko sakkowa ma bata yi ba, bata jin daɗi shiyasa ko aiki bata je ba. Jeki zan tasota sai tazo ta same ki." Tare suka fita da Didi da Salma. A harabar gidan wani ɓangaren daban suka shiga, Salma ta buɗe ƙofar da ta san nan ne falon Abiy na waje.
Ai kuwa yana zaune shi kaɗai da alama ya gama cin abinci suka shiga falon da sallama, Jawad ne ya fito daga kitchen ɗin falon da ruwa a hannunsa ya ajjiyewa Abiy a gaban sa. Abiy ya amsa sallamar sai ya murmusa ya ce, "A'a Salma, ke ce tafe?." Salma ta ƙarasa ta zauna a kan carpet ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta Hajja da Daddy ta ce duk suna lafiya lau. Da Didi suka gaisa lokaci ɗaya ya gane ta, Salma ta ce, "Abiy Didi ce." Abiy ya ce, "Aisha dai, Ai na gane ta." Didi tayi murmushi tana sunkuyar da kai.
Salma ta ce, "ta ce na rakota wajan ka shiyasa muka taho yau. Tare mu ke da Omar ƙaninta ma yana waje a tsaye." Abiy ya ce, "yana waje a tsaye? Kun yi wannan doguwar tafiya a barshi a waje? Jawad jeka ku shigo tare." Jawad ya tashi ya fita ba jimawa suka dawo tare da Omar harda driver Hajja. Gaisawa suka yi da Drivern kafin ya tashi ya fita Omar ya gaishe da Abiy cikin yanayin sa na kadaran kadahan.
Abiy da murmushi yana kallon sa ya ce, "Lafiya lau Omar, ya hanya?."
"Alhamdu lillah" ya amsa a taƙaice dan jinsa yake a takure. Wani irin girma yake ji Abiy ya yi masa a jikinsa da zuciyarsa, shiyasa gabaɗaya ya kasa sakewa ya kuma kasa haɗa ido da Abiy.
Didi ta ce, "Abiy mun zo mu yi godiyar alkhairin da aka yi mana, Allah ya saka da alkhairi ya biya ka da aljanna. Babu abinda zamu saka maka dashi sai addu'a. Ga Omar ya dawo cikin alfarmarka, Allah ya sa a fi haka, Allah ya kare ka, Allah ya shirya maka zuri'arka, Allah ya ƙara maka lafiya da tsahon rai mai amfani." Abiy yana ta murmushi cikin jin daɗin addu'arta ya ce, "Amin ya rabbi. Tun daga Kano har Kaduna ku ka taho?."
Didi ta ce, "ai ya zama dole ne, dole mu zo mu yi godiya."
"Har gida kin je kin yi min godiya a lokacin, sai da ku ka sake ɗauko hanya ku ka zo?." Didi ta yi murmushi Abiy ya ce, "Babu komai ai yiwa kaine. Kuma kafin na taimaki Omar ai shi ya taimake ni, na rama alkhairi da alkhairi ne kawai."
Omar wani iri yake ji a jikinsa, ba saba yiwa mutane godiya ya yi ba balle ya san irin addu'ar da zai musu, duk sai ya rasa abinda zai ce yake jin bakin sa kamar an ɗaure tamau. Gashi yana ji a jikinsa ya kamata yayi magana amma ya rasa me zai ce. Zai yi magana kenan Nayla ta shigo falon ba tare da ta lura da Didi ko Omar ba, a shagwaɓe ta shigo ta san Abiy yana nan dan kawai Mama ta ce mata Abiy na kiranta bata san su waye a ba.
"Abiy" ta faɗa tana ƙarasowa inda yake. Ya kalle ta ya ce, "Mamana kin tashi? Tun ɗazu aka ce bacci ki ke yi, ya zazzaɓin?" Ya faɗa yana riƙo hannunta ya zaunar da ita kan kujera yana taɓa wuyanta. Abiy ya ce, "har yanzu jikinki da zafi. Mamana baki da lafiya gaskiya yana da kyau ki ga likita, gabaɗaya kin rame sai yawan ciwo a kai akai-akai. Zan yi magana da likitan da zaki gani ki je gobe ya duba ki a san abinda yake damunki. Jiya Maman ki ta ce min harda ciwon ƙirji ko?." Kai ta ɗaga alamun eh har lokacin idanunta a lumshe yake kafin ya ce, "Jawad gobe zai kai ki wajan likita, na lura kece bakya son zuwa."
"Hajiya Nayla" Salma ta furta tana kallon ta. Da sauri ta buɗe ido tana kallon mutanen da suke zaune a falon. Dam! Gabanta ya buga haɗa ido da suka yi da Omar da yake zaune daga gefe ya ɗago kenan suka haɗa ido. Wara idanu tayi ta kalli Abiy ta sake kallon su Salma ta ce, "Salma, Didi?." Didi tayi murmushi ta ce, "Na'am Nayla." Sai kuwa tayi ihu ta tashi a guje ta koma kusa da Didi ta ce, "Didi yaushe ku ka zo? Shine ba a faɗa min ba?. Wai ko mafarki nake yi ne?."
Didi ta ce, "ba mafarki ki ke yi ba Nayla, ni ce yau a Kaduna." Nayla ta ce, "ikon Allah. Kuma Mama bata faɗa min ba fa, ta ce min kawai Abiy yana nemana, ashe ku ne kuka zo. Sannu da zuwa."
"Yauwa Nayla, ya jikin na ki?."
"Da sauƙi" ta faɗa tana sauke da ido ƙasa farin ciki yana mamaye zuciya ta ganin masoyin ta a zaune a falon gidan su.
Abiy da yake kallon ta yana murmushi ya ce, "ki tashi ki je ki saka a haɗa musu breakfast sun yi tafiya mai nisa." Mama ce ta shigo falon da sallama ta ƙaraso ta zauna suka sake gaisawa da Didi shi dai Omar bai iya kallon ta ba sun gaisa kawai dan in akwai abinda ya tsana bai wuce gaisuwa ba.
Abiy ya kalli Mama ya ce, "wannan shine wanda ya taɓa taimakon Nayla a Kano shekarun baya....Kin tuna?." Mama ta ce, "Allah sarki na gane shi." Didi ta bawa Mama abinda ta taho musu dashi Abiy ya ce, "harda wahala? Ku da ku ka yi tafiya mai nisa har sai an yi tsaraba?." Didi murmushi ta ke yi ta ce, "Babu komai Abiy." Abiy ya ce, "mun gode sosai, Allah ya bar zumunci."
Didi ta amsa da amin tana murmushi, ta ji daɗin yadda Abiy ya karɓe su wallahi, ta kuma fuskanci gadon kirki Nayla tayi daga wajansa. Mama ta kalli Nayla da ta kwantar da kanta a kafaɗar Didi tana kallon Omar ta gefen idanu ta ce, "Nayla ki je ki saka a haɗa musu abinci su ci ko?." Nayla ta ɗago a sanyaye ta ce, "To Mama." Abiy ya ce, "Mamana jikin ne?." Ta girgiza kai ta ce, "A'a Abiy, murnar ganin Didi ce kawai."
"To maza ki je a haɗa musu abinci, sun yi doguwar tafiya."
Bata miƙe ba gani take in ta tafi bazata cigaba da kallon Omar ba, shi kam ko kallon inda take ma bai yi ba balle ya yi magana. Abiy ya ce, "amma dai sai gobe zaku koma?." Didi ta wara idanuta ce, "A'a, anjima kaɗan zamu koma in sha Allah." Abiy ya ce, "Toh, ai na ɗauka zaku kwana ku huta gajiya ai. Shikenan ni daga nan zance ya kiyaye hanya, zan shiga Zaria bazan dawo na zame ku ba gaskiya. Allah ya kiyaye hanya na gode da girmamawa." Omar ne ya buɗe baki kamar mai koyan magana ya ce, "Amin. Mun gode sosai, Allah ya ƙara girma."
Lumshe ido Nayla tayi jin kalaman Omaar idanunta suna cika da hawaye saboda tsantsar bugawar da zuciyarta take yi. Salma na lura da ita haka Mama duk motsin ta akan idanunta take yi. Abiy ya ce, "amin Omar, Na gode sosai. Mamana ki raka su falo su huta." Nayla ta amsa ta miƙe ta ce, "Didi ku zo mu je" ta faɗa a sanyaye. Didi ta miƙe Salma ma ta miƙe Abiy ya ce, "Omar ku je tare, Jawad raka shi zai fi sakewa." Jawad ya amsa yana miƙewa shima suka shiga ciki.