Sashe 42
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka Mama ta dinga lallaɓa Abiy da kalamai masu kwantar da hankali tare da kai suka ga abinda zai saka ya sake yin fushi da Nayla. A haka ta samu ya ɗan sauka ya ce ta bashi waje bacci zai yi ta fito daga ɗakin.
Nayla kuwa lokacin da ta fita daga ɗakin daƙyar ta iya ƙarasawa dakinta tana kuka mai tsuma zuciya. Ta jima tana wannan kukan babu mai rarrashinta, babu mai bata shawara, babu mai faɗa mata laifin da ta aikata. Tun tana kukan cikin daɗin rai har kanta yayi bala'in yin nauyi, zuciyarta kam kamar dutse haka take ji saboda nauyi. Lokaci ɗaya take ji kamar ana zare mata son Omaar ɗin daga zuciyarta, bata sani ba ko dan bata nutsuwar ta ne, amma gabaɗaya ya fita daga ranta cikin ƙaramin lokaci.
"Aure fa, aure fa da Omaar Abiy yayi min. To meye dalilin hakan? Me na aikata masa ya yanke wannan hukuncin a kaina?. Wa zan tambaya ya bani amsa?" Ta faɗa hawaye na ganganarowa daga idanunta.
Sautin buɗe ƙofa taji ta juya taga Mama ce ta shigo ta ƙaraso inda take ta miƙa mata kuɗin ta ce, "yace na tabbatar na baki sadakin auren ki, sannan ki bani number Yayar Omaar ɗin Ina so zan tambaye ta a gidan da zasu ajjiye ki. Na saka za a kawo kaya gobe ban sani ba ko zasu burge ki, kawai na zaɓa ne saboda babu lokaci."
Nayla ta bi kuɗin da kallo ta miƙe tsaye tana kallon Mama ta ce, "Mama me na yiwa Abiy ya yanke min wannan hukuncin?."
"Nayla nima ban sani ba, abinda na sani ya dawo jiya ya ce min ya aurar dake ga Omar. To me zan ce masa? Shine ya haife ki Ina da magana akan haka ne?."
Nayla ta ce, "Mama amma ke kika ce naje Kano ko? Meyasa baki faɗawa Abiy ke kika tura ni ba?."
"Na tura ki Kano dan a samu mafita ki auri wanda kike so ne ba dan ran mahaifinki ya ɓaci ba, abinda na lura ba zuwan ki Kano ne ya ɓata masa rai ba, akwai wani abun a ƙasa da ya saka ransa ya ɓaci." Nayla ta dafe kai ta koma da baya ta zauna ta ce, "me na yiwa Abiy haka? Bai taɓa fushi dani kamar yau ba, me na aikata masa ni Hauwa?" Ta faɗa cikin rawar jiki dan zazzaɓi ne yake neman kamata.
Mama ta ɗauki wayar Nayla ta buɗe ta nemo number Didi ta ɗauka a tata wayar sannan ta ajjiye mata wayar kana ya ce, "to wai meye na wannan koke-koken? Naga burinki ne na son auren Omar ya tabbata ko? To meye na kukan ke da ya kamata ace kina farin ciki?."
"Mama Abiy fushi yake yi dani, kuma ni ba ta wannan hanyar nake son samun farin cikin ba. Meye abin farin ciki bayan mahaifina ransa yana "ɓace? Meye abin farin ciki bayan kowa haushina yake ji?. Ban san me na aikata ba, ban san me nayi ba!."
"Aikin gama ai ya riga ya gama Nayla, yanzu ke matar Omar ɗan daba ce, akwai igiyoyin aurensa guda uku chas akan ki. Dan haka kawai ki yi tawakalli ki karɓi ƙaddara komai zai warware."
Wani haushin Mama taji a zuciyarta abinda bata taɓa ji a zuciyarta ba, ta kawar da kai gefe Mama ta fita daga ɗakin ita kuma ta cigaba da aikin tunani. Ko Twiny da Salma ta kasa faɗawa, gani take wannan ba abinda za a faɗa bane gwara kawai taja bakin ta tayi shiru.
Washe gari Ranar Sunday da safe Mama ta siyi kaya aka kawo aka dinga shigo da kwalaye na gado da kujeru. Nayla na sama ta kasa fitowa saboda zazzaɓi da ya rufeta ga azabar ciwon da kanta yake yi. Jalila ce ta shiga ɗakin ganin yadda take ya saka ta fito da sauri ta samu Abiy da Yaya Jawad a tsaye fitowar Abiy ɗin kenan ta ce, "Abiy Anty Nayla bata da lafiya." Abiy ya nufi ɗakin shida Jawad, ganin yadda Nayla take rawar jiki Abiy ya matsa kusa da ita ya taɓa goshin ta yaji yadda yayi zafi sosai.
Jawad ya kalla ya ce, "kira Dr yazo ya duba ta, ka faɗa masa zazaabi ne da ciwon kai kuma kuka ne ya kawo shi. Sai ya san da abinda zai zo." Jawad ya amsa yana kallon Nayla nan take sai ta bashi tausayi, yaji tausayinta ya maamaye masa zuciya. A kasalance ya ɗauki waya ya kira Dr aka yi sa'a yana kusa ya ce gashi nan zuwa. Suna zaune a ɗakin har Yaya ya shigo da Jalila da Mama, Dr yayi waya ya ce gashi yazo Jawad yaje ya shigo dashi.
Ƙarasowa ya yi suka gaisa da mutanen ɗakim kafin ya taɓa jikin Nayla. Jin zafin sai da ya tsorata shima, ya haɗa allura yayi mata ganin yadda take ta juya kai alamun ciwon kan yake mata sai ya saka mata har da ruwa. Kallon Abiy yayi ya ce, "in ta farka taci abinci ta sha wannan maganin, in sha Allah zata dawo daidai." Abiy ya karɓi maganin yayi masa godiya ya fita.
Nayla ta kalli Abiy da yake kallonta cikin jajayen idanunta ta ce, "Abiy kayi haƙuri, kayi haƙuri Abiy. Na fasa aurensa, na amince ka aura min wanda kake so."
Tausayi ta bawa Abiy amma har lokacin bai yi dana sanin abinda yayi mata ba, dan shi kaɗai ya san abinda ta turo masa da kalaman da ta furta akan Omar, auren shine daidai ko a wajan Allah bashi da laifi. Jawad ya ƙaraso ya riƙe hannunta ya ce, "ki nutsu ki samu bacci, ki daina magana."
Cikin rauni ta ce, "Yaya J Abiy fushi yake dani, ban san me nayi masa ba. Ka bashi haƙuri kar na mutu yana fushi dani, kuma ku yi hakuri,
Yaya ka yi haƙuri" ta faɗa tana kallonsa da yake tsaye. Shi kansa ta bashi tausayi sosai ya daure ya ce, "ki daina magana kinji Nayla, ki yi bacci." A hankali idanunta ya fara rufewa hannunta na cikin na Jawad har tayi bacci.
Tare suka fito falon gabaɗaya suka samu Mama tana waya Abiy ya wuce ta su kuma suka tsaya suna so ta gama wayar. Tana yanke wayar Jawad ya ce, "Mama wai wanne kaya ne haka ake ta shigowa dasu?."
"Kayan auren Nayla mana, baka ji mai mahaifinku ya ce ba?." Jawad ya ce, "Amma Mama sai na ga kamar murna ma kike yi da auren nan. Gabaɗaya hankalinki yana kan siyan kaya gata can a kwance babu lafiya." Mama ta ce, "umarnin mahaifinku na ke cikawa, shi ya ce na tabbatar yau an siyi komai dole na mayar da hankali." Yaya ya ce, "Amma ko shi Abiy a yanzu bazai saurare maganar kaya ba, don Allah ki bar maganar nan ki bari ta samu lafiya tukunna."
Mama bata ce komai ba ta wuce ɗaki ta nemo number Didi da ta ɗauka a wayar Nayla ta kira. Bata jima tana ringing ba aka ɗauki wayar, da sallama Mama ta amsa ta ce, "Ina magana da Aisha ne?." Didi ta ce, "itace."
"Nice Maman Nayla, daaga nan Kaduna."
"Lah Mama, barka da safiya" ta sake jaddada gaisuwarta saboda girmamawa. Mama ta sake amsawa kafin ta ce, "Mahaifin Nayla ya saka na kiraki, yace na tambaye a ina za a ajjiye kayan Nayla na aure?." Sai da gaban Didi ya faɗi, ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Wallahi Mama bana ce ba, ni gabaɗaya a rikice nake da wannan lamari na rasa abinda zanyi."
Mama ta ce, "mu ma nan duk a haka muke, amma ya zama dole na tambaya saboda ya saka a siyi kayan ɗaki. Ya ce da a yau ma zata taho Kano, to saboda rashin kayan ne zai saka a ɗaga." Didi ta ce, "To Mama zan tambaya naji."
"Yauwa ki tamabaya, ki faɗa min adadin ɗakukanan, in ɗaya ne to, in biyu ne ma dai duk daya. Bana so ya sake tambayata nace ban yi ba."
"In sha Allah Mama zaki ji ni."
"Yauwa na gode" ta faɗa tana yanke wayar. Sai kuma tayi dariya ta ce, "to kayan ɗakin ma suka wuce ɗaki daya ko biyu? Ina yake da wajan da za a ajjiye kaya na alfarma? Me ya ke dashi me ya tara?. Tunda dai an ɗaura auren ni burina ya gama cika wallahi" ta faɗa tana ajjiye wayar tare da shiga toilet.
••••
Didi lokacin da ta yanke wayar ajiyar zuciya tayi mai ƙarfi cikin rashin sanin abinda zata yi. AbdulHamid da yake bayanta ya ce, "Lafiya dai?." Didi ta kalle shi ta ce, "Maman Nayla ce." Ya kalle ta cikin rashin fahimta ya ce, "wacece Nayla?."
"Yarinyar da aka aurawa Omar ita mana."
"To meye ya faru?."
"Tana magana akan gidan da za a ajjiye Nayla, dan suna siyan kayan ɗaki ne. Ni wallahi ban san me zance, ban san me zan aikata ba gabaɗaya kaina ya gama kullewa" ta faɗa tana zama akan kujera tare da dafe kai. Ya ce, "da Omar ɗin ya kamata ki fara magana, ko kuma ki san gidan da zata zauna ɗin ki faɗa musu dan su naga da gaske suke yi."
Didi ta ce, "Na faɗa maka akwai gidan a ƙasa, amma babban tashin hankalina Omar wallahi. Tijarar da zai yi akan auren nan shine bana so, ran kowa sai ya ɓaci wallahi, ya ɓata nasa ran ya ɓata na mutane." AbdulHamid ya ce, "to ya za ayi? Haka Allah ya ƙaddara aurensa
haka zai zo. Ni kuma sai nake ganin kamar zai karɓi auren."
Didi ta kalle shi tana girgiza kai ta ce, "baka san waye Omar ba ne shiyasa kake faɗar haka. Tun asali haushin Nayla yake yi, saboda itace mace ta farko da na taɓa yi masa faɗa a gabanta. Yayi mata tsawa, ya harareta, ya razanata duk akan na taɓa yi masa faɗa tana wajan. Babu kalma mai kyau da ta taɓa haɗa su, kullum a cikin jin haushinta yake. Kwatsam sai naje masa da labarin itace matarsa? Kana ganin zai amince cikin sauƙi?."