← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 52

Sashe 7

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki, Allah ya sa tayi nasarar zuwa, Allah yasa su dawo tare."
"Amin. Ke ni bana so ma ya fito wallahi, haka kawai yake bani haushi." Nayla sai taji ranta ya ɓaci sosai da kalaman Salma akan Omar, ta harare ta tare da yin tsaki ta ce, "Sai ki ta ji ai, bani da lokacinki" ta faɗa tana datse kiran tana jin zuciyar ta bugawa sosai. Tabbas ya kamata tayi wani abun akan Omar.

A haka ta gama shiri ta fito zuwa falo ta tarar Abiy ma bai fita ba. Ganin sa a falo sai suka gaisa ya ke cewa, "ya zaki yi da bikin yayarki Shayida ta Kano?." Nayla ta ce, "Zan je."
"Aikin fa?." Nayla ta kalli Abiy jin abinda ya ce sai ta ce, "Abiy ai na lokaci ɗaya ne, zan ɗauki excuse ." Abiy ya ce, "har yaushe kika fara aikin da zaki fara ɗaukar excuse? fara ɗaukar excuse ya yi wuri Mamana."

"To Abiy haka za ayi bikin Yaya Shayida babu ni?" Ta faɗa tana hawaye daman a wuya take, kukan take son yi. Abiy ganin tana kuka aya yi tsaki ya ce, "to meye abin kukan? Kwana biyu kin zama shagwaɓaɓɓiya, da anyi magana sai kuka."

Ta share ido dan a zahiri ne kawai take kukan son zuwa bikin Shayida Kano, amma a baɗini Omar ne a zuciyarta. Abiy ya ce, "akwai abinda zai kai ni Kano ni zan riga su Maman ku yin gaba, babarki ma ta ce ranar laraba zata tafi, in sun tafi ranar laraba ɗin ai Jawad yana nan, sai ku zauna tare in ya so ranar Friday sai ki tafi kema."

Nayla ji tayi kamar an sakata aljanna saboda farin ciki, ta kasa ɓoyewa ta ce, "To Abiy Allah ya kaimu, na gode sosai."
"To maza tafi aiki." Hanyar fita tayi tana murna ya ce, "kin yi breakfast?." Nayla ta ce, "nayi takeaway sai naje can."
"Okay, Allah ya kiyaye" ta amsa da amin ta fita tana murya. Ko babu komai zata je Kano, duk da dai Omar ɗin baya nan amma zata je ko gidan su ne ta kalla ta ji daɗi, kuma tayi alƙawarin zata yi duk yadda zata yi wajan ganin Omar ya dawo.

Fan's Waye zai ci wasan ne? Nayla ce ko kuma Narma?. Waye zai yi silar dawowar Omar? Nayla ce ko kuma Narma ko kuma Didi ce?.
[20/09, 8:30 am] +234 906 075 3382: KRB2P004
Arewabooks@nanahaleema11

Su Didi sun isa Abuja sha biyu na rana, Bashir yana yiwa driver Hajja kwatancen estate ɗin da zasu shiga wancan lokacin. Suna zuwa gate na estate ɗin suka ganshi a kulle ga manyan jami'an tsaro a wajan da alama ba a shiga. Didi ta kalli Bashir ta ce, "ba a shiga ne?." Bashir ya ce, "Gaskiya mu ma saboda Damisa ne a lokacin mu ka shiga, amma yanzu ban san ta ya zamu shiga ba." Tk ya ce, "muje muyi magana dasu mana."

Didi ta ce, "A'a karku je su yi mu ku wani abun fa." Tk ya ce, "kar ki damu babbar Yaya, Bash mu je" suka faɗa suna fita zuwa wajan su. Sun jima suna magana kafin su dawo su kalli Didi Bashir ya ce, "sun ce ba a shiga dole sai da izini." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "kawai dai munyi wahalar banza za su ce." Kallon gidan da aka nuna mata na Sen ta ke yi don shine na biyu layin, jinjina girma da kyaun da take yi a zuciyarta.

Didi ta ce, "Bashir ku shigo mu san abinda zamu yi, gashi mu ba wani muka sani a garin nan ba balle mu je mu huta." Driver Hajja ya ce, "Akwai gidan da Hajja ta ce na kai ku ku huta a can, ku zo mu je in yaso in anjima sai mu sake dawowa nan ɗin." Shiga motar suka yi ya bar unguwar dasu zuwa gidan da Hajja ta ce su je.

Gida ne babba mai apartment guda biyar, ya faka motar ya fito suka shiga ciki yana cewa, "Gidan Hajja ne da take bayarwa haya, ɗaya daga cikin gidajen da mahaifiyar Nayla ta rasu ta bari Hajja ta gada, shine take karɓar kuɗin haya. Wannan ɓangaren babu kowa ta ce na kawo ku nan a huta in yaso gobe sai mu koma Kano."

Didi murmushi take yi a bayyane ta ce, "Allah ya sakawa Hajja da alkhairi, ya biya ta da aljanna. In ba ita ba waye zai yi min haka?." Suka amsa da amin suna shiga ciki. Ƙofar farko ya nunawa Bashir da Tk ya ce, "ga ɗaki a nan sai mu zauna a ciki, ita sai ta shiga ciki." Da to suka amsa suka shiga ciki itama ta shiga.

Falon harda kujeru sai dai ya ɗan yi ƙura, bata damu ba ta zauna sai ga wuta haske gauwaye ina. Sayyadi ne ya shigo da sallama ya shigo ya kunna mata a.c sannan ya kalle ta ya ce, "yanzu za a kawo abinci." Ita dai Didi murmushi take kawai cikin jin daɗi. Ƙaunar Hajja da iyalanta take ji a zuciyarta, girma da darajar na sake mamaye mata zuciya. A nan suka ci abinci suka ɗan huta, ita dai tana kwance ne kawai amma burinta kawai ta ga Sen ta nemi alfarma ko zai amince.

Sai dare sannan suka koma wajan suka tarar an canja masu tsaron wajan ba na ɗazu bane, suka sake yi musu magana amma basu bada dama ba Didi ta ja ta tsaya a wajan ta ce babu inda zata je sai ta ga Senator. Sun hana su tsayawa a wajan gate ɗin, sai can baya suka koma kamar almajirai.

Motar Sen ce take fitowa daga gidan ba tare da jiniya ko jami'an tsaro ba, ya hangi su Didi a tsaye tunda a baya yake zaune amma bai san su waye ba, suka wuce su dan ya ɗauka almajirai ne. Bashir ya kalle ta ya ce, "shine ya wuce a cikin motar nan." Didi ta ce, "mu jira dawowarsa to."

Haka suka ta zaman jiransa sama da awa uku sannan motar ta dawo ta sake wuce su ta tsaya a wajan masu gadin wajan Sen ya sauke glass daga baya da yake zaune ya ce, "su waye waɗancan can a tsaye? Meyasa ku ke barin mutane a tsaye a bakin gate ɗin nan?." Ɗaya daga ciki ya ce, "Sorry Sir! Sir kai suke nema, tun da rana suka zo. Na gansu a lokacin da nazo wajan Jibson."
"Ni suke nema kuma? Ina sadaka ne a gidana?."
"Haka dai suka ce kai suke nema." Sen ya juya ya kalli bayan sa ya hango Didi a tsaye tana kallon motar.

Kallon su ya yi ya ce, "kira ɗaya daga cikin su." Cikin ɗaga murya ya yafito Tk, da hanzari Tk ya ƙaraso Sen ya kalle shi ya ce, "su waye ku?." Tk ya ce, "mu ƴan uwan Damisa ne, mun zo muna son ganin ka, tare da yayar sa muke." Sen ya ce, "waye haka?." Da mamaki Tk yake kallon sa amma sai ya ce, "Tiger na Kano."

Wani irin kallo Sen ya yi masa na baku da hankali ya ce, "gani na ɗin me ku ka zo yi?." Zai yi magana ya kalli masu tsoron wajan ya ce, "a tabbatar duk bar wajan nan yanzun nan, in na leƙo naga ɗaya a cikin su ranku ne zai ɓaci" yana faɗa ya ɗaga glass ɗin motar aka ja motar zuwa ciki.

Nan da nan aka fara yi musu tsawa su bar wajan babu shiri suka bar wajan zuwa inda suka ajjiye motar. Jingina Didi tayi da motar ta rufe ido kawai bata ce komai ba. Kallon gidan ta sake yi ta yi ajiyar zuciya cikin damuwa mai yawa. Ga gidan tana kallo amma babu yadda zata yi, bata da damar shiga balle ta yi magana da Senator ko zai taimaka mata.

Senator da ɓacin rai ya fita daga motar ya shiga ciki, a sama ya samu Mum a zaune ya kalle ta ya ce, "kin san su waye a wajan estate ɗin nan?." Mum ta ce, "su waye?."
"Wai ƴan uwan Tiger ne suka zo son ganina." Mum ta ce, "ƴan uwansa? Kenan daman da sanin su yazo nan neman aure?."

Dad ya ce, "bara na yi waya gabaɗaya a kama su." Mum ta ce, "A'a Dear, kar ka saka a kama su."
"Meyasa?" Ya tambaya yana kallon ta. Mum ta ce, "ka shigo dasu, ka shigo dasu mu yi musu warning, sannan mu saka su je su karya asiri da Tiger ya yiwa ƴarmu." Dad ya kalle ta da mamaki ya ce, "hakan ya yi?."
"Hakan ya yi mana, ki shigo dasu muyi amfani dasu a karya asirin da ya yi mata. Babbar dama muka samu da zamu tura su gida su je su karya asirin ko dan hankalin Narma ya dawo jikinta."Waya Dad ya ɗauka ya kira masu gadin ya yi musu magana yana kashewa.

Su Didi suna tsaye aka ƙaraso inda suke, su sun ɗauka ma laifi suka yi. Bashir ya ce, "ya dai? Nan ma korar mu za a yi ne? Na ga nan kan titi ne ko?." Kallon su ya yi ya ce, "ku ku zauna a nan, ke mu je Sen yana kiran ki." Bashir ya kalli Didi da ta zabura zata bisu ya ce, "Didi bai kamata ki je ke kaɗai ba." Didi ta ce, "kar ku damu, bara naje na dawo." Tare suka tafi zuwa gidan aka raka ta har bakin falon gidan sannan ya dawo wanda ya rakata.

Da sallama Didi ta shiga amma bata ga kowa ba, falon shiru sai sanyi da ƙhamshi da yake tashi a cikin sa. Didi bata tsaya ƙare masa kallo ba dan ba abinda tazo yi ba kenan. Tana tsaye a falon aka turo aka shiga da ita ciki, a wani falon ta same su a zaune su biyu suna kallon mai shigowa. A sanyaye Didi take shiga, ganin su kawai ya sanyaya mata jiki,
ba kamar kallon wulaƙancin da suke binta dashi duk sai ta sare guiwar ta tayi sanyi sosai.
Chapter 7 · 0% Book details