← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 52

Sashe 14

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Didi ta ce, "tafiyar ta tashi?."
"Wallahi Abiy yace na zo zamu tafi."
"Na so kun haɗu da Omar kafin ki tafi gashi bai dawo ba har yanzu. Amma zamu zo Kaduna tare dashi mu sake yiwa Abiy godiya sha Allah." Nayla ta yi murmushi ya ce, "Allah ya kawo ku. Salma zo mu je" tare suka fito Didi tana ta yi mata godiya har sai da Nayla ya nuna bata so sannan ta daina suka shiga gidan Hajja. A harabar gidan Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma don Allah ki zauna da Didi in ya dawo ki yi min video ki tura min kin ji?."

Yadda tayi maganar sai ta bawa Salma tausayi a sanyaye ta ce, "in sha Allah zan yi miki, kar ki damu."
"Na gode ƴar uwa." Daga haka suka shiga wajan Hajja tayi mata sallama a gaggaucs saboda kiran Abiy da yake shigowa wayarta. Ta ɗauki motar da ta zo da ita ta bar unguwar zuciyarta duk babu daɗin rashin ganin masoyinta.
[22/09, 6:58 am] +234 906 075 3382: KRB2P008
Arewabooks@nanahaleema11.

Didi da Salma tun suna zaman jiran dawowa Omar har suka gaji da zama suka koma gidan Hajja. A can suke zaune har akayi sallar magriba babu alamun Omar. Didi a lokacin ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, "wataƙila bai amince ya sake shi ba ne, wataƙila kuma Omar ɗin ne ya yi taurin kai ko ya faɗi wata magana mara daɗi." Hajja ta ce, "ki ta addu'a zai dawo, tunda Abdullahi ya ce zai dawo na tabbatar zai dawo kar ki damu."

"Assalamu alaikum!" aka faɗa a ciki ba tare da sallamar ta fito sosai ba tare da shigowa cikin falon. Gabaɗaya suka juya ga wanda ya shigo suna kallon sa.

Didi wara idanu tayi ganin Oamar ɗinta a tsaye yana kallonta, sai ta zabura ta miƙe ta ƙarasa inda yake ta riƙe hannunsa ta ce, "Omar kai ne?." Kai ya ɗaga mata ya ce, "eh Didi, ni ne." Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Alhamdu lillah! Allah na gode maka, Allah na gode maka da ka dawo min da Omar cikin ƙoshin lafiya."

Duk ta ruɗe tana addu'a kamar wacce bata cikin hankalinta, ganin hakan sai ya dafa kafaɗarta muryarsa a shaƙe ya ce, "Didi ki nutsu mana." Didi ta ce, "na kasa nutsuwa Omar, na kasa. Farin cikin dawowarka ba zai bar ni na nutsuwa ba." Sai a sannan ya kalli Hajja da take kallonsa ya ce, "Ina yini."

Hajja ta ce, "daga nan? Baza ka shigo ka zauna ba?." Didi ta riƙo hannunsa zuwa cikin falon ya tako daƙyar dan baya jin daɗi gabaɗaya. Zama ya yi Hajja ta kalle shi ta ce, "Barka Omar, Ina fatan komai lafiya ko?." Kai ya ɗaga kawai bai ce komai ba dan maganar ma wahala take masa, ya kalli Didi da take kuka ya ce, "meye na kukan kuma Didi? Ba dai gani na dawo ba? In kina kuka bazan ji daɗi ba."

Saurin goge ido tayi ta ce, "na daina Omar, farin cikin ganin ka ne ya saka haka nake kuka amma na daina." Hajja ta yi murmushi tana kallon sa, abinda ya bata mamaki tsaf dashi baza ka ce ya fito daga wahala ba. Duk da ya rame sosai fuskar sa ta ɗan yi duhu amma shigarsa da yanayinsa gabaɗaya bai nuna haka ba. Yadda ta ce gashin fuskarsa ya taru yanzu duk an rage sai wanda ya saba bari abin ya bawa Hajja mamaki.

Didi ta kalle shi ta ce, "Ka yiwa Hajja godiya, ta silar Hajja da Nayla ka dawo gida yau. Mahaifin Nayla shine ya saka aka dawo da kai gida." Hajja ta katse ta ta ce, "Aisha ki bar shi ya huta tukunna, yana buƙatar hutu sosai. Ku je gida ya huta maganar ta biyo baya." Kamar jira yake ya miƙe dan daman bai so shigowa ba, kawai dan Bashir ya ce masa tana ciki ne ya saka shi ya shiga. Hajja ya kalla ya ce, "Sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya Omar" ta faɗa da murmushi tana kallon sa.

Fita ya yi Didi ta dawo kusa da Hajja ta ce, "na gode Hajja, na gode Allah ya biya ki da aljanna. Duk ta dalilinki Omar ya fito, ta dalilinki ne Hajja. Allah ya sa aljanna ce makomarki." Hajja da Salma suka amsa da amin Hajja ta ce, "kar ki damu Aisha ai a riga an zama ɗaya, kallon jikata nake yi miki kamar Nayla da su Salma, Kar ki damu ki kwantar da hankalinki. Ki shiga kitchen ki ɗauki abinci a nan ki kai masa ya ci ya huta, in zai je ganin likita ma aje a duba shi ya dawo hankalinsa kamar da."

Didi ta ce, "to Hajja. Amma na so Nayla tana nan ya dawo, ban san dame zan sakawa Nayla abinda tayi min ba Hajja." Hajja tayi murmushi ta ce, "kin san bashi da uwa sai ke Aisha, ki tashi ki je ki bashi abinci ya huta sai mu yi magan." Da to ta amsa ta tashi taje ta ɗauki abinci a kitchen ɗin Hajja, ta ɗauki hijjabi da wayarta ta fita daga gidan cikin farin ciki.

Hajja tayi murmushi bayan ta fita ta ce, "Allah sarki Hauwa'u sarki tausayi, sai da ta san yadda tayi mahaifinta ya fito da Omaar. Allah ya biyata." Salma ta amsa da amin tana kallon video da ta yi a zuwan Omar tana tunanin ta tura mata ko ta share ta kawai. Kiran Nayla ne ya saka shigowa wayarta, daga tafiyarta zuwa yanzu sau goma sha bakwai kenan tana kiranta, Salma
tayi tsaki ta miƙe ta shiga ɗaki.

Didi da ta fita a tsaye a ƙofar gidan ta ga Omar shida mutane sa, da hanzari ta ƙarasa ta buɗe gidan ta manta a rufe gidan ya ke. Sai da ta ɗan jima da shiga sannan ya shigo falon tana kallon sa har ya ƙaraso. Ta ce, "ƙanina ga abinci kazo ka ci sai ka kwanta ka huta ko?." Omar ya zauna ya ce, "na ƙoshi Didi, na ci abinci magani kawai zan sha na kwanta."
"Sannu" ta furta a sanyaye tana kallon sa. Kawai ya ɗaga kawai bai ce komai ba.

Didi ta ce, "na ganka tsaf ba kamar lokacin da naje na same ka ba." Omar ya ce, "ban shigo cikin gari ba sai da na tabbatar na dawo nutsuwata. Da aka bani wayata sai na kira su Bash suka same ni a wajan gari, har asibiti mun je a ƙara min ruwa an kuma bani magani. Wannan dalilin ne ya saka na jima ban shigo ba sai yanzu." Didi ta ce, "gwara da ka yi hakan ko dan saboda ƴan gulma. Amma ka rame sosai Omar, kuma ka yi duhu." Bai ce komai ba ta sake kallon sa ta ce, "to ka sha maganin kafin kwanta sai ka fi jin daɗin bacci."

Kallon ta ya yi da kulawa ya ce, "kema kin rame Didi, baki da lafiya ne?."
"Lafiya lau nake Omaar, rashin ka ne kawai ya kawo hakan." Ɗan murmushi ya yi ya ce, "Sai ka ce in ina na nan ɗin ba faɗa muke yi ba." Didi ta yi ƴar dariya ta ce, "Ko doke-doke muke yi ƙarewar faɗa ba." Murmushi ya sake yi ya ce, "Kar ki damu yanzu na dawo ai."

Kafin ta yi magana ya ce, "an ce a gidan Hajja ki ke kwana ko?."
"Eh Omar, hana ni kwana anan tayi ta ce na koma gidan ta saboda mutane." Kai ya girgiza da yayi masa nauyi bai sake magana ba. Dauriya kawai yake yi yana magana saboda ita, amma kansa ciwo yake yi sosai.

Miƙewa ya yi sai ya yi kamar zai fadi ta zabura ta miƙe tana kallonsa, Omar ganin yadda ta zabura sai ya dake ya ce, "kar ki damu ba wani abun bane, kaina ne yake ciwo kaɗan." Har ɗaki sai da ta raka shi ta tabbatar yana cikin ƙoshin lafiya sannan ta fito ta shiga nata ɗakin tana tunanin dame ya kamata ta sakawa Nayla alkhairin da tayi mata?.

Washe gari.

Ya ji sauƙin jikinsa babu laifi ya daure bai kwanta ba saboda kar hankalin Didi ya tashi, hakan ya saka shi ya fito ya samu tana ta aikace-aikace kamar kullum. Tana ganinsa ta dakata ta ce, "ka fito? Ya jikin na ka?." Ɗan lumshe ido ya yi ya buɗe, da zai iya faɗa mata gaskiya da ya ce mata babu sauƙi dan ciwon kan bai rabu dashi ba, ga jikinsa gabaɗaya babu ƙarfi, ga ciwo da duk gaɓoɓin jikinsa suke masa. Amma da yake baya so ya sakata a damuwa sai ya ce, "na ji sauƙi. Kawai bana jin ƙarfi ne sosai."

Didi ta ce, "Sannu. Zauna na kawo maka shayi ka sha zaka ji daɗi." Zaman ya yi kamar yadda ta ce ta kawo masa shayi ya karɓa tana yi mata sannu. Zama tayi a nesa dashi tana kallon sa ta ce, "sannu Omar." Kai ya ɗan ɗaga kaɗan yana shan shayin a hankali ba dan yana jin daɗinsa ba sai dan saboda ita ɗin.

Shiru ya ratsa tsakani, tayi shiru shima ya yi shiru yana shan tea a hankali yana kallon wani wajan daban. Didi ta ce, "in ka warware ina so zamu je Kaduna gidan mahaifin Nayla mu yi masa godiya. Shi ne ya yi magana da Sen ya rabu da kai Omar, ƴarsa Nayla ce taje tana kuka ta ce don Allah ya yi wani abun ka fito." Omar ya kalle ta ya ce, "to" ya amsa a taƙaice dan baya son doguwar magana.

Ido ta ga ya lumshe ya ajjiye kofin hannunsa ta bishi da kallo kafin ta miƙe ta ƙyale shi a wajan tana cigaba da aikin da take yi.

••••••
*England, london.*

Tunda Narma da Najwa suka sauka a ƙasar England Najwa ta kasa gane kan Yayarta, domin kuwa ta koma wata iri babu walwala babu dariya babu zaman hira. Ko yaushe tana cikin ɗaki ta rufe kai ko tana kuka ko tana tunani. Gabaɗaya zaman bai yiwa Najwa daɗi ba saboda ba haka suka saba zaman ba, sun saba su ne yaje su je nan su je can, amma yanzu gabaɗaya ta canja.
Chapter 14 · 0% Book details