← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 52

Sashe 28

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiss yayi mata a wuyanta hakan ya saka ta kalle shi suka haɗa ido ya ce, “Haba my love kina wahalar dani, kin san Ina sonki fa, please daina wahalar dani.” Hannunta ta saka ta cire hannunsa gaga cikinta ta ce, “I need rest, please leave!” ta faɗa a sanyaye tana ƙoƙarin barin wajan. Riƙo hannunta yayi ya dawo da ita baya yazo daf da ita yana kallon idanunta ya ce, “i don’t want to leave your side, ina sonki sosai Narma. Allow me to show you how much you mean to me” ya faɗa tana riƙe wuyanta yana shafawa a hankali har gashin kanta.

“Kai ka ce zaka iya zama dani a ko wanne irin yanayin ko? To bani buƙatar your love or time and whatever, ka ƙyale ni a haka, haka nake son zama bana son takura” ta faɗa tana janye jikinta ta fita ta bar masa ɗakin. Girgiza kai yake yi cikin ɓacin rai ya ce, “No Narma baki isa ba, baki isa ki dinga saka ni a damuwa da yanayi mara daɗi ba. I feel your desire a strongly, and i want to satisfy, tun kafin na aure ki nake jin son kasancewa dake a zuciyata. Yanzu matata ce ke baki isa ki yi min iyaka da jikinki ba” ya faɗa shi kaɗai yana shiga toilet. Koma meye sai dai ya faru bazai sake barin ta haka yana kallon ta kamar wacce ya dasa yana jiran ta girma ba.

Narma falo ta koma ta ɗora ƙafa kan ɗaya tana kaɗawa cikin tunani. Yanzu in ta kira Omar sau dubu bata shiga ma balle ta same shi, ta gwada WhatsApp duk a banza. Gashi iya WhatsApp ta san yana yi bata sani ba ko yana da wani handle a social media platform. Ajiyar zuciya tayi ta ɗauki wayarta tana duba hoton da ta yi masa tana murmushi cikin soyayya.

Karɓar wayar taji an yi suka haɗa ido ta ga ya ɗaure fuska ta sauke kai ya ce, “Narma bazan juri wannan shirmen naki ba fa, da aurena a kanki ki dinga kallon hoton wani banza?.” Narma ta kalle shi ta ce, “kar ka sake ce masa banza, ai na faɗa maka daman bana sonka kace ka shirya aurena, to gani ga ka ai.”

A fusace ya yo kanta ya ce, “na rantse da Allah bazan juri wannan shirmen naki ba, na juri iya abinda zan iya yanzu bazan jure ba. Mijinki ne ni dole ki yi abinda nake so.” Narma kallon sa take yi kafin ta ce, “ni bani da wani miji in ba Faruk ba, don haka ka daina wahalar da kanka baza ka taɓa samu na a matsayin matar ka ba.” Ya ɗaga idanunsa ya kalle ta ya ce, “au haka ne? Zan tabbatar miki da ni ne mijin ki ba shi ba, kuma zan nuna miki nike da iko dake bashi ba, kuma har abada bazaki aure shi ba.” Wuce shi ta yi zuwa ɗaki dan lokacin sallar azahar ya yi.

Sai da ta idar da sallah ta cire abayar da ta ɗora akan rigarta ajjiye ta zauna akan gadon tana tunani. Asharaf ya shigo ɗakin yana binta da shu’umin kallo, a yadda yake jinsa wannan lokacin ko cikin Mum zata koma bazai iya ƙyaleta ba. Ya gwada damarsa tana dakatar dashi, a wannan lokacin bazai dakatu ba sai ya tabbatar da abinda yake so ya samu.

A hankali yake takowa zuwa inda take, zai zauna sai kuwa tayi zumbur ta miƙe ya riƙo hannunta shima ya miƙe ya jawo ta baya. Juyowa tayi zata yi magana ya hana ta ta hanyar haɗe bakinsa da nata. Kiciniyar ƙwacewa take yi amma ta kasa ya riƙe ta sosai haka bai hana ta daina ƙoƙarin ƙwantar kanta ba amma ya hanata. Ganin ta dage ƙarfi zata gwada masa sai ya ya saka hannunsa a bayanta ya sake haɗe ta da jikinsa yadda bazata samu damar motsi ba.

Gently yake kissing ɗinta cikin ƙaramin lokaci ya kashe mata jiki, ƙoƙarin ƙwantar kanta da take yi sai ta daina jikinta ya yi sanyi tayi luf a jikinsa. Ganin ya fara samun kanta sai ya fara yawo da hannunsa a jikinta bayan ya sauke hannun rigar ƙasa. Ganin da gaske ya samu abinda yake so sai ya murmusa dan wutar sha’awarta sake kunnuwa tayi a zuciyarsa, da azama ya ɗauketa ya ajjiye a kan gadon yana kashe hasken ɗakin ta hanyar saka hannun a gefen gadon.

••••••

A cikin kwanakin da suka gabata Omar sun fara aikin sarrafa takalma na maza da na mata, takalma suke yi masu kyau suna kaiwa kasuwa. Cikin ikon Allah sun fara sana’ar da sunan Allah, domin kuwa batch ɗin farko na takalma guda ɗari suka yi amma sai da ya ƙare tas ya zamana ana nema suka sake yin guda ɗari biyu shima ya ƙare ana nema. Sosai hakan ya faranta ran Omaar yana kuma hango nasara wacce tafi haka a gaba.

Yana zaune a falon Didi na gidan su shida Bashir da Tk yana sake bada sabon design ɗin da suke gani ya kamata ayi. Bashir ya ce, “Boss ya kamata ace mun sakawa company nan namu suna, bamu san inda zai je ba nan gaba.” Omaar ya kalle shi ya ce, “Zamu yi wannan tunanin daga baya, yanzu dai a je ayi wannan. Duk kun iya aikin ma kuwa?.” Bashir ya ce, “ni dai ina gwadawa, Tk dai ya iya sosai.”
“Yanzu meye a ƙasa?.”
“Anyi guda ɗari uku yanzu, an raba su a kasuwa.”
“Dakyau, zan shigo zuwa anjima duk abinda za a yi sai a yi.” Suka amsa suna tashi suna fita.

Gaisawa yaji suna yi da mace a cikin gidan sai abin ya bashi mamaki, dan tunda Didi ta bar gidan babu macen da ta sake shigowa, suma mazan sai su Bashir kawai bayan su babu wani baƙo da yake zuwa. Didi ce ta shigo falon hakan ya saka ya ce, “Nayi mamaki da naji ana gaisawa da mace a gidan nan, har nace wacce mai neman a raunanata ce ta shigo gidan nan.”

Didi tayi dariya ta ce, “Omar kana nan da halin ka, Ban da abin ka wacce mace ce zata shigo gidan maza?.”
“Mai rabon wahala mana” ya faɗa yana kallonta da murmushi a fuskarsa. Zama tayi ya bita da kallo yana hango canjin da ya gani a tare da ita ya ce, “Amarya da kanta, Kin yi haske amma kin rame kaɗan. Shi mijin naki baya baki abinci ne?.” Didi tayi dariya tana mamakin yadda akayi ya fahimci tayi haske ta kuma rame, lallai Omar yana kula da lamarinta sosai, in ba haka ba babu ta yadda za a yi ya fahimta lokaci ɗaya.

Ta ce, “Kai ba sai ka bani abincin ba.” Ya murmusa kaɗan ya ce, “Allah kin rame, Ina fatan lafiya?.”
“Lafiya lau wallahi, bani da damuwar komai Omar. Jinkirin aurena ya zamar alkhairi a rayuwata, haƙiƙa in ka yi haƙuri ka barwa Allah komai ka kuma riƙe mutuncin ka wallahi Allah bazai wulaƙanta ka ba. Na ga hakan a kaina Omar, Ina kukan farin ciki ina godewa Allah da ya jinkirta min zuwa wannan lokaci.” Omar ya ɗan taɓe baki ya ce, “Yayi. Amma baki amsa min tambayata ba, kin rame, babu damuwa ko?.”

Didi tayi dariya ta ce, “na amsa mana Omar, babu komai kawai na ɗanyi rashin lafiya ne daga shekara jiya zuwa yau.” Ya ɗaga kai bai ce komai ba ta bishi da kallo ta ce, “kaima ka rame ai, kuma ka ɗan yi duhu kaɗan. Lafiya ka ke?.” Sai ya langwaɓar da kai kamar ƙaramin yaro cikin shagwaɓa ya ce, “to bani da uwa, bani da Yaya, bani da mai kula dani, ba dole nayi duhu na rame ba?.” Sai taji babu daɗi a zuciyarta ta ce, “Baka girki?.” Ya kalle ta ya ce, “Didi ba fa zaman banza nake yi yanzu ba, in na fita tun safe wani lokacin har dare Ina can ana aiki. Yaran basu gama iya aikin ba ni ne nake yi da kaina, har yaushe na dawo na ce zan yi girki?.”

Sai ya bawa Didi tausayi ta ce, “Ayya haka ne kuma. Ka yi haƙuri kaji ƙanina, yau nazo zan maka girki ka ci har sai ka barshi.”
“Gobe fa?” Ya tamabaya yana kallonta. Ajiyar zuciya tayi ta kalle shi ta ce, “To ka yi aure mana Omar, yanzu kana da sana’a kuma ka rage rashin ji zaka iya riƙe mata ai ko?.” Kallon ta yayi na wani lokaci kafin ya yanje ido ya ce, “ba yanzu ba.”
“Sai yaushe? Ko kana jiran Narma ne?.”
“Wace haka?” Ya tambaya yana kallon wani wajan daban.

Harararsa tayi ta ce. “Ban sani ba.” Sai ya yi shiru bai bata amsa ba. Didi ta sake cewa, “ya kamata ka fara neman aure zuwa yanzu, kaga watan ramadan zamu shiga zaka sha wahala, ga azumi, ga aiki, ga kuma girki. Mu ba ƴan uwa a kusa ba balle mu ce zaka dinga karɓa a wajansa.” Hararata yayi ya ce, “kawai sai na karɓi abinci a gidan wani ɗan uwa, haka akwai dan mutuwar zuciya?. Ba halina bane, ko a gidanki bazan karɓa ba balle wani.”

Didi ta yi murmushi kaɗan ta ce, “yanzu dai me zaka ci yau?.” Ya marairaice fuska yana lumshe idanu cikin jin daɗin ganinta ya ce, “kema kin sani ai Didi.”
“An gama.”
“Me kika fito yi ne?.”
“Ganin ka mana, tunda kai baka je inda nake ba ai ni nazo inda kake. Kullum cikin tunanin ka nake, sai da na fito nazo na samu nutsuwa.” Omar ya shafa kansa yana murmushi cike da ƙaunarta ya ce, “naso nazo kuma fa, zan zo dai ba yanzu ba.” Bata ce komai ba tayi murmushi kawai.

Kallon ta ya kuma yi fuskarsa a sake kamar zai yi magana sai ya fasa. Ta ɗaga kai ta ce, “Faɗi abinda yake bakin ka.”
Yayi ƴar dariya ya ce, “a dai yi shiru kawai, amma naji daɗin ganinki.” Murmushi ta kuma yi ta ce, “na shiga wajan Hajja ta ce min kwana biyu bata ganin ka, shine nace Omaar kai kuwa baka shiga ku gaisa?.”
Chapter 28 · 0% Book details