Sashe 17
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kulle ido ya yi ya buɗe cikin mutuwar jiki amma ya dake bai nunwa Didi ba ya kalle ta ya ce, "babu wanda ya san abinda Allah ya ɓoye kam, amma bana tunanin aure ta gaskiya. Ke kin san in na wuce bana dawowa."
"Daman bai kamata ka yi wannan tunanin ba duba da abinda ya faru, amma in Allah ya rubuta ƙaddara babu wanda ya isa ya canja ta." Ajiyar zuciya ya yi ya kalle ta ya ce, "shagon aikin takalmi nake so zan buɗd" ya faɗa dan kawar da zancen Narma kar ta saka jikinsa ya yi sanyi saboda tausayinta.
Didi a sanyaye ta ce, "Da gaske?."
"Da gaske nake, Ina tattara kuɗin ne saboda hidimar aurenki da kuma buɗe shagon. Amma a yanzu haka fitar da nayi akwai wani machine na aikin takalmin dana bayar za a siyo mana shi daga lagos. Bana so abin ya ɗauki lokaci ne da wuri nake so a fara in sha Allah." Didi tayi murmushi ta ce, "Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah ya sa albarka a neman da za a fara."
"Amin."
"Amma Omar ba da kuɗin ƴan siyasar nan zaka gina halak ɗinka ba ko?." Ya kalle ta ya ce, "ban gane ba."
Didi ta ce, "Ina magana akan kuɗin da irin su Senator suke baku dan a zubar da jini a wajan zaɓe ko a tayar da hayaniya, ba dasu zaka fara sana'ar ba ko?." Ya zuba mata ido yana kallon ta kana ya ce, "Didi daman an taɓa biyana na kashe wani ne ko na zubar masa da jini?." Ganin yadda ya kafe ta da ido yana kallo sai ta ji daɗi a ranta, hakan da ya yi ya bata tabbacin ba irin kuɗin da take tunani bane, kallon da yake mata kuma na rashin jin daɗin maganar ta ne.
Didi ta ce, "Ni ban ce an taɓa baka ba, kawai ina nusar da kai da ka gina halak ɗin ka da tsarkakan kuɗi, kar ka gina halak da kuɗin haram babu abinda zaka ɗauka a ciki." Ya ce, "ki daina yi min wannan tunanin bana jin daɗi, na san abinda nake yi. Ba a taɓa bani kuɗi dan na cutar da wani na karɓa ba, ko shi Senator ki je ki tambaye shi ban taɓa karɓar aikin tayar da hayaniya bama balle kisan kai. Tunda na wuce lokacin da nake ji da iskancina ban yi kisa ba bana tunanin akwai wata halitta da zata iya biyana dan na kashe rai. Ki daina min irin haka ban so."
Didi ta yi murmushi ta ce, "To Allah ya baka haƙuri."
"Da haƙurin ya mutu sadakar nawa ki ka bayar?" Ya faɗa yana harararta alamun ya ji haushi. Didi ta yi dariya ta ce, "Tunda dai na bada haƙuri ai sai ya wuce ba sai an faɗa min magana ba."
Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Ya kamata a fara siyayyar kayan aurenki ko?."
"Eh haka ne, lokaci yana ta zuwa kamar wasa. Zan sanar da kai abubuwa da ya kamata." Kai ya ɗaga kawai bai ce komai ba yana kallon wani wajan daban. Tashi ya yi ya fita ita kuma a gaggauce ta gama abinda zata yi ta fita zuwa gidan Hajja.
Hajja tana ganinta ta fara murmushi ta ce, "Aisha ke ce tafe?."
"Hajja ni ce, Ina tare da labari mai daɗi da nake so na faɗa miki." Hajja ta ce, "Ina jinki."
"Hajja Omar dai ya fara nutsuwa, Omar ne jiya yake yi min zancen na faɗa masa duk abinda yake yi mara kyau zai daina. Na faɗa masa ya kuma ce in sha Allah na ɗauka ya daina ɗin. Yanzu da ya dawo maganar yana so ya buɗe shago na aikin takalmi yake min, har ya bada kudin siyan injin aikin takalmi."
Hajja tayi murmushi ta ce, "Alhamdu lillah! Wannan labari ne mai daɗin gaske Aysha. Fahimtar kuskure sa da ya yi har yake so ya gyara babbar riba ce a rayuwarsa. Kin ga abinda nake faɗa miki ko? Na kan ce miki Omar daƙyar in ba mace ce zata yi silar nutsuwarsa ba, sai gashi ta dalilin mace abubuwa zasu canja."
Didi ta ce, "kuma na fahimci a gidan su Narma ne aka faɗa masa maganar da yake ji a zuciyarsa zai canja, ya ɗan faɗa min wasu daga ciki kaɗan amma bai faɗa min duka ba, na kuma lura maganar tana damunsa a zuciyarsa."
Hajja ta ce, "kiran rabo da kiran canjin ƙaddararsa ne ya saka shi amsawa Narma. Kar ki yi mamaki in aka ce Allah ya shigo da Narma rayuwarsa ne kawai dan ya je gidan su a faɗa masa maganar da zata farkar dashi daga dogon baccin da yake yi, kar yi mamaki in aka ce Allah ya yi haka ne kawai saboda Omaar ya nutsu ya zama mutum kamar kowa. Wataƙila amfanin Narma kenan a rayuwarsa, ta shigo rayuwarsa ta zama silar da ya je inda aka faɗa masa abinda ya saka yake ji a zuciyarsa zai canja, ya amsa kiran rabonsa ta dalilinta, wataƙila ta fita kenan bazata sake dawowa ba har abada. Wataƙila kuma zata dawo nan gaba ta kasance matsayin matarsa. Ikon Allah ai girma gare shi, sai abu ya faru zaka tabbatar da in Allah ya yi nufin shiriya a lokaci ɗaya komai zai faru ayi a gama. Kai dai ka kasance cikin addu'a ko yaushe, duk ƙanƙantar addu'a bata faɗuwa a ƙasa wallahi."
Didi tana murmushi ta ce, "haka ne wallahi Hajja, Omar ya amsa kiran rabonsa ta silar Narma." Hajja ta ce, "wataƙila matarsa tana gefe zata shigo rayuwarsa ta wata fuskar, wataƙila kuma Narma ɗin ce matarsa, duk abinda iyayenta zasu yi sai dai su yi su gama amma sai ta aure shi. Allah ai ba abin wasa ba ne ba, in Allah ya rubuta babu wanda ya isa ya canja, In kuwa kaga ya canja to daman haka abin yake a cikin ƙaddararsa." Didi ta ce, "Wallahi Hajja na yi farin ciki, daɗi nake ji sosai zuciyata wallahi."
Hajja ta dafata ta ce, "zaki fi kowa jin daɗin canjin Omar a yanzu, ke kaɗai ce uwa, uba, yaya, ƙawa, ƙanwa a gare shi. Allah ya baki lada Aisha, ya jiƙan iyayen ku, ya ɗorar da zumunci da ƙaunar da ku ke yiwa junan ku har aljanna."
"Amin Hajja. Amma yarinyar nan Narma tana bani tausayi, yanzu ta kira ni tana kuka kina ji kin san ba ƙaramin so take yiwa Omaar ba. Abin har mamaki yake bani, ta rasa wanda zata yiwa wannan soyayyar mai zafi sai Omar, dole iyayenta su ce asiri ya yi mata."
Hajja ta yi dariya kaɗan ta ce, "ita Narma ƙaddararta kenan soyayyar Omar, in Allah ya rubuta matarsa ce kamar yadda na faɗa miki iyayenta basu isa su hana ba, duk matsayin da take dashi zasu manta su bashi aurenta. In kuma ba matarsa bace Allah zai sassauta mata abinda take ji tayi aure ta huta. Babu mamaki a cikin ikon Allah Aisha, bayan Narma sai ki ga Allah ya sake kawo wata da zata sake haukacewa akan soyayyarsa. Komai yana da sila, hatta mutuwa tana da sila, shi Omar silar soyayyar da Narma take masa ne ya saka ya amsa mata har yaje gidan su, ashe zuwa gidan na su shine silar canjawasa."
Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya sa mu dace, Allah ya tabbatar dashi akan tafarkin halak."
"Amin Aisha." Didi ta kalli Salma da take ta murmushi ta ce, "Salma zaki raka mu Kaduna jibi in sha Allah, zamu je mu yiwa Abiy godiya har cikin gida." Salma ta ce, "gidan su Nayla?" Ta faɗa tana wara idanu. Didi ta ce, "can zamu je, amma kar ki faɗa mata Ina so mu bata mamaki. Ki dai san yadda zaki yi ki tabbatar da Abiy yana nan zamu je a ranar mu dawo."
Salma ta yi dariya ta ce, "in sha Allah. Allah ya kaimu." Ta amsa da amin Hajja ta ce, "Allah ya kaimu."
"Amin Hajja. Me ki ka san yana so da zamu siya daga nan mu kai masa?." Hajja ya ce, "kar ki takura kan ki Aisha, iya zuwan da zaki yi ya wadatar." Didi ta ce, "A'a Hajja, ai ya wuce na je gidan haka babu tsarabar Kano. Me zan tafi dashi?."
Salma ta ce, "yana son gurasar Kano, musamman ta gidan gurasa na nan baya, zaki iya yi masa ita kaɗai ta isa. Dan indai Nayla tazo Hajja tana bayarwa a kai masa. Didi ta ce, "na gode Salma, zan saka a yi sabuwa wacce zamu karɓa da safe sai mu tafi." Hajja ta ce, "Allah ya kaimu, sai ku je Sayyadi ya kai ku." Didi ta ce, "To Hajja, na gode Allah ya ƙara girma." Suka amsa da amin kafin ta ce, "Hajja sai magana ta gaba."
Hajja ta ce, "ina jinki." Didi ta ce, "magana ce akan kayan ɗaki da za a siya, Baba Adamu ya kira ni ya tabbatar min da shi ne zai yi komai na aurena, hatta cokali baya so na siya shi ne zai siya da kansa. Kawai abinda yake so na bashi makullin gidan zai zuba duk abinda ya kamata ace an zuba."
Hajja da fara'a ta ce, "kai amma ya kyauta, Allah ya bar zumunci." Didi ta ce, "amin Hajja. Babbar matsalar itace Omar, in yaji Baba Adamu ne zai yi komai wallahi bazai bari ba, in kuwa ya haƙura ya bari to sai raina na dana Baba Adamu ya ɓaci. Yanzun nan kafin na fito maganar kayan yake min sai na ce masa zamu yi magana, na rasa ta yadda zan faɗa masa saƙon Baba Adamu shima kuma Baban baya so Omar ya sani saboda tijarar Omaar. Ya dinga faɗa kenan yana cewa an faɗa musu bashi da kuɗin da zai yi min komai ne, kai lefe ma da nace an kai gidan kawu ya yi min shiru ne amma zai nuna min yaji haushi nan gaba."