Sashe 24
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Didi ta ce, "baka san halin Omaar bane, baya son cin abinci sai ance masa gashi, ko ance gashi ɗin sai yaga dama. Bara ba kira shi" ta faɗa tana ɗaukar wayata kira shi. Ɗauka taji anyi ta ce, "Assalamu alaikum." Daga can ɓangaren Omar ya ce, "Wa'alaiki Salam, Hajiya Didi amarya."
"Alhaji Omar ƙanin amarya." Dariya Omar ya yi ya ce, "ya naji maganar ki a dashe? me ya same ki?."
"Babu komai, mura ce kawai." Omar ya ce, "Kin sha ruwan sanyi kenan, shi bai san in kika sha ruwa mai sanyi kina tari ba ya bari ki ka sha?."
AbdulHamid da yake surarensa ya yi murmushi amma bai ce komai ba. Didi ma murmushin tayi ta ce, "jiya shine ka gudu ko?." Omar ya ce, "ni ai bana guduwa, kawai na ɓuya ne saboda ban son damuwa." Didi ta ce, "Haɗuwa dani ɗin ne damuwa?."
"Kukan da zaki yi min shine damuwa, a haka ma kin barni da tunani inaga kin saka ni gaba da kuka?." Didi tayi dariya ta ce, "To yaushe zaka zo?."
"Zan zo, Zan zo ko dan na yiwa mijin ki huɗuba ya san wacce yake aure, akwai gaɓar da zan tabbatar masa da Yayar Damisa yake aure." Didi da AbdulHamid suka yi dariya gabaɗaya AbdulHamid ya ce, "To Alhaji Omar ina nan jiran ka, Allah ya kawo ka."
Murmushi shima ya yi Didi ta ce, "ka ci abinci? Har sha biyu na rana tayi, Allah ya sa ka karya." Omar ya ce, "ban ci ba, ban jima da tashi ba. Yanzu dai nake tunanin abinda zan ci."
"Ka tashi ka yi girki mana, akwai abinci a kitchen da gas da komai ka dafa ka ci don Allah."
"To Didi zan ci."
"Ka kuma shiga gidan Hajja kayi mata godiyar abubuwan da suka faru."
"Didi nifa bana son godiyar nan kin sani."
"Ta zamar maka dole ne Omar, ta zama dole kaje kayi mata godiya." Ɗan tsaki ya yi ya ce, "to zan je."
Didi ta ce, "zan kira ka in anjima naji in kaje." Da to ya amsa a taƙaice ya kashe wayar ta kalli AbdulHamid tana murmushi. Shima murmushin yayi ya ce, "Kina ji da Oamar kamar yadda yake ji dake." Didi ta ce, "to mu kaɗai Allah ya bawaa iyayen mu, kuma iyayen na mu su ma babu."
"Gaskiya ne. Allah ya ƙara muku zumunci." Ta amsa da amin tana murmushi yana ta tsokanarta da sunan amarya ita kuma tana murmushi cikin jin nauyi.
Bayan Kwana biyu.
*Abuja.*
Najwa tausayin Narma take yi sosai, gashi ana ta batun ɗaura aurenta a ranar kuma bata sani ba. Duk tayi wani iri kamar ba ita ba kana kallon ta kasan tana tattare da damuwa mai yawa. Najwa ta fita wajan mahaifinsu ta zauna ta ce, "Dad don Allah kar a ɗaura auren nan, ku ƙyaleta taji da abinda yake damunta mana don Allah. In kuka aura mata Ashraf yanzu ba shi take so ba, ku ƙyaleta taji da damuwarta."
Mum ta kalle ta cikin harara ta ce, "kin fi mu sanin abinda ya kamata ne?." Najwa ta ce, "A'a Mum, Amma ina guje mana danasani a nan gaba." Dad jikinsa ya yi sanyi, maganar Najwa gaskiya ce amma bashi da zaɓi ko mafitar da ta wuce wannan, kuma dole ita zai bi dan samar mata da lafiya da kwanciyar hankali ta kuma manta da batun Omaar gabaɗaya a rayuwarta.
Dad ya ce, "Najwa ki bar zancen nan, aure za ayi shi yau in Allah ya kaimu. Sannan bance ki faɗa mata ba." Najwa ta tashi ta bar wajan cikin tausayin Narma sosai.
Narma tana zaune tana shan tea a falon sama tayi wanka ta saka ƙananun kaya riga da wando, wando iyakarsa guiwa sai riga mai baya a buɗe. Najwa wajanta ta dawo ta zauna bata ce mata komai ba itama bata ce ba tea kawai take sha a hankali.
Sun jima a haka kafin suji ana hayowa sama ba tare da ta kalli wajan ba ya dai jin motsin mutane. Muryar Dad ta ji yana cewa, "gata nan ma a zaune." Kallon wajan tayi sai ta ga gwamna Katsina ne da Ashraf da kuma minister sai Dad da Mum da Nabil. Bata yi ƙoƙarin miƙewa tsaye ba Dad ya karaso ya zauna kusa da ita mahaifin Ashraf shima ya zauna ya ce, "Daughter ya jikin na ki?."
Murmushi tayi ta ce, "Da sauki Daddy. Ina yini."
"Lafiya lau. Ina fatan babu abinda yake damun ki?."
"Babu komai Dady" ta faɗa tana ɗauke kai daga wajan.
Ya ce, "ma sha Allah, Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin tana ji suna maganar da ita ba ganewa take yi ba kafin duk su sauka ya rage daga Dad sai Mum sai ita a wajan. Dad ya kalle ta ya ce, "Narma yanayin damuwa da tashin hankalin da kike ciki, yau ciwo gobe lafiya shiyasa muka yanke hukunci a kanki." Da sauri ta kalli Dad ta ce, "ka yarda da Omaar?." Mum ta yi tsaki ta ce, "waye wani Omaar? Daughter ki nutsu mana, ki daina zancen wannan banza."
Shiru tayi bata ce komai ba. Dad ya ce, "Ashraf shine saurayinki wanda zaki aura a baya, kina sonsa shima kuma yana sonki. Wannan dalili ya saka yau ɗin nan mun ɗaura auren ku ke dashi, zaku tafi America ku je ku huta in kika nutsu sai a dawo ayi biki gabaɗaya." Kofin da take shan tea ne ya suɓuce daga hannunta ta kalli Dad murya na rawa ta ce, "au....re...Dad?."
"Yeah Aure, an ɗaura miki aure keda Ashraf yanzu. Kuma gobe in anjima zaku tafi america ku huta daga baya sai ku dawo."
Narma kallon mahaifin nata take yi ba tare da ta iya cewa komai ba, muryarta rawa take yi haka jikinta ma rawa yake yi cikin tsananin tashin hankali. An aura mata wani ba Omaar ba? Kenan yanzu bata da hope ɗin aurensa ake so ace ko me?. Ganin yadda jiki ta yake rawa ya saka Mum ta riƙeta calmly ta ce, "Calm down my daughter! Kar ki damu Ashraf yana sonki kuma zai kula dake yadda ya kamata. Mun yi haka ne saboda ki dawo nutsuwarki bama so mu dinga ganin ki cikin damuwa."
Murya na rawa ta ce, "Mum in dai bakwa sona cikin damuwa meyasa baza ku aura min Faruk ba? Meyasa baza ku amince na aure shi ba?. Bana son Ashraf, Faruk nake so dashi nake so nayi rayuwar aure ba Ashraf ba, don Allah ku ce wasa ku ke yi min ba ku yi min aure dashi ba, please Dad you're just kidding me right?" ta faɗa tana haɗe tafukan hannayenta waje daya alamun roƙo.
Mum ta ce, "Zaki manta dashi a hankali, asirin da yayi miki zai bar jikinki saboda tasirin auren da aka yi miki. Kar ki damu ki nutsu."
Narma kuka take yi sosai zuciyarta nayi mata zafi, shikenan an rabata da Oamar ɗinta kenan? Shikenan yanzu bata da damar aurensa tunda gashi an aura mata wani ba shi ba. Tuna hakan ne yake sakawa ta ƙara ƙarfin kukanta cike da ƙunar zuciya. Rarrashinta suka dinga yi amma taƙi ta daina sai kawai Dad ya kira Ashraf ya ce ya hayo saman, yana shigowa saman ya samu tana wannan kukan duk sai jikinsa ya yi sanyi.
Dad ya kalle shi ya ce, "ka rarrasheta" abinda ya ce kenan suka bar musu wajan shi da Mum. Ashraf a hankali ya taka zuwa inda take ya ɗagota daga kan kujerar ya haɗata da jikinsa ya rungumeta tsamtsam yana shafa fatar bayanta a hankali kasancewar rigar bayanta a buɗe yake. A kunne yake raɗa mata yana cewa, "Shiii! relax my wife, i'm here for you, stop craying."
Kuka take yi sosai a jikinsa shi kuma ya matse ta ya hanata koda motsin kirki sai kukan da take yi. "Ki bar kuka my wife Ina tare dake a ko yaushe, bana so ki dinga zubar da hawayenki. Ina sonki zan zauna dake a ko wanne yanayi ki ke, don't be nervous about this early marriage. I'll take care of you, i promise i'll always be there for you and make you happy. I love you so much my love, I love you! I love you! you're my heart, you're my life, you're my world. Stop crying, please..." a kunne yake raɗa mata cikin salo mai ɗaukar hankali da son rarrashi yana sake hura mata iska a cikin kunnenta tare da sake matse ta a jikinsa.
Narma duk tana jinsa amma bata daina zubar hawaye ba, imagination take yi wannan kalaman da yake faɗa mata ace Faruk ɗin tane yake faɗa mata da bata san farin cikin da zata yi ba, hango kanta take a rungume a jikinsa ya matse ta yana faɗa mata wannan kalaman. Nan take tsigar jikinta tashi ta runtse ido zuciyarta na bala'in bugawa har shi Ashraf yana jin bugun zuciyar a jikinsa.
Ido a kulle tana daga jikinsa ta ce, "I love him, I love Faruk. Dashi nake so nayi rayuwa, shi nake so na aura. Bana son zama da kai, dashi nake so na zauna......!" ta furta cikin wata irin murya mai nuni da raunin da yake tare da ita. Maimakon ya ji haushin kalamanta sai ya zaunar da ita akan kujera ya zauna a gefenta ya riƙe hannunta ya ce, "ina jin irin abinda ki ke ji, komai zai wuce na tabbatar da kina sona soyayyata zata dawo a cikin zuciyarki. Ina so kawai ki nutsu ki bani dama zan saka ki manta dashi a cikin rayuwarki gabaɗaya."
"Bazan taɓa mantawa dashi ba, shi nake so ba kai ba, shi nake so na aura ba kai ba, dan haka ka ƙyale ni" ta faɗa tana miƙewa da sauri ta shiga ɗaki tare da kulle ƙofa ta saka key. Bai yi ƙoƙarin binta ba sai ma murmushi da yake yi, tunda dai an aura masa ita koma me zata yi daga baya ne.