Sashe 22
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun dawo daga asibitin suna zaune wajan Abiy Jawad yana yi masa bayanin abinda likitan yace. Jawad ya ce, "Zancen gaskiya Abiy likita ya ce tana tare da damuwa sosai. Dalilin damuwar shi ne yake haifar mata da zazzaɓi da kuma ciwon ƙirjin da ta ce tana yi. Na tambayeta abinda yake damunta amma ta ce babu komai, na tambayeta ko akwai wani mai takura mata a wajan aiki ko barazana nan ma ta ce babu komai."
Abiy ya kalli Nayla da take zaune a gefen sa a tausashe ya ce, "Mamana me yake damunki?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ce, "Abiy babu komai."
"Ƙarya ki ke yi, likita ai bazai miki ƙarya ba sannan yanayinki ya gwada kina tare da damuwa mai tarin yawa. Me ya ke damunki? Ki faɗa min ko meye zan miki maganinsa." Nayla ta yi ajiyar zuciya tayi shiru bata ce komai ba.
Abiy a tausashe ya ce, "ban kai na ji damuwarki bane?." Ta girgiza kai alamun A'a ya ce, "ni mahaifinki ne, Jawad yayan ki ne, Maman ku kuma babarki ce. Babu abinda zaki ɓoye mana na rayuwarki saboda mu ne ahlinki, ki faɗa min abinda yake damunki nayi miki alƙawarin zan yi miki maganin ko meye."
Nayla ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba. Ganin haka sai Mama ta ce, "Abiy ka bar ni da ita zamu yi magana." Abiy ya kalli Mama ta ɗaga masa kai ta ce, "zan yi magana da ita, zata faɗa min in sha Allah. Nayla tashi ki je ki shirya, ko ba zaki je Kano bikin Didi ba?."
Nayla a sanyaye ta ce, "Zan je Mama."
Mama ta ce, "to tashi ki je ki shirya." A sanyaye ta tashi ta fita. Mama ta kalli Abiy ta ce, "kar ka damu, ka bari ta je Kano ta dawo zan tambayeta a nutse na tabbatar zata faɗa min. Sai ta kasa faɗa maka damuwarta amma ni ta faɗa min, na san ta yadda zan bi da ita har naji abinda yake zuciyarta."
Abiy ya ce, "meyasa zaki ce ta ce ta tafi Kano bayan yanayin da take cikin na rashin lafiya?." Mama ta ce, "zuwa Kano zai ɗebe mata kewa sosai, ko babu komai zasu haɗu da Jidda da Salma." Ambatar Jidda da tayi sai wani abu ya shiga zuciyar Abiy amma bai nuna ba ya ce, "shikenan ai, Allah ya dawo da ita lafiya. Ki tambayeta har batun samarinta."
Mama ta ce, "in sha Allah." Bata sake cewa komai ba shima haka, amma a zuciyarta tana ji lokacin da take jira ne yake gab da zuwa, da wannan damar zata yi amfani wajan cika burinta a akan Nayla.
[22/09, 3:27 pm] +234 906 075 3382: KRB2P013
ArewaBooks@nanahaleema11
Bayan sallar juma'a Nayla suka tafi Kano, kamar ko yaushe a gidan Hajja ta sauka a lokacin Didi ma tana gidan ana ta shirye-shirye ana walima gashi washe gari ne ɗaurin aure. Gabaɗaya bata da walwala bata sakewa ayi komai da ita, tana daga gefe tana tunani ko Omar ɗin bata son gani saboda kar ya taso mata da abinda take son binnewa a zuciyarta.
Washe gari da safe aka ɗaura auren Aisha da AbdulHamid, Didi ta sha kukan farin ciki, tayi kuka kamar babu gobe Hajja ce ke aikin rarrashi tana sake tuna mata sai yanzu lokacin auren ta ya yi. Omar ma tunda aka ɗaura auren yake ciki da matuƙar farin ciki, duk da yana daga gefe aka yi komai, Kawu ne ya bada aurenta bai hana hakan ba saboda burinsa a ɗaura auren kuma an ɗaura. Yana sanye da manyan kaya riga da wando na farar shadda sai hula da ya saka, ya kame kansa a waje ɗaya ko magana ma ba yayi sai masu yi masa Allah ya sanya alkhairi.
A gidan Hajja ake taron ƴan uwan su Didi na ɓangaren uwa da uba duk sun zo,musamman su Umma Saroot da suka kasance iyaye a gareta duk suna nan aka ɗaura auren. Su Jidda dasu Salma har da iyayen su Salma ɗin ma duk sun zo saboda kowa ya san Didi.
Ana ta hidima, ko wanne dangi yana so ya nuna ƙauna ga Aisha da ƙaninta. Wannan ya ciko cooler da abinci, wannan ya bada kuɗi a siyo abinda ake buƙata duk burin su su wanke laifin da suka yi a baya. A ɓangaren Didi zata iya cewa ya wuce ta karɓe su hannu biyu matsayin iyaye, babu kamar dangin Maman su in tana kallon su sai ta ga kamar mahaifiyar su take kallo. Ɓangaren Omar ko kallon kirki ma basa samu, in ya gansu bazai nuna ya gansu bama balle ya yi magana. Su kuma tsoron dizgi da wulaƙancin da ya saba yi ne ya saka basa kula shi.
Bayan ɗaurin auren ne Didi ta nemi Nayla ta raka ta gidan su suka fito ita da Nayla da Salma zuwa cikin gidan. Tana shiga takar gidan taga babu kowa sai Omar da yake ya jingina da bango ya harɗe hannayen sa a ƙirji yayi shiru kamar mai cike da damuwa.
"Omar!." Didi ta furta murya na rawa, Omar sai ya kalle ta ya miƙe tsaye sosai ya yi murmushi ya ce, "to meye na kukan Didi?." Da sauri ta ƙarasa wajansa ta rungume shi har lokacin murmushi yake yi ya ɗora hannunsa a bayan ta kafin ya ɗagota daga jikinsa ya riƙe kafaɗarta ya ce, "meye na kuka kuma? Yau ranar farin ciki ce a gare mu gabaɗaya, me ya saka ki kuka?."
"Sai naga kamar baka murna" ta faɗa murya tana rawa. Ɗan ƙaramin tsaki yayi yana murmushi ya ce, "Kiɗa ki ke so kiga na saka? Ko tsalle-tsalle ki ke so ki ga ina yi sannan zaki tabbatar ina murna?." Ta yi dariya kaɗan ta ce, "kusan hakan." Ya kalle ta ya ce, "ban san meyasa ba amma har na fara kewarki, gabaɗaya bana jin daɗi."
Didi ta ce, "Omar nima ina jin hakan a zuciyata, ina ta tunanin wacece zata dinga kula min da kai?." Ƴar ƙaramar dariya ya yi ya kalle ta bayan ya ɗage gira sama ya ce, "yaro ne ni da za a kula dani? Allah Didi kin raina ni" ya faɗa yana share mata hawaye da hannunsa.
Didi ta ce, "Omar rayuwarka kai kaɗai ce bana so, don Allah kawai ka yi aure." Idanu ya wara waje sosai sai kuma ya sake yin dariya mai sauti ya ce, "kawai dan kin yi aure sai nima nayi kamar ƴan wahalar matan su Kawu? Su ne duk abinda ɗaya ta yi sai sun yi." Zata sake magana ya ce, "Didi don Allah ki yi shiru, a bar maganar nan tukunna dai."
"Ka ci abinci yau kuwa?." Ya kalle ta cike da tsonaka ya ce, "waye zai bani abinci? Bani da kowa fa" ya faɗa cike da tsokana yana kallon ta. Sai zuciyar ta sake karyewa ido ya ciko da hawaye ya ce, "Wasa nake miki fa, na ci abinci tun ɗazu. Kar ki yi kuka, Allah bana so." Idanunta goge tana murmushi ta ce, "ni na san cin abincin ka kuma sai yadda hali ya yi tunda babu mai ce maka gashi, daman ya lafiyar kura balle ta yi zawo."
Murmushi ya sake yi ya ce, "Yaushe za a tafi kai ki? Bana son taron mata nan da kaina zan kai ki gidanki" ya faɗa bayan ya ɗaure fuska. Kallon sa tayi ganin ya ci magani alamun da gaske yake sai tayi dariya ta ce, "to babban yaya."
"Da gaske nake, na faɗawa mijin na ki bana son taron hayaniya. Baza a je gida ai ta kallo babu mai addu'a ba."
Murmushi tayi ta ce, "Ai daman kai kullum da gaske ka ke, wannan kalma kamar a bakin ka aka yi ta. Komai ka ce da gaske nake."
"To da ƙarya nake?."
"A'a, indai ka ce to da gasken ne." Share ta ya yi bai sake magana ba, tayi sosai tana mamakin ƙarfin hali irin nasa kafin ta juya ga Nayla da Salma da suke tsaye har lokacin.
Didi ta ce, "Nayla ku shiga ciki na bar ku a tsaye." Kai tsaye inda ta kalla ya kalla ya haɗa ido da Nayla da take murmushi tana hawaye. Salma ya kalla ya ga murmushin itama ta ke yi amma ita babu kuka. Ya ɗan taɓe baki kaɗan ya ce, "ita wannan kullum cikin kuka?" Ya tambayi Salma yana nuna mata Nayla da girarsa.
Ba Nayla da Salma kaɗai ba, har Didi sai da tayi mamakin abinda ya ce, kuma har lokacin idanunsa na wajen fuskarsa a ɗan sake. Nayla ta sunkuyar da kai tana murmushi cikin farin ciki, ko babu komai yana kula da yanayin ta, hakan ya yi mata daɗi sosai har bata san ta riƙe hannun Salma ba. Salma ganin fuskarsa a sake sai ta ce, "tana kewar Didi ne."
Bai amsa ba ya kalli Didi da ta ce, "Nayla tana kuka ne saboda taga Ina kuka, murmushin ma tana yi saboda Ina yi Omar. Bata da lafiya amma ta taho daga Kaduna tazo kawai saboda aurena, Ina ji da ita sosai kamar yadda nake ji da kai. Kai ƙanina ne ita kuma ƙanwata ce." Girgiza kai ya yi bai ce komai ba ya ɗauke kai yana taɓe baki, ya sake kallon gefen da take ya ga kanta a sunkuye amma murmushi take yi.
Didi ta ce, "Nayla mu shiga ciki." Tare suka shiga falon Nayla tana ji kamar kar ta shiga ta tsaya ta dinga kallon Omar tana samun sauƙin abinda yake damunta.
Shigar su babu jimawa suka fito harabar gidan da niyar komawa gidan Hajja. Turus suka yi ganin Narma da Najwa sun shigo gidan har lokacin Omar yana tsaye a inda suka bar shi. Narma ta kalle shi ta ce, "Faruk!." Ɗago idanu ya yi ya kalle ta sai ta zube a wajan tana kuka sosai. Ido ya kulle ya buɗe ba tare da ya kalle ta ba ta ce, "Omar me nayi maka ka ke hukunta ni da laifin da ba nawa ba? Faruk ni meye laifina da ko wayata baka ɗauka?. Na yi maka message sau babu adadi amma ka ƙi ka saurare ni Faruk, meye laifina a maganar nan?."