← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 52

Sashe 48

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda ta rufe ido ruf ya kai bakinsa kunnenta ya ce, "I love you my Baby, I so much love you." Buɗe ido tayi ta kalle shi, man da yake shafa mata ne ya faɗi ƙasa sai ta ɗan firgita ta dawo hankalinta tuna ba fa Omar ɗinta bane Ashraf ne. Ƙwace jikinta tayi bayan ta riƙe towel ɗin da yake a cikin ta dan ya sauke shi daga ƙirjinta. Mayar dashi tayi ta rufe jikinta ta ce, "zaka iya bani waje please?." Kallonta yayi cikin tsananin buƙatuwa ya ce, "Haba my baby, kar ki yi min haka kin ji?."

Kallonsa take yi dan gabaɗaya zuciyarta bata ƙaunarsa, tsanarsa take ji a zuciyarta mai yawa baza ta sake mallaka masa kanta ba sai dai duk abinda zaiyi yayi mata. Sake nuna masa ƙofa tayi ta ce, "ka bani waje bana son ganinka."

Takowa yayi zuwa inda take ta zaburata yi gefe ta ce, "na ce ka bani waje ko? Kar ka sake kuskuren taɓa min jiki wallahi." Jin yadda tayi magana da tsawa ya saka ya buɗe janayen idanunsa ya kalle ta itama shi take kallo ta ce, "kar ka matso inda nake, ka fita ka bani waje bana ƙaunar ganin ka."

Sake takowa ya ke zuwa inda take tana ja baya, da hanzari ya damƙo hannunta tayi ihu ta ce, "Wallahi baza ka sake mallakar jikina ba Ashraf, bana sonka, bana ƙaunarka ka ƙyale ni." Jin abinda tace sai ya ɓata masa rai ya kalleta ya ce, "ni kuma zan nuna miki jikinki nake aure ba ke ba" ya faɗa yana riƙeta da ƙarfin gaske ya fizge towel ɗin jikinta ya jefa ta kan gadon, zata miƙe ya saka ƙafa ya taketa ya danne ta yadda baza ta iya koda motsin kirki ba.

Kuka take tana faɗin, "bana sonka, bana ƙaunarka, na tsane ka." Ya kalleta ya ce, "nima bana sonki, amma Ina son jikinki. Baki isa ki hana ni mallakarsa ba tunda kina amsa sunan matata." Kuka take tana juya kai amma ya riƙeta tamau babu ta yadda zata iya ƙwatar kanta. Tana ji tana gani ya sake yi mata fyaɗe kamar yadda take faɗa, bai ƙyale taba sai da ya tabbatar bakin cewa bata sonsa ya mutu sannan ya tashi.

Sai numfashi take saukewa na wahala saboda azabar da ya gana mata, shi kansa ya wahala amma saboda ya nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane shiyasa yayi mata haka. Wanka yayi ya fito ya kalleta a baje a kan gado tana sauke ajiyar zuciya. Harararta yayi ya ce, "daga yau irin halin da zaki dinga shiga kenan indai zaki dinga cewa zaki yi min gardama, wallahi na daina binki da rarrashi, Igiya zan siyo na dinga ɗaureki nayi abinda nake so na tsallake na ƙyale ki tunda haka kika zaɓa."

Kallon sa tayi murya a shaƙe ta ce, "bazan sake kwana a Texas ba, na faɗawa Mum zan bita taƙi tafiya dani, amma yanzu bazan sake kwana ba."  Baice mata komai ba sai bayan ya shirya ya ƙaraso inda take ya ɗauke wayarta, ya koma inda kayan su yake ya ɗauke passoport ɗinta ya nuna mata ya ce, "wallahi babu inda zaki je, babu ke babu amfani da waya sai lokacin da na ga dama. Ban gama morarki ba har yanzu balle ki ce zaki koma nigeria" ya faɗa yana ficewa ita kuma ta fashe da kuka.

Yana fita ƙofar da zata fitar da kai shi compound na gidan ya canja passoword ɗin ƙofar saboda kar ma tayi tunani guduwa, dan bai gama fanshe wahalar da ta bashi ba, ta tara masa sha'awarta mai yawa tun kafin ya aureta, baza su haɗu su rabu ba sai ya shiga mugun yanayi ba saboba shigar jikinta. Balle in ta kwanta a jikinsa kusan rasa hankalinsa yake yi. Dan haka sai ya gama fashewa son ransa sannan zai ƙyaleta.

•••••••••

Didi har dare tana gida, Omar tunda ya fita ya bar gidan bai dawo ba, ji take ina ma zata iya hana zuwan gobe da tabbas ta hana zuwanta saboda abinda zata tarar a wajan Omar. Gabaɗaya a sanyaye take yin komai har ta yi masa girki ta ajjiye masa.

Bayan sallar magriba ya dawo gidan yayi mamaki da ya ga gidan a buɗe dan bai ɗauka Didi tana ciki ba. Har ya shigo falon bata sani ba ta shiga duniyar tunani, ya zauna ya ce, "Didi tunanin me kike yi?." Kallon inda taji maganarsa tayi ta ganshi a zaune ya zuba mata idanu ta ce, "yaushe ka shigo?."
"Na shigo kina aikin tunani.Wai me yake faruwa ne don Allah?." Tayi ajiyar zuciya, "Sai gobe zaka ji. Ni dai burina kar ka bani kunya Omaar."

"Ko dai AbdulHamid ɗin yake yi miki wani abun da bakya so?." Ta kalle shi ganin yadda ya kafa mata idanu yana kallonta yana jiran amsar ta ce, "Ko ɗaya."
"To meye?" Ya tambaya cike da damuwa da kuma gajiya da maganar.

Didi ta ce, "na faɗa maka zaka ji gobe, amma don Allah....." dakatar da ita ya ce, "zan baki kunya kuwa indai aka yi min abinda bai min ba, bazan yi miki alqawari akan abinda ban sani ba dan haka ki daina roƙona. Wallahi bazan yi alqawari ba kin ji na rantse, haka in aka yi min abinda bai kwantan min ba zan baki kunya" ya faɗa tana kallonta. Ya yi ƙaramin tsaki ya ce, "bazan sake tambayar damuwarki ba, tunda ban kai matsayin na sani ba ki riƙe kayar ki."

Jikin Didi ya sake yin sanyi jin harda rantsuwa, ta san kuma indai ya rantse magana ta ƙare, baya taɓa karya rantsuwa balle ta saka ran zai yi kaffara. Ta zuba masa ido tana kallo cikin rashin sanin abinda zata yi. To da wa zata haɗa Omaar wanda yake jin maganarsa...? Babu kowa a duniyar nan, mutum ɗaya ne tal kuma baya duniya, baya shi babu wani da Omar yake ganin darajarsa, ita ɗin ce kawai kuma gashi da alama za a kai ruwa rana dashi.

Tashi yayi ya fita ya barta a wajan yana mamakin abinda zai faru goben wanda shi bai san dashi ba kuma ta kasa faɗa masa. Har aka yi sallar i'sha tana nan, ya dawo cikin gidan tana zaune ganinsa sai ta miƙe ta ce, "nayi maka girki, ni zan wuce sai gobe."
"Ke kaɗai zaki tafi?."
"A'a, yazo zamu wuce." Kai ya ɗaga mata kawai ya wuce kitchen ta fita jikina matuƙar sanyaye.

Shi kansa Omar ɗin da tunani ta barshi, bayan ya gama cin abincin tunanin abinda zai faru goben yake yi, duk yadda ya kai ga son ganowa ya kasa dan gabaɗaya tunaninsa ya tattara akan wani abun ne akan danginsu ko kaɗan bai yi makamancin tunanin abinda yake faruwa ba. A haka ya gama cin abinci ya ɗan zauna yana danne-dannen waya saboda yanayin sana'ar ta su sannan ya tashi ya fita ya kwanta.

        Washe gari.

        Nayla tun asuba yanyinta ya sake canjawa, ko magana bata iya yi sai dai ta bisu da ido, a haka take zaune ko bacci bata iya komawa ba saboda fargabar da take ciki. Gari yayi haske sosai, a lokacin ƙarfe tara na safe ta jiyo muryar Abiy a kusa da ɗakinta. Miƙewa tayi daƙyar ta kalli Salma da take kallonta tashin ta daga bacci kenan, ta kalli Jidda da take bacci dan a wajena ta suke kwana basa iya barin ta ita kaɗai.

Fita tayi tana fitowa falon suka haɗa ido da Abiy. Ƙarasowa inda yake tayi ta zube a ƙasa ta ce, "Abiy ina kwana."
"Kin tashi lafiya? Ya jikin?."
"Da sauƙi" ta furta a sanyaye ya kalli Mama da tazo wajan ya ce, "kiyi hanzari ki shiryata bana so lokacin sallar azahar ya yi ba ku wuce ba. Nan da sha ɗaya nake so ku wuce gidan Hajja" Abinda ya ce kenan y bar wajan Nayla ta kasa koda motswa.

Mama ce ta ƙaraso ta ɗagota ta rungume a jikinta ta ce, "mahaifinki baya fushi dake Nayl,  ya kamata ki fahimta ki daina asarar hawayenki haka, baki da lafiya koda dan lafiyarki ki nutsu don Allah." Nayla bata ce komai b, a lokacin Jidda da Salma suka fito falon Mama ta kalle su bayan su gaisa ta ce, "Ku kawo mata abinda zata ci." Jidda ce ta sauka da kanta ta kawo musu abinci suka ci ita dai daƙyar ta iya shan tea.

Bayan ta gama Mama ta kalle ta ta ce, "muje ki yi wanka." Hannunta ta riƙe har ɗaki da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta ce tayi. Nayla ta shiga banɗakin jiki a sanyaye tayi wanka ta fito, Mama ta fita ba jimawa ta dawo da kaya ta ajjiye mata ta ce, "ki saka wannan" ta faɗa  tana bata waje. Salma da Jidda ne suka shigo ta kalle su ta ɗauke kai dan bata iya cewa komai, hawayen ma ya gama ƙafewa a idanunta.

A haka ta saka kayan a kasalance, atamfa ce mai tsadar gaske ɗinkin doguwa bubu. Tana gama sakawa Mama ta shigo ta ɗauki mayafin ta yafa mata ta ɗauki turare akan madubin ta fesa mata ta ce, "mahaifinki yana jiranki, zo mu je" ta kalli Jidda da Salma ta ce, "Ku haɗa mata kayan da zata yi amfani dasu kafin a haɗa mata duka." Amsawa suka yi a sanyaye ganin da gaske anyi auren Nayla har ana niyar kaita gidan mijinta. Ba jimawa sai ga Jalila da babbar trolly bag ta kawo musu, suka karɓa duk kayan da hannun ya kai suke watsawa a ciki.

Abiy yana zaune a falo shida Yaya da Jawad Mama ta shigo da Nayla tana riƙe da hannunta. Tunda Abiy ya ga Nayla a haka sai jikinsa ya yi sanyi matuƙa, ya bita da kallo cikin wani irin yanayi wanda bai yi tunanin zai ji shi a lokacin ba.

Nayla ta zauna a akan carpet Mama ta ce, "Abiy ga ta kamar yadda ka ce." Abiy ya kalle ta ya ga kanta yana ƙasa, ya yi ajiyar zuciya yana kallonta kafin ya ce, "Hauwa!." Wani irin dum taji a zuciyarta ta runtse, hawayen da ta nema ta rasa suka fara cikowa a idanunta tare da sakkowa kan fuskarta.
Chapter 48 · 0% Book details