← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 52

Sashe 30

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai na san ka sansu, shiyasa ana nemo ka dan ka taimaka min." Omar yaja numfashi ya kalle shi ya ce, "ni unguwar da nake babu wannan matsalar gaskiya, sai dai sauran unguwanin."
"Su nake so ka bani list na waɗanda ka san basa jin magana." Omar ya girgiza kai kafin ya kalle shi ya ce, "To ni yanzu bazan iya banbancewa ba saboda kaga na jima da fita harkar nan, kullum samun sabbabin fuska ake yi musamman yaran da ka faɗa wanda suke fara ta'addaci saboda babu. Amma idan na tattara zan turo maka koda ta waya ne." Dpo ya ce, "na gode sosai Damisa. Samun irin ku masu taimakawa hukuma abin alfahari ne sosai." Ya kalli Bashir ya ce, "ma sha Allah! Kaima ka dawo kamar Ogan ka."

Bash ya ce, "duk inda Damisa yake a nan muke." Murmushi yayi ya ce, "Gaskiya ne. Gwara hakan, yanzu kowa ya ganku ya ga mutanen kirki. Duk da dai daman Damisar naku bai yi irin kamannin ku ba." Omar miƙewa yayi suka sake gaisawa da shi sannan ya fita suka wuce shago kai tsaye.

Ana ta aikin takalma shagon ma ya yi kaɗan sai da aka sake karɓar wani haya aka haɗa biyu saboda ɗaya ya matse. Ya jima a can sai bayan sallar la'asar sannan suka koma gida Bashir yana sauke shi ya tafi shi kuma ya shiga gida.

Kallon gidan ya tsaya yi domin an share shi tass babu ƙura ko kaɗan sai ƙhamshi yake yi, ya yi murmushi dan ya san aikin Didi ne ya shiga falon da sallama. A zaune ya same ta tana waya yana shigowa ta kashe wayar ta ce, "ina ka shiga tun safe?." Zama ya yi ya ce, "na je shago ne. Ni na ɗauka kin tafi."
"Ban tafi ba, sai zuwa magriba zai zo mu tafi." Bai amsa ba ta ce, "da sai na fita na bar gidan a buɗe?."
"Yau aka fara?" Ya faɗa yana kallonta.

"To kaje dai ka ci abinci."
"To Didi, an gode." Kallon sa dai take yi cikin tausayi dan gabaɗaya tausayi yake bata, rashin uwa babban masifa ce a duniya, inda ace mahaifiyarsu tana da rai da Omar bazai yi maraici dan tayi aure ba. Tashi yayi ya shiga kitchen ɗin sai ga shi ya dawo da abinci a bowl ya zauna yana ci sai aka kira shi a waya ya ɗauka yana amsawa duk magana akan sana'ar da ya fara ne kafin ya kashe.

Kallon sa ya ga tana yi ya ɗauke kai bai ce komai ba, ya kuma kallonta ya ga dai kallonsa take yi ya ce, "Didi ya dai?."
"Omar ka daure ka yi aure don Allah." Ya ɗan yi murmushi kaɗan ya ce, "Ikon Allah, wai meye damuwarki akan nayi aure ne?."
"Saboda ina so ka fita daga maraicin nan da ka ke ciki."

"Wa zan aura?."
"Ga mata nan da yawa sai wacce ka zaɓa. Ka duba yadda ka koma saboda rashin mai kula dakai." Ɗan taɓe baki ya yi ya ce, "to zan yi."
"Ko ka bani dama na zaɓa maka matar?." Kallon ta yayi sai ya ɗaga mata gira alamun eh ta ce, "da gaske fa nake."
"Nima haka" ya bata amsa yana cigaba da cin abinci dan so yake ya katse zancen auren nan da take yawan yi masa.

Kamar yadda ta ce sai bayan sallar magriba AbdulHamid yazo suka shiga har wajan Hajja suka gaisa sannan suka fito, Omar ta kira a gida suka gaisa yana ta tambayar yaushe zai kawo musu ziyara ya ce zai zo. Sallama suka yi suka tafi shi kuma ya koma gida zuciyarsa babu daɗi ko kadan.

••••••••

Ashraf duk yadda ya kai ga rarrashin Narma abin ya ci tura sai kuka take yi kamar ranta zai fita, hankalinsa ya tashi sosai dan bai ɗauka zata yi kuka har haka ba. Ya ɗagota jikinsa yaji jikinta akwai zafi alamun zazzaɓi ya ce, "Haba my love! ki daina wannan kukan mana, jikinki yayi zafi sosai." Narma ta ture hannunsa daga jikinta ta ce, "ka ƙyale ni."

"Ta ya zan ƙyale ki bayan baki da lafiya? Ki tashi na kai ki asibiti kinji." Tsaki tayi ta juya ta kwanta tana share hawaywe. Babban baƙin cikinta da Ashraf ya same ta a banza a wofi, ta so tayi tattalin jikinta har ta kai wa Omar masoyinta amma gashi a banza a wofi ya same ta komai ya lalace.

Shi kuwa Ashraf baya ya koma yana kallonta, sai da ta gaji da kukan dan kanta sannan tayi bacci ya tsaya yana kallonta. Murmushi ya yi yana shafa fuskarsa, tarin sha'awarta da yake ji gabaɗaya ta kau sai shauƙi da ya ke mamaye masa zuciya. Leɓensa yake lashewa a hankali in ya tuna irin abinda ya tarar a jikinta sai yaji tsigar jikinsa na tashi har yana mararin sake kai kansa gare ta.

Ta jima tana bacci har akayi sallar i'sha sannan ta farka, tunawa da abinda ya faru da ita sai baƙin ciki ya mamaye zuciyarta, tsanar Ashraf ta yi mata dirrar mikiya a zuciyarta. Daƙyar ta iya tashi ta kai kanta banɗaki ta jima a ciki sannan ta fito. Doguwar riga kawai ta saka ba tare da ta saka komai ba ta saka hijjabi ta tayar da sallah. Jiri taji yana ɗaukarta a tsaye sai da ta zauna ta iya ƙarasa sallar.

Tana idarwa kiran Mum ya shigo wayarta ɗauka murya a dashe ta ce, "Mum!." Daga can ɓangaren Mum ta ce, "Subahanallah! Daughter me ya same ki? Kar ki ce min kuka kika yi?." Narma ta ce, "Mum bana son zama a nan ni gida zan dawo, bana son zama da Ashraf baya sona ko kaɗan."
"Me ya faru?."
"Mum raping ɗina yayi" ta faɗa murya na rawa alamun kukan zata sake yi. Mum da mamaki ta ce, "raping! Ashraf ɗin ne yayi raping ɗinki?."

Narma ta ce, "Eh Mum." Mum ta ce, "Narma! he's your husband fa, dan hakan ya faru baza ki kira shi da raping ba."
"Amma Mum ai ya faru ne without my consent, ya san bani da lafiya bana cikin nutsuwata amma bai iya ƙyale ni ba sai da yayi raping ɗina. Ya bari na amince mana, ya bari na samu lafiya mana. Ni na gaji bazan iya zaman nan ba Nigeria zan dawo."

Mum ta tausasa murya ta ce, "i'm sorry, yanzu me kike ji?." Narma a shagwaɓe ta ce, "my whole body is in pain, I can't event sit properly. Mum I don't think I can stay here anymore" ta faɗa a sanyaye cikin sangarta da shagwaɓa. Mum ta ce, "ki daina kuka, kin sha magani?."
"Uhum uhum."
"Ina Ashraf ɗin?."
"I don't know."
"Okay, let me call him to take you out to hospital" Tana faɗar haka ta yanke kiran.

Ba jimawa Ashraf ya shigo ya ƙaraso ya ɗuka a gabanta ya ce, "i'm sorry my love, I'm sorry. Tun ɗazu nace mu je asibiti kika ƙi, yanzu ga Mum ta kira ni tace na kai ki asibiti. Please saboda Mum ki tashi mu je kin ji?." A tausahe yake maganar amma jin maganarsa take yi kamar ta aljanu saboda haushinsa da take ji.

"Please my love!" Ya sake faɗa yana kallonta tare da ɗagota ta miƙe tsaye. Zare hijjabin jikinta ya yi ya ajjiye ya kalle ta ya ce, "na saka miki kayan?." Idanunta a kulle yake ya kalli kayan jikinta yaga ana hango komai na jikinta. Wajan kayanta yaje ya duba ya ɗauko doguwar riga wacce tafi ta jikin ta kauri sai dai itama roba ce. Bai damu ba ya ƙaraso ya bata ya ce ta saka.

Zame ta jikinta tayi ta fara saka wacce ya bata yana tsaye yana kallonta, lumshe ido yayi yana sake ƙarewa surarta kallo da take a bayyane babu abinda ya rufeta. Ashe duk abinda yake gani a cikin kaya yana ɗaukar hankalinsa ba komai bane, yanzu ne yake ganin asalilin sura da abinda ya aura, dan shi kam surarta ya aura dan ba ƙaramar sha'awarta yake yi ba. Babu abu mai ɗaukar hankali a jikinta kamar ƙugunta, hips ɗinta a cike yake sosai ga wrist ɗin nata ɗan ƙarami kuma siriri hakan ya bawa shape ɗinta damar fita sosai, in ta juya baya boobs ɗinta ma abin kallo ne.

Daƙyar ya iya kawar da kai ta saka kayan amma taƙi motsawa ƙarshe sai dauƙota ya yi suka fito harabar gidan. Da yake akwai mota a apartment ɗin da suke yana fita ya ajjiyeta ya buɗe garage ya ɗauko mota sannan ya sake fitowa ya ɗauketa ya sakata ciki suka tafi. Koda suka je can ma duba ta aka yi aka bata magani aka saka mata drip dan jikinta ya saki. Bacci ta sake yi shi kuma yana tsaye yana kallon ta cikin tsantsar shauƙi da son sake kasancewa da ita a karo na biyu.

••••••••

        Da daddare hankalin Nayla sam baya jikinta kasancewar washe gari shine ranar da Abiy ya bata zata faɗa masa waye zaɓinta. Bata cikin kwanciyar hankali dan bata san abinda zata ce masa ba. Tana zaune a falo tana kallon tv amma ba fahimta take yi ba tunanin ta na ga abinda zata cewa Abiy ya amince da ita. Dan ita dai ta san bata son waɗannan mutane, in tace ta ɗauki ɗaya wanda zata iya zaman aure dashi ta cuci kanta ne, kuma kamar yadda Mama ta faɗa zata dinga kwasarwa kanta zunubi ne kawai.

Mama ce ta shigo ɗakin har ta zauna kusa da ita bata sani ba sai da ta taɓata sannan ta kalleta ta ce, "Nayla tunanin me kike yi haka?." Nayla ta sauke numfashi tace, "Mama tunanin gobe nake yi, ban san me zan cewa Abiy akan maganar nan ba."
Chapter 30 · 0% Book details