Sashe 44
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "Hajja ban sani ba ko kin ji labarin abinda ya faru, amma jiya yanayin ki ya nuna min kamar baki sani ba." Hajja ta murmusa ta ce, "eh ban sani ba, ɗazu ake sanar dani abinda ya faru."
"Hajja meyasa Abiy ya yiwa Nayla haka?."
"Babu wanda ya san dalilinsa, dan yanzu haka ma ya saka ana ta siyan kayan gida."
Didi ta ce, "Ɗazu Mamanta da kanta ta kirani tana tambayar inda za a kawo kaya da kuma adadin ɗakunan gidan, wallahi Hajja ni gabaɗaya kaina ya kulle na rasa abinda zanyi, wanne irin aure ne wannan ya yiwa Nayla? Ta sani ko bata sani ba duk bamu da tabbas a kai."
"Wannan dalilin ya saka Salma tace zata je Kaduna gano yanayin Nayla ɗin. Amma ke kin san daman tana son Omar?."
Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "na sani Hajja. A ranar ɗaurin aurena kin san yarinyar nan Narma ta Abuja tazo, to a ranar bayan ta tafi na taho nan na bar su a can suke hirar su uku, ita da Jidda da Salma. A lokacin naji komai na kuma tausaya mata domin soyayya bata yi mata adalci ba, Ina ita Ina Omar? Ba sa'ar auren Omar ba ce ita kanta ta sani, sannan Omar ba mutum ne kamar kowa ba, ko wanne uba ne zai bashi auren ƴarsa ba."
Hajja ta ce, "ni babban abinda yake bani mamaki dalilin yin auren da gaggawa haka, meye ra'ayinsa akan wannan auren har ya aikata haka?." Didi ta ce, "wallahi ban sani ba, nima shine abinda yake damuna."
Hajja ta ce, "yanzu Omaar ɗin ya san batun auren?." Kamar zata yi kuka ta ce, "Wallahi Hajja bai sani ba, babban tashin hankalina ma bai wuce tunkararsa da maganar nan ba. Kin san halinsa Hajja, kin san abinda zai yi da wanda bazai yi ba, yadda zan tunkare shi da maganar nan shine abinda yake ɗaga min hankali."
Hajja ta ce, "tabbas zaiyi, zai yi abinda ba ki tunani ba ma dan Omat ya wuce tunanin mu gabaɗaya.." Didi ta ce, "To Hajja wannan ai kin ga akwai rashin kyautawa ita Nayla ɗin, sannan akwai zubar da mutuncinta na ƴa mace. Ace an ɗaura mata aure da wanda ake tunanin zai karɓi auren ko bazai karɓa ba, kinga kamar ba'a kyauta mata ba."
Hajja ta ce, "babu wanda ya san dalilin mahaifinta na aikata haka, ban sani ba ko ita Nayla ɗin ta san zai ɗaura mata aure dashi oho? Amma yanzu me ki ka yanke?."
"Wallahi ban sani ba, ga dai gida Kawu ya bayar kyauta, ya kuma ce min don girman Allah kar na bari Omar ya san shine ya ba da gidan. ni ko zuwa ban yi na duba gidan ba."
Hajja ta ce, "nima a shawarata kar ki faɗa masa yanzu, ki bari komai ya daidaita tukunna sai ya sani."
"Hajja kar yazo yana ɓatawa mutane rai fa."
"Ki ƙyale shi, ki bari sai nan gaba. Ko da ace ma Nayla ta tare a gidansa ki bari sai zaman yayi nisa sannan ki faɗa masa." Dogon numfashi Didi taja ta ce, "Hajja anya haka baganganci bane? Omar fa?." Hajja tayi dariya ta ce, "kar ki damu, komai zaizo da sauƙi in sha Allah. Ni a jikina nake jin shine mijin Nayla, wannan auren nasu aure ne na har abada. Karki damu mu cigaba da yin addu'a kawai." Didi ta ce, "To Hajja, Allah ya sa haka shine mafi alkhairi" ta faɗa kawai ba dan har zuciya ba. Hajja ta amsa da Amin.
•••••••
Ashraf yana tsaye a falo yaji an danna door bell daga ƙofar falon, ya ƙarasa ya buɗe da mamaki yake kallon wanda suka zo. Mum ce sai kuma Najwa ya basu hanya tare da murmushi ya ce, "Mum sannu da zuwa." Murmushi tayi ta ce, "Yauwa Ashraf, mun zo babu notice ko?." Ashraf ya murmusa ya ce, "Haba Mum babu komai, have a seat." Mum ta zauna Najwa ma ta zauna.
Mum ta kalle shi bayan ya zauna ya ce, "Good morning Mum."
"Morning Ashraf, ya kake?."
"Am fine Mum. Ya hanya?."
"Alhamdu lillah. I hope komai yana lafiya tsakaninka da matarka?."
"Yes Mum, Alhamdu lillah."
"Glad" Mum ta faɗa da murmushi.
Najwa ta kalle shi bayan sun gaisa ta ce, "where is she?." Ashraf ya ce, "Tana ciki." Najwa ta miƙe ta shiga cikin bedroom ɗin wajan Narma.
A kwance ta hangi Narma ta rufe kanta da blanket ta ƙarasa ta buɗe fuskarta. Ganin yadda fuskarta tayi ja ya bawa Najwa mamaki, ta taɓa fuskar ta tana mamakin me ya kawo wannan jan. Narma da ta fara bacci tashi ana shafa fuskarta ta fusata ta bige hannun tare da zabura ta ce, "Ashraf stop it, how dare you to touch me?."
Najwa ta ce, "easy Sis! It's me, Najwa." Narma ta kalli Najwa da take kallonta ta ce, "Najwa!." Najwa ta ce, "yes Sis." Sai ta miƙe zaune ta riƙe hannunta ta ce, "Najwa yaushe kika zo?."
"Yanzu, nida Mum ne, tana falo...." Bata ƙarasa ba Mum ta shigo ɗakin. Narma ganin Mum ta shigo sai ta miƙe da sauri ta ƙarasa ta rungume Mum. Mum ta yi hugging ɗin itama tana shafa bayanta ta ce, "My daughter, I missed you."
"Likewise Mum." Mum ta ɗagota tana kallon fuskarta ta ce, "meya faru naga fuskarki tayi ja haka? Are you okay?."
Narma ta ce, "Mum I'm not okay, bana son zama a nan ko kaɗan." Mum ta ce, "stop crying mana, just calm down and let me know what is happening to you." Narma ta ce, "Mum Ina Dad?."
"Dad yana Nigeria. Na taho ne dan na ganki, na damu da rashin ki shiyasa muka zo." Narma ta ce, "na nemi flight nima ban samu ticket ba, da tuni na dawo gida."
Mum kallon fuskar ta take yi ta ce, "So faɗa min me ya faru be?." Narma ta ce, "Mum I hate him, I don't want to see him."
"What are you saying Narma? He's your husband fa." Narma ta ce, "Mum baya sona, he raped me again!" Ta faɗa tana kwanciya a kafaɗar Mum tana kuka.
Riƙeta Mum tayi suka zauna a kan gado ta ce, "ya sake raping ɗinki?." Ta ɗaga kai alamun eh ta ce, "Bana son shi, gida nake so na koma. Ihu yake yi min yana yi min shouting, Sannan ya ce shima baya sona." Mum ta bita da kallo cikin mamaki da ɓacin rai, Narma ta kuma cewa, "Mum ni dai bana sonsa, zan dawo gida kawai." Ashraf ne ya shigo ɗakin Mum dai bata yi magana ba ta bishi da kallo har ya ƙaraso ya ce, "Mum ga takeaway."
Mum ta kalle shi ta ce, "Aheaf me yake faruwa ne? Kalli face ɗin Narma me ya same ta haka?." Ashraf ya kalli Narma da take hawaye ya kalli Mum ya ce, "Mum bata manta da shashashan ɗan daban nan ba, always she'stalking about him,
I'm so jealous when she mentions him." Mum ta kalli Narma ta ce, "Narma why?." Narma ta ce, "Mum ni Nigeria zan koma, na gaji da zama a nan, na gaji bazan zauna ba."
Mum ta ce, "is okay" Mum ta faɗa tana miƙewa tana riƙe da hannun Narma har falon. McDonald yayi musu order Mum bata ci ba, ta dai ci chips ɗin daga nan bata sake cin komai ba. Gabaɗaya tunani take yi akan zaman Ashraf da Narma, kana ganinsu ka san basa zaman lafiya kowa da abinda yake ɓoyewa a zuciyarsa. Kallon Narma tayi ta ce, "Zamu koma hotel, kwana biyu zamuyi zan koma. Don't worry in anjima zamu tattauna abubuwan da suke faruwa, yanzu na gaji, I need rest."
Narma ta ce, "Mum zanje."
"No Narma, ki zauna a nan zan dawo. Kar ki damu komai zai zama daidai" ta faɗa tana shafa fuskarta. Narma ta ɗaga kai suka fita, ko fita raka su bata yi ba shine dai ya rakasu.
Yana dawowa ya kalleta ya ce, "har kina da bakin cewa kin gaji da zama dani?." Banza tayi masa bata amsa ba, yayi tsaki tare harararta ya bar wajan dan haushinta yake ji bai san meyasa ba, duk tarin soyayyar da yake yi mata gabaɗaya ta gushe yanzu baya jin ko kaɗan akan abinda yake ji a ba
Nayla tana kwance a ɗaki taji an dafata, ta buɗe ido ganin Salma sai ta zabura ta ce, "Salma!." Sai kawai ta rungume ta tare da fashewa da kuka. Salma ta ce, "ki daina kuka Nayla, ki nutsu jikinki akwai zafi." Nayla bata daina kuka ba ta ɗago daga jikin Salma ta ce, "Salma Abiy yana fushi dani, ban sani me na yiwa Abiy ba Salma. Salma wai Abiy ya aura min Omar, Meyasa Abiy yayi haka?."
Salma ta ce, "shiyasa nace ki nutsu ki dawo hankalinki sai muyi magana. Amma yanzu kin ci abinci?." Ta girgiza kai alamun a'a Salma ta tashi ta fito ɗaga ɗakin. Falo ta fito wajan Mama ta ce, "Mama akwai abinci?." Mama ta ɗauka ita zata ci ta ce, "akwai mana Salma, duba ki zuba abinda zaki ci." Da to ta amsa ta ƙarasa ta zuba abincin har da tea ta haɗawa Nayla sannan ta koma ɗakin.
Daƙyar ta lallaɓata tasha tea ɗin, ta bata maganin da ta gani a gefenta sannan ta riƙe hannunta bata ce mata komai ba. Sai da taga ta nutsu tana ajiyar zuciya sannan ta ce, "ya akayi haka ya faru?." Girgiza kai take yi alamun bata sani ba. Salma tayi ajiyar zuciya ta ce, "ke kika faɗawa Abiy kina son Omar?."
"Mama ce" ta bata amsa murya na rawa.
"To meyasa ya yanke wannan hukuncin? Ko daman ya ce zai aura miki shi ne?."