Sashe 40
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin motsinsa sai ta kalle shi tana zare hijjabin daga jikinta, ajiyar zuciya ya yi ganin rigar jikinta wacce tayi daidai da yadda yake so ya ganta. Iyakar rigar guiwa tana da hannu mai ɗan girma kaɗan amma bata da kauri sannan tana bin jiki. Zama tayi a gefen gado tana kawar da kai dan tun lokacin da ya same ta sau ɗaya bata sake bari hakan ya faru ba.
Murmushi yayi ya ce, “My Love zamu iya fita?.” Kallonsa tayi ta girgiza kai alamun a’a ya ce, “Haba my love, ki amince muje ba jimawa zamu yi ba dawo. Kullum kina gıda, tunda muka zo bakya fita.” Bata ce masa komai ba yazo kusa da ita ya zauna yana ƙare mata kallo, halittarta na burge shi sosai, amma yanzu abinda yake ji a kanta ya ragu da kaso mai yawa, kawai ya san yana son kasancewa da ita bayan wannan babu wani abu a zuciyarsa a kanta.
A hankali ya kai hannu ya fara shafata ya ce, “My love muje mu dawo. Ko kina so mu taje miami mu kalli ball ɗin messi?.”
“Pls Ashraf ka ƙyaleni, babu inda zanje in kai zaka je kaje amma ka daina saka ni ciki” ta faɗa tana kawar da kanta gefe.
“Come on my love” ya faɗa yana yajowata jikinsa lokaci ɗaya yana ƙoƙarin zare rigar jikinta. Da hanzari ta fincike jikinta ta miƙe tsaye ta ce, “kar ka sake wannan kuskuren, wancan ka damu dama a banza a yanzu baza ka samu ba. Ka tashi ka fita ka bani waje bana son ganinka, wallahi na tsaneka, ka fahimi bana so ganin koda fuskar ka ne.”
Kallon ta yake yi jin wai ta tsane shi ya ɗan buɗe idanu tare da taɓe baki ya miƙe shima yana kallonta ya ce, “kin tsane ni kika ce?.”
“Eh natsane ka, bana son ganinka ko kaɗan.”
“Wannan mahaukacin yaron kike so?.” Ba tare da shakka ba tace, “eh shi nake so, ganganar jikina kawai kake tare da ita a nan amma zuciyata tashi ce. In ka sake kuskuren zuwa kusa dani zanyi maka illa babba a jikinka.”
“Wow! Daman ni ai ganganar jikin naki nake da buƙata ba zuciyarki ba Narma. Jikinki nake so kuma na riga na mallaka, ko yanzu nace Ina son wani abu a tare dake baki isa ki hana ni ba. Dan yana riƙe da zuciyarki Ina riƙe da jikinki hakan yayi min daidai. Da ki soni, da kar ki soni ni dai ina son jikinki.” Narma ta bishi da kallo kamar zata yi magana sai ta fasa ta koma gefe ta harɗe hannaye a ƙirji bata ce komai ba.
Ashraf ya ce, “this is the last time da zaki sake yi min maganar sa a nan, ni mijinki ne ko bakya so, in kika sake ambatar wancan shashashan mara hankalin a gabana ranki zai ɓaci matuƙa.” Harararsa tayi ta ce, “Sai na faɗa baka isa ka hana ni ba, kuma kaine shashasha mara hankali amma ba shi ba. I love Faruk! I love him!i love him!! I love him!. In kaga dama ka kashe ni kar ka barni da rai” ta faɗa tana harararsa cike da jin haushi da tsana.
A firgice ya tako inda take ya na zare mata idanu ya ce, “ni kike kira da mara hankali Narma?.”
“Eh na faɗa, baka da hankali…..”bata ƙarasa ba ya ɗauketa da mari mai zafi yana huci. Sai da ta gigice jin zafin marin da yayi mata, in tace tunda take Dad ne kawai ya taɓa dukanta lokacin da Omar yaje gidan su bata yi ƙarya ba, amma kafin nan iyayenta basu taɓa marin ta ba tunda tazo duniya, zata iya cewa babu wanda ya taɓa marinta a duniya bayan Dad sai shi. Nan da nan idanunta suka yi ja ta kalle shi ta ce, “ni ka mara Ashraf?.”
“Na mare ki, in ki ka sake furta maganar da kika furta wallahi sai na yi miki dukan tsiya a wajan nan.”
“Ni Narma ni ka mara?” Ta amsa faɗa tana kallon sa. Ta ɗaga hannu zata rama ya riƙe hannun tare da murɗa shi baya, tayi ƙara mai sauti tana runtse ido.
Ashraf ya ce, “lallai baki da hankali, ni zaki daka?.” Narma ta ce, “to ka sake ni, bana son aurenka, ka sake ni na koma gida bana sonka.”
“Nima bana sonki amma bazan sake ki ba, zama dake nake so yi ko dan na mallaki jikinki a duk lokacin da nake so” ya faɗa yana jawowa jikinsa da ƙarfi ya fara kissing ɗinta da zafi-zafi cike da mugunta. Da faɗa da dambe da Asharaf ya samu yaje inda yake so yaje a jikin Narma, tun tana fizge-fizge har ta daina ta koma zubar da hawaye cikin ƙunar rai da kuma ƙunar zuciya.
Shi kam Ashraf ko a jikinsa, abinda yake so a tare da ita ya samu yana barin wajan yaji gabaɗaya haushinta yake ji, abinda yake ji a zuciyarsa gabaɗaya ya kau, indai yana jin shauƙi akanta to tabbatar akwai abinda yake buƙata a tare da ita, da zarar wannan buƙata ta gushe shikenan sai yaji ta fita daga ransa gabaɗaya komai tayi baya burge shi. Kallonta ya yi tana kuka yaja tsaki ya fita ya barta a wajan bai ko sake kallon ta ba.
Narma daƙyar ta iya miƙewa ta shiga banɗaki tayi wanka ta fito da zazaaɓi da ciwon kai. Hannu na rawa tasha shan pracetamol sannan ta ɗauki waya hannunta na karkarwa tana neman ticket na Nigeria dan baza ta sake kwana a America ba, gida zata koma duk abinda zai faru sai dai ya faru amma ta gaji.
•••••••••
Nayla ta shirya tana jiran Baba Salisu yazo su tafi tana zaune a falon Hajja, gabaɗaya jikinta babu daɗi ji take kamar tayi ihu bata san dalilin faruwar hakan ba. Hajja ta kalleta ta ce, “gashi ba a siyawa Abban naki gurasa ba, ko zaki jira?.”
“Hajja ki ƙyale shi kawai, ai duk zuwa kina siya masa wannan dan ba a siya ai ba komai.”
Hajja tayi shiru bata ce komai ba amma zuciyar ta bata yi mata daɗi in taga Nayla a wannan yanayi na damuwa. Babu abinda zata iya, ta tambayeta tace babu komai amma ba dan ta amince ba. Tana zaune ba jimawa Baba Salisu ya ƙaraso kamar ko yaushe ta kai masa ruwa ya sha yace ba sai ya huta ba tazo kawai su wuce. Sallama ta yiwa Hajja da Salma ta shiga motar suka tafi gabanta yan faɗuwa bata san dalilin hakan ba.
Tafiyar awa uku ta kai su garin Kaduna har cikin gidan su Nayla. Yana faka motar ta fito tare da jakar kayanta zuwa cikin gidan. Faɗuwa gabanta yake yi abinda bata taɓa ji ba in ta dawo daga Kano, ta saba tana jin zumuɗin ganin ƴan gidan amma yau ta rasa meyasa take ji haka.
Da sallama ta shiga babban falon Mama ce kawai sai Jalila suka amsa mata ta ƙaraso ta ce, “Mama na dawo.” Mama ta bita da kallo ta ce, “sannu da zuwa, na ɗauka sai gobe.”
“Yaya J ne ya kira ni yana ta faɗa ya ce lallai na dawo yau.”
Gaisawa suka yi da Mama Jalila ta kalle ta ta ce, “Ashe Abiy bai san kin tafi Kano ba? Bayan kin tafi ya dinga faɗa.” Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, “na dawo na bashi haƙuri” abinda tace kenan ta miƙe ta wuce zuwa ciki. Sai da tayi wanka tare da yin sallar azahar, tana idar da sallar Jawad ya shigo ɗakin nata abinda bai saba ba. Da kallo ta bishi ta miƙe tsaye ta ce, “Yaya J Ina yini.”
Harara ya sakar mata ya ce, “Nayla ashe baki da hankali ban sani ba? Ashe ilimin ki bashi da amfani?.” Nayla ta sunkuyar da kai duk a tunanin ta akan son da ta ce tana yiwa Omar yake wannan maganar.
“Yanzu Nayla sai ki saka ƙafa ki bar Kaduna ba tare da sanin Abiy ba? Guduwa kike son yi saboda an hana ki auren ɗan daba ko?.”
Ta girgiza kai ta ce, “ba guduwa nayi ba Yaya J, kuma Mama…” dakatar da ita yayi ya ce, “Mama me? Me maman tayi?. Kin bani mamaki wallahi, kin kuma cuci kanki, kin cuci rayuwarki, in kai kanki inda zaki sha wahala. Ba dai kin zaɓi ɗan daba akan mahaifinki ba? Kin zaɓi ɗan daba akan mu, kin zaɓi ɗan daba akan iyalan gidan nan gabaɗaya ko?. Shikenan gaki gashi nan sai ki je ki kwaɗa soyayya ki cinye, banza mara hankali!” ya faɗa yana harararta cike da ɓacim rai.
Gaban Nayla ta faɗi tana tunanin yaushe ta zaɓi Omar akan su kuma?. Bata damu da faɗan da yake mata ba duk da karo na farko kenan a rayuwarta, ta kalle shi ta ce, “Wallahi Yaya J ni ban zaɓe shi na barku ba, taya zan zaɓe shi na bar ku?. Ni na haƙura ma fa, na haƙura bazan sake maganar ba in sha Allah.”
“Ko kiyi min shiru ko na buge miki baki, haƙurar taki me zata hana faruwarsa yanzu kuma? Ai aikin gama ya riga da ya gama. Tunda haka ki ka zaɓa gaki ga shi nan ai” ya faɗa yana fita daga ɗakin nata.
Jikin ta gabaɗaya ya gama yin sanyi, dana sanin tafiya Kano ya mamaye mata zuciya. Amma Mama ce tace ta tafi ta ɗauka zata yiwa Abiy bayani in ya tambaya. Da wannan sanyi jikin ta fito falo. Gabanta ya faɗi da ta hango Abiy a zaune yana cin abinci, ga Yaya, ga Yaya J, ga Mama, da kuma Jalila. A hankali take takowa zuwa tsakiyar falon ta zauna akan carpet ta ce, “Abiy Ina yini.”