Sashe 41
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallonta yayi yana tuna irin abinda ta sake turo masa cikin wayar, ya kasa yarda Nayla ƴar cikinsa zata iya aikata abinda ta aikata masa akan soyayya, har tana cewa ta zaɓi ta zauna dashi akan shi da ya haifeta. Zafin kalaman yake ji a zuciyarsa sosai, hakan ya saka ya kafa mata ido ba tare da ya sani ba. Sai daga baya ya ɗauke idanunsa ya ce, “Har kin gaji da zaman Kanon?.” Nayla ta ce, “Daman ba zama zanyi a can ba.”
“Zaman can ya kama ki kam yanzu” ya faɗa yana cigaba da cin abinci.
Shiru falon yayi bai ce mata komai ba itama bata ce ba, sai daga baya ya ce, “naga saƙonki, hala dai ke kika rubuta ko?.” Nayla ta ɗaga kai ta ce, “ni ce Abiy. Ka yi haƙuri in na ɓata maka rai.” Girgiza kai yayi ya ce, “ɓata min ran me zaka yi Nayla? ke ki ka zaɓi abinda kike so, kuma abinda yake zuciyarki kika faɗa min, Meye zai bata min rai a kalaman ki?. Ai haka ki ka zaɓa ko?” Ya faɗa yana kallonta.
Nayla ta ɗaga kai a sanyaye ta ce, “haka na zaɓa Abiy, kayi haƙuri” ta faɗa kai tsaye tana sunkuyar da kai. Abiy ya girgiza kai cikin tsananin jin zafin amsar da ta bashi, ya kalle ta zai sake magana sai ya fasa saboda abinda yake ji a cikin zuciyarsa game da ita.
Shiru yayi na wani lokaci yana sarrafa zuciyarsa sannan ya ce, “shikenan tunda haka ki ka zaɓa ai aikin gama ya gama. Ga Maman ki nan, kuje kasuwa tare duk abinda ya kamata a siyawa amarya ki siya, ki zaɓi abinda kike so dan iya yau kawai kike de ita, Gobe zaki tare a gidan mijin ki!.” Wani irin yarrrr Nayla taji jin kalaman Abiy da kuma kalmar mijinta da ya faɗa, ta ɗago ta kalle shi idonta ya ciki da hawaye, Abiy ya ɗauke kai daga kallon ta.
Mijinta? Wanne irin mijinta kuma ake zance?. Ko dai Abiy ya zaɓa mata miji a cikin masu neman aurenta ne kamar yadda ya ce?. Abiy ya katseta ya ce, “ki tashi kije kasuwa.” Mama ta ce, “Abiy siyayya bazata yu a iya yau ba, don Allah ka janye kalaman ka mu zauna a tattauna tukunna. Wannan wanne irin hukunci ne lokaci ɗaya?.” Ya kalli Mama ya ce, “bazan lamunci matar aure ta cigaba da zama a gidana da auren wani a kanta ba.”
“Amma Abiy abin yayi kusa, ko sanar da ita ba a yi ba, bata san abinda ya faru ba ka dinga zancen tariya gobe? Wacce irin tariya ce wannan? Wanne irin aure ne wannan?. Babu wanda ya san an yi a dangi, kuma kawai sai a ɗauketa akai Kano?.”
Abiy ya ce, “Haka nayi niya haka kuma nayi ra’ayi, ita ta zaɓi mijin ita zata zauna dashi ba mutane ba, dan haka ban ga amfanin sanar da mutane biki ko wani abun ba. Taje ta zauna da zaɓinta shine kawai.” Mama ta ce, “amma iya yau ya yi kaɗan a siyayya, ko dan siyayyar ka ƙara mana lokaci don Allah.” Bai ce komai ba yaja kujerar dining ɗin da yake kai yayi baya ya tashi ya hau shiga ɗaki bai sake kallon kowa a cikin su ba.
Nayla dai ta daskare a wajan, wai me hakan yake nufi kenan? Kayan ɗakin wa Abiy yake nufi za a siyo?. Muryar Yaya taji a bayanta ya finciki hannunta ta miƙe tsaye ya ce, “kin cuci rayuwarki, kin lalata rayuwarki, kin ɓata rayuwarki Nayla. Abinda ki ka yi ba kowa kika cuta ba sai kanki, na tabbatar Umma da take kwance a kabari baza tayi alfahari dake akan abinda kike aikata ba.”
Nayla da take a firgice ta ce, “Yaya me ya faru? Me na aikata haka?.” A fusace ya ce, “au baki san abinda ya faru ba? Na ce baki ana abinda kika aikata ba ko!?.” Nayla tana hawaye ta ce, “ban sani ba, wallahi ban sani ba. Ku sanar dani abinda na aikata don girman Allah.”
Yaya ya ɗauketa da mari cike da baƙin cikin da yake ji a zuciyarsa, Nayla ta fashe da kuka mai sauti, ya ce, “in kika sake furta baki sani ba wallahi sai fasa miki baki, ba dai kin zaɓi ɗan daba akan mu ba? Kin yi daidai ai Nayla. Kin ji daɗi kin fusata zuciyar mahaifinmu, to wallahi bara kiji, duk abinda ya faru a tsakaninki dashi kar ki nemi kowa ki yi kuka da kanki, tunda har kin iya tattara kaya ki bar gida saboda ke ga ƴar soyayya ko?.”
Nayla ta kalli Mama tana kuka ta ce, “Mama me nayi? Mama me na aikata ne haka?. Me su Yaya suke faɗa wanda bana fahimta ba?.” Mama ta bita da harara ta ce, “Nayla kinfi kowa sanin abinda kika yi, kin aikata abinda ya saka ran mahaifinki ɓaci, kin kuma san Abiy bai iya ɓacin rai ba. Sai kije ki shirya kizo mu je ki zaɓi abinda zaki zaɓa, kina ji ya ce gobe ne tarewarki.”
“Tarewata, tarewata kuma Mama? Tare ta a ina kenan?” Ta faɗa cikin fitar hankali tana kallon Mama. Jawad ya ce, “a gidan wanda kika zaɓa mana Nayla, a gidan wanda kika ce shine rayuwarki. Yanzu maganar da nake miki ke matar Omar ɗan daba ce, Abiy yaje har Kano da kansa ya ɗaura miki aure dashi tunda abinda kike so kenan” yana faɗa yaja tsaki ya bar falon, Yaya ma ya fita dan in ya cigaba da zama da Nayla sai ya ɓalla ta.
Wani irin yuuuu Nayla take ji a tsakiyar kanta kamar zata kifa, jiri ne yake ɗaukarta daga tsaye hakan ya saka ta saurin zama ta dafe kai da hannayenta duka biyu, kalaman Jawad suna yi mata amsa kuwa a cikin kunne ta. Aure fa ya ce, an ɗaura auren mata da Omar, abinda taji daidai ne ko kuma dai ba daidai bane, da gaske ne ko wasa yake yi mata?. Sai kuma ta firgita ta kalli Mama ta ce, “Mama da gaske abinda Ya J ya faɗa? Da gaske ne wai ko mafarki nake yi.”
“Da gaske ne, yanzu ke matar Omaar ce Nayla. Jiya mahaifinki yaje Kano ya ɗaura miki aure dashi.” Baya tayi zata kifa Allah ya taimaka ta dafa kujera. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Mama meyasa Abiy yayi haka? Meyasa?. Mama dan na tafi Kano? Mama ba ke kika ce min na tafi Kano ba?” Ta faɗa a gigice tana kallonta.
Mama ta ce, “ba a kan zuwan ki Kano yake magana ba, bai yanke wannan hukuncin dan kinje Kano ba Nayla, yana da dalili mai ƙarfi wanda ni ban san dashi ba.” A guje Nayla ta nufi apartment ɗin Abiy dan yadda take jin zuciyarta kamar zata fito dole tayi magana dashi. Mama ta rufa mata baya zuwa ɗakin ta same ta a lokacin da take shiga ta zube akan tiles a gabansa.
“Abiy! Abiy don Allah, don Allah Abiy!” Abinda yake furtawa kenan ta haɗe hannayenta waje ɗaya tana kuka sosai. Abiy da ya kalle ta sai ya miƙe ya ɗauko sadakinta ya buɗe hannayenta da ta haɗe waje ɗaya ya saka mata ya ce, “Sadakin ki na auren masoyinki, kije ki fara shiri gobe zaki tare a gidan sa.” Jin kalaman take yi tamkar saukar aradu, ta saki kuɗin a ƙasa ta riƙe hannun Abiy ta ce, “Abiy don Allah kace wasa kake yi min, Abiy dan na je Kano ka yanke min wannan hukuncin?. Mama…Mam….tasan zan je Kano…” ta juya tana kallon Mama ta ce, “Mama…baki san zanje Kano ba? Ba ke kika ce min na je Kano ba?. Meyasa ki baki faɗawa Abiy ba har ya yi fushi da ni?.”
Mam ta ce, “ni nace ki je Kano Nayla? Yaushe mu ka yi haka dake?. Ke kin san ban taɓa baki umarnin zuwa Kano ba, Abiy ne yake yanke hukuncin lokacin da zaki je da lokacin da zaki dawo, ni na taɓa cewa tafi Kano ki dawo rana kaza Nayla?. Ban taɓa ba, kawai kin shiga ruɗani ne kike tunanin nace miki kije amma bamu yi haka dake ba.” Nayla sakin baki tayi tana kallon Mama jin kalaman da take faɗa ta ce, “Mama ta ya zan shiga ruɗani akan wannan? Wallahi….” Cikin tsawa Abiy ya ce, “Nayla ki tashi ki bar min ɗaki! kije can ki zauna da wanda kika zaɓa, mu da zaki iya barin mu saboda shi ki barmu kije kiyi zaman ki dashi tunda shine zaɓinki. Ki tashi ki fita kafin na saɓa miki!.”
Nayla kuka take yi kamar ranta zai fita magana take so tayi amma ta kasa bakin ta rawa yake yi sosai, jikinta rawa yake yi cikin tashin hankali. Maganar ta maƙale ta kasa furta komai, so take ta kare kanta a wajan Abiy amma ta kasa sai rawar jiki da rawar baki. Abiy kukan ta yake ji har zuciyarsa, baya so ya bata wata gaɓa da zai ji tausayinta, hakan ya saka ya ce, “ki fita na ce!” Jin yadda yayi maganar bata san ta miƙe ba sai ganin ta tayi a bakin ƙofar ɗakin jiki na rawa.[24/09, 3:38 pm] +234 906 075 3382: KRB2P023
ArewaBooks@nanahaleema11
Nayla tana fita daga ɗakin Abiy Mama ta ƙarasa wajansa ta ce, "kayi haƙuri ka sassauta wannan ɓacin ran don Allah. Nayla bata kyauta ba na sani, abinda tayi sam bai kamata ba, taci amanar kauna da soyayyar da ka nuna mata, na tabbatar ko mahaifiyarta da take kabari baza taji daɗin wannan abun da Nayla tayi ba. Da me aka rageta dashi a gidan nan? Da ci ko sha ko suttura?Amma ta rasa da abinda zata saka maka sai wannan abun?. Na san dole zaka ji babu daɗi a zuciyarka, amma ka yi haƙuri ka kwantar da hankalin ka komai zai wuce in sha Allah."
Kalaman Mama sake hura wutar ɓacin rai suke yi a zuciyar Abiy, gasgata maganarta yake yi dan tabbas Nayla bata yi masa halacci ba, tunda mahaifiyarta ta rasu bai taɓa bari tayi kukan rashin uwa ba amma da haka zata yi masa sakayya. Tabbas bata kyauta masa ba, ta cutar dashi ta kuma cutar da rayuwarta.