Sashe 18
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajja tayi dariya ta ce, "Omar kenan, Omar mazan fama, Omar carbin ƙwai, ya ci sunan nasa damisa kamar yadda ake faɗa masa." Didi ta ce, "wallahi na rasa abinda zan yi, ga makullin ya aiko min dashi amma na masa faɗawa Omar saboda saƙon Baba. Shiyasa nazo na same ki don Allah ki kira shi ki ce masa kece kika ɗauki nauyin abinda Baba zai yi, yana ganin girmanki sosai, ke kaɗai ce kaf duniya zan ce kin yi bazai musa ba, duk da zai yi magana amma ƙarama ce shikenan ya wuce. In na ce Baba Adamu ne ranar sai kowa ji kan mu dashi."
Hajja ta ce, "shikenan kin kawo dabara. Ki bawa kawun na ki makullin ni ki turo min shi in anjima. Kar ki damu ai an wuce wannan matsalar." Didi tayi murmushi ta ce, "Na gode Hajja. Kin kasancewa uwa a gare ni kuma kakata, bani da mai share min hawaye a duniya sai ke ɗin kawai. Allah ya shirya miki zuri'arki gaba da baya." Hajja ta yi murmushi ta ce, "Amin. Aisha ai an zama ɗaya kar ki damu." Didi tana ta murmushi suka ɗan cigaba da hira kafin ta tashi ta koma gida.
Washe gari da safe take sanar masa da Hajja na son ganinsa, ya ɗan yi jimm yana kallon ta kafin ya ce, "lafiya take son ganina?." Didi ta ce, "Omar
ya za a yi na sani? Ta ce min kawai na ce kaje." Ya ɗan ɗauke ido daga kallon ta ya ce, "to in na fita yanzu zan shiga." Bata sake kula shi ba kar tayi magana ya gano sai tayi shiru ta cigaba da aikin ta.
Kamar yadda ya ce da ya fita kam gidan Hajjan ya shiga da sallama, mai aikin Hajja ta amsa ta ce ya shiga ciki Hajjan tana ciki. Hajja ita kaɗai a zaune tana lazumi, ta amsa sallamar ya zauna sai ta ajjiye carbin suka gaisa ta ce, "Ummaru daman na ce kazo ne akan batun kayan ɗakin Aisha na aure. Na karɓi makullin gidan da Aisha zata zauna a hannunta, ni nake so nayi mata komai na ɗaki a matsayina na uwa a gare ku. Shiyasa na ce ta turo min kai na faɗa maka da kaina kar ka ji hakan a bakin ta bai maka daɗi ba."
"Ina kallon ku matsayin jikokina ne, Aisha ta ɗauke ni kamar uwa tana faɗa min duk damuwarta. Ana zaman mutunci da amana shiyasa zan sauke haƙƙin da yake kaina matsayin uwa a gare ta. Ina fatan hakan bazai ɓata maka rai ba." Shiru ya yi bai amsa ba Hajja ta ce, "Ummaru baka ce komai ba." Ya kalle ta ya ce, "babu abinda zan ce, tunda an yanke hukunci shikenan." Hajja tayi dariya kaɗan ta ce, "an yanke kam, sanar da kai yanzu ma nayi ba neman shawara ba."
"Shikenan, an gode Allah ya saka da alkhari" ya furta a kasalance dan bai ji daɗi ba. Hajja tana lura da yanayinsa tana girmama ƙarfin hali irin na Omar, da gaskiyar Aisha da ta faɗa masa asalin su waye suka yi da babu zaman lafiya.
Sallama ya yi mata ya fita ya koma wajan Didi ya shiga har cikin ɗakinta ya samu tana mopping a lokacin. Kallon sama da ƙasa ya yi ya ce, "Daman abinda aka tsara kenan shiyasa baki faɗa min dalilin kiran ba?." Didi ta ce, "Shiyasa na ce ta faɗa maka da kanta."
"Ai wallahi tunda naga kin kasa kallona kafin na fita na san akwai munafurcin da kika haɗa, da farko nayi tunanin akan waɗancan makiran ne ashe sabuwar gulma ki ka samo hanyar ƙullawa." Didi tana jinsa bata ce komai ba sai ma dariya da yake so ya bata.
Omar ya fusata ya ce, "Ni fa bana son shishshigi a cikin lamarin rayuwata, an ce mata bani da kuɗi da zan iya yi miki ne da za a yi miki a waje?. Ba dangin iya babu na baba a ce itace tayi miki kayan ɗakin auren ki haka daidai ne?. Salon nan gaba azo na yi min gori ace kayan ɗakin Yayata ma maƙota ne suka yi mata saboda na gaza?."
Didi ta kalle shi ta ce, "Omar kyautatawa ce fa ba wani abu ba." A fusace ya ce, "Allah ya tsinewa kyautatawar!." Didi ta yi shiru jin abinda ya ce. A kausashe ya ce, "in kyautatawar ce a yi ta wani ɓangare mana lallai sai ta kayan ɗaki? Yanzu kaf unguwar nan sai a san itace tayi ko dan a faɗa, ni kuma a cigaba da yi min kallon mara amfani tunda ni Allah ya ɗorawa yi miki ba wasu a waje ba."
Shiru tayi masa bata tanka ba kar ta tanka ta sake tsokano shi, ta san halin kayanta tsaf shiyasa take gujewa abinda zata sake tunzura shi. Shirun da tayi ma bai saka ya yi shiru ba ya ce, "wai komai na kayan ɗaki ita zata yi ko a matsayin ta na wa oho?. Nuna min ake yi ni bani da kuɗin da zan yi kenan? ko ke kika ce mata bani da kuɗin da zan yi miki ita tayi miki?."
Didi a sanyaye ta ce, "ni bamu yi haka da ita ba, abinda ta faɗa maka shi ta faɗa min." Omar ya yi ƙaramin tsaki yana binta da harara ya ce, "To meyasa baki ce mata zan miki ba? Meyasa kika amince har ki ka ce ta faɗa min da kanta?. Kenan kina tunanin bazan iya ba ko?." Didi ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Nidai ban ce ba."
"Mtsw! Na rantse da Allah ba dan Ina ganin girmanta baza'a karɓi kayan nan ba, to babu yadda zan yi mata ne amma da sai ta bar kayanta ai ba roƙa muka yi ba." Shiru Didi ta sake yi masa ta cigaba da aikin ta bata ce komai ba ya sake yin tsaki ya ce, "Abin haushi." Ita dai bata ce masa komai ba tana mamaki hali irin na Omar a zuciyarta, tabbas da ace ya san Baba Adamu ne ya yi ba Hajja ba da sai an yi yaƙin duniya na uku saboda bala'i da masifar da zai dinga zazzagawa kowa.
Juyawa ya yi ya fita ta bishi da kallo ta ce, "Na kuɓuta. Alhaji Omar manya, Allah ya shirya ka ya taimake ka a rayuwarka" ta faɗa tana cigaba da aikinta tana dariya da tunanin irin kalar tizajarar da zai yi mata in ya san asalin su waye zasu yi kayan ɗakin.
Haka ya wuni rai a ɓace, ko kula ta ma bai yi saboda baya son maganar, gani yake kamar an raina masa hankali ne da za a ce wata a waje ce zata yi kayan ɗakin yayarsa ba shi ba. Ita kuma tana sane ta share shi, tana yin magana zai sake yin sama ƙarshe ma ya ce zai je ya samu hajja ya ce gaskiya bai yarda ba shiyasa ta yi masa banza.
Washe gari ƙarfe bawai na safe ta buga masa ƙofa, da yake bacci yake yi a lokacin sai ya taso yana cewa, "Didi kin san ƙofar a buɗe take amma sai ki ta buga min ƙofa kin san na tsani a buga min ƙofa amma sai kin yi, lafiya?." Didi ta ce, "na san a buɗe take ai, shigowa ne bazan yi ba. Ka tashi ka yi wanka ƙarfe takwas zamu wuce." Ya kalle ta ya ce, "Zuwa Ina?." Harararsa ta yi ta ce, "ban sani ba, ka koma ka kwanta in ka manta" ta faɗa tana wucewa ta ƙyale shi. Ƙaramin tsaki ya yi, dan kawai ya san mahimmacin alkhairi ne da bazai je ba wallahi.
Wanka ya yi ya shirya cikin ƙananun kaya a lokacin Didi ta fito daga falo shi kuma ya fito ta kalle shi ta ce, "Omar don girman Allah ka koma ka saka manyan kaya, ba dan ni ba, don Allah ka saka manyan kaya har hula ka saka." Bata barshi yayi magana ba ta dinga magiya dole ya koma tunda ba son magiya yake yi ba, ba jimawa ya dawo da shadda kalar blue mai haske har hula ya saka kamar yadda ta ce.
Murmushi tayi tana kallon sa ta ce, "Ko kai fa. Ka ci abinci sai mu wuce." Shayi kawai ya sha aka kawowa Didi saƙon gurasar da ta bayar ayi, duk yana kallo ta juye a babban bokitin roba sabo dal da ta siya. Kallon sa ta yi ta ce, "ranka ya daɗe in in ka gama sai mu tafi ko?."
"Ki jira na je na samo mai motar da zai kai mu ko?."
"Ai da driver Hajja zamu tafi." A kaikaice ya kalle ta ya ce, "Hajja dai?." Didi ta ce, "eh Omar, ita tace zata saka ya kaimu bazan ce mata a'a ba."
"Daman ai komai baza ki iya ce mata a'a ba tunda ga wacce ta haife ki, wallahi da na san haka ne bazan je ba."
"Shiyasa ban faɗa maka ba, mu je" ta faɗa tana fita ta bar shi kar tayi wani abun ya ce ya fasa.
Ransa a ɓace ya fito zuwa ƙofar gidan ya kulle gidan ya tarar da driver Hajja ya fito da motar ga Salma a tsaye a jikin motar da alama tare zasu je. Ƙaramin tsaki ya yi lokacin su Bashir suka zo wajan ya tsaya yana yi musu magana, Didi ta shiga motar shima bai jima ba ya ƙaraso ya shiga gaba su kuma daman baya suka shiga, motar ya yiwa key bayan sun gaisa da Omar da Didi suka ɗauki hanyar Kaduna ransa duk a ɓace.
[22/09, 6:58 am] +234 906 075 3382: KRB2P0011
Arewabooks@nanahaleema11.
Sha ɗaya da mintina na safe suka shiga Kaduna, da yake gidan su Nayla ba baƙo bane a wajan driver Hajja ba ɓata lokaci suka isa har ƙkofar gidan ya tsaya yana danna horn. Didi kallon gidan ta ke yi tana girgiza kai, domin gidan yana da matuƙar girma da kyau. Duk da bashi da ƙyale-ƙyale daga waje amma kana gani ka san gidan babban mutum ne ba gidan yaro matashi ba. Ko iya masu gadin da suke zaune a gate ɗin sun kai su biyar ko wanne da uniform kalar blue a jikinsa.