← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 52

Sashe 20

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙaramin falon baƙi aka shigar dasu mai kyau madaidaici. Nayla ta kunna a.c bayan ta kunna hasken falon ta fita daga falon ita da Salma. A kitchen Salma take ce mata, "Nayla don Allah ki nutsu, sai rawar jiki ki ke yi kina bayyana feeling ɗinki a fili." Sai kawai ta rungume Salma ta fashe da kuka tana cewa, "Salma Omar ne a gidan mu, Omar ne a zaune shaida Abina suna magana. Salma na kasa tantance adadin farin cikin da nake ji, ji nake kamar zuciyata zata buga saboda murna Salma. Omar ɗina yana nan lafiya, Allah na gode maka, Allah na gode maka" ta faɗa cikin kuka sosai.

Salma ta ce, "to ki yi haƙuri ki bar kuka mu kai musu abincin in ya so sai mu yi magana." Nayla ta ɗago daga jikin Salma tana share hawaye ta ce, "Salma ki yi addu'a Allah kar ya ɗora miki soyayya irin wacce ya ɗora min, akwai azaba ba kaɗan ba Salma. Na kasa yin lafiya cikin kwanakin nan kuma duk saboda tunaninsa." Tausayi ta bawa Salma matuƙa, idon Salma ya kawo ruwa amma bata yi kuka ba ta daure ta yi mata shiru bata tanka mata ba.

A haka suka zuba abincin a flaks, doya ce da ƙwai da sauce sai dankalin turawa soyayaye da kuma soyayyen ƙwai. Ga farfesun naman rago da aka yi shi mai ruwa, sai shayi da manyan slice bread da gwangwanin madara da na milo da sugar.

A kan table suka ajjiye sannan Salma ta koma ta kawo ruwa da lemo masu shegen sanyi ta ajjiye. Didi ta kalli Nayla da take tsaye kana ganin ta ka san tayi kuka ta ce, "Nayla jikin ne?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "A'a Didi, kaina ne yake ciwo shiyasa."
"Sannu, Allah ya ƙara lafiya. Ki je asibiti a duba ki." Kai kawai ta ɗaga dan ƙirjinta ya yi mata mugun nauyi, ga Omar dai tana kallonsa amma kewarsa take ji kamar ta je ta rungume shi haka take ji.

Shi kuwa Omar yana jin su amma baya ɗagowa waya yake dubawa ba tare da yana yin wani abun a wayar ba. Fitar Salma da Nayla ya saka Didi ta ce, "kai kuwa Omar ko sannu ai ka ce mata ko? Itace silar fitowar ka daga hannun Sen na faɗa maka. Ko ya jiki ai ya kamata ka ce mata zata ji daɗi." Shiru ya yi bai ce komai ba, gabaɗaya a takure yake jin kansa cikin jin nauyi wanda bai san dalilin faɗuwar hakan ba.
Salma da Nayla sun jima basu dawo ba har kusan mintina talatin kafin su dawo, Didi ce kawai ta sha tea amma shi ruwa kaɗai ya sha bayan nan bai sake ɗaukar komai ba.

Nayla ta kalli Didi ta ce, "Didi har kin ci?." Didi ta ce, "na sha tea Nayla, in zan yi tafiya bana son cin abinci wallahi." Nayla tayi murmushi tana satar kallon Omar da ya ajjiye ruwan da ya sha a lokacin.
"Yaushe zaki zo mana Kano?." Nayla ta kalli Didi ta ce, "ai sai bikinki, aiki ya saka ni a gaba ya hana ni zuwa ko ina. Ni dana sanin ma fara aikin nake yi wallahi."

Didi tayi dariya ta ce, "Allah ya kaimu, ya taimaka miki." Ta amsa da amin wajan ya yi shiru babu mai magana. Didi ce ta sake cewa, "Salma an kaiwa driver abincin?." Salma ta ce, "na tabbatar ma ya cinye yanzu." Didi ta yi murmushi suka sake yin shiru. Ƙarar wayar Nayla ce ta katse shiru ta kalla ta ga Abbas ne ta kalli Salma ta ce, "Yayanki ne." Salma tayi dariya ta ce, "yayan mu dai, kema ai yayanki ne. Baza ki ɗauka ba?." Nayla ta ce, "ana babbakar giwa waye zai je ƙaure zomo?."

Salma ta murmusa cikin tausayin ƴar uwarta ta ce, "Gaskiya ne." Didi ta kalli Nayla ta ce, "Nayla zan shiga banɗaki." Salma ta ce, "mu je na raka ki." Didi ta miƙe ta fita ita da Salma aka bar Omar kawai da Nayla a zaune. Wani irin yarrr Nayla take ji a jikinta, gashi dai kamar bai san tana zaune ba amma wani irin suka zuciyar take yi ga farin ciki da yake mamaye zuciyarta. Ganin ba ita yake kallo ba kawai sai ta zuba masa ido tana kallon sa cikin shauƙi ko ƙifta ido bata yi.

Waya ta ɗauka kamar tana dubawa tana yi masa video ta yadda bazai fahimta ba. Omar kuwa shi kansa wani iri yake ji, ya na kallon su har fitar su Didi ya kuma san tana zaune ita a falon. Wani iri yake ji a jikinsa kamar taɓa zama da mace shi da ita kawai ba. Duk da dai akan Narma kawai ya faru amma sai yake jin wannan daban kamar bai taɓa shiga irin yanayin da yake ji ba.

Hannunsa ta kalla ta kuwa yi farin gani, domin azurfar da ta bashi tana sanye a ɗan yatsansa na biyun ƙarshe a hannun haggu. "Wayyo Allah!." Ta furta bata san ta ce ba saboda farin cikin da ya sake mamayeta. Jin abinda ta furta sai ya ɗago ido yana kallonta a lokacin ta rufe ido ita kuma saboda tsananin farin ciki. Ɗauke kai ya yi ita kuma ta buɗe ido, gabaɗaya ta kasa sarrafa kanta ƙiris take jira ta fita daga hankalinta

Didi da Salma ne suka dawo Didi ta kalle ta ganin sai murmushi take yi ita kaɗai sai ta kalle shi taga babu alamun ma sun yi magana da ta san hali. Mamakin murmushin Nayla take yi saboda ta san tsoron Omar take ji, amma yanzu gashi an bar su su biyu tana ta murmushi mai kyau.

Nayla ta kalle ta ta ce, "Didi mu je ɗakina ki kwanta ki huta." Didi tayi dariya ta ce, "Sallar azahar kawai zamu yi mu juya, kwanciyar me zanyi gashi har sha biyu da rabi tayi?." Nayla ta ce, "kai Didi, ni na ɗauka sai yamma."
"Gwara mu shiga Kano kafin duhu ya yi Nayla." Nayla ta girgiza kai tana ta murmushi abin ta kamar sabon kamu. Omar dai baya magana Didi sai girmama hali irin na sa take yi, yazo har gidan su yarinya amma ya kasa ce mata ya jiki bayan a gabansa aka ce bata da lafiya.

Salma ta ce, "Didi mu je ɗakin Nayla ki yi alwala ki yi sallah." Didi ta amsa da to Nayla dai bata son tafita amma haka ta miƙe a lokacin Jawad ya shigo ya zauna yana ɗan jan Omar da hira duk da bai sake ba. Nayla bata so barin wajan ba, haka suka shiga babban falon suka hau sama har ɗakin Nayla.

Didi girmama gata irin na Nayla take yi, musamman yadda Abiy ya ruɗe akan ciwon ta ga kuma girman ɗaki kamar baza tayi aure ba. A nan suka yi sallar azahar suna ta hira da Didi, duk da ta lura Nayla bata cikin walwala dawowar su ɗakin amma bata tambaya ba.

Bayan an idar da sallama suka sakko suka haɗu sa Mama ta bawa Didi kaya a leda sannan ta bata kuɗi ta ce in ji Abiy ya ce su yi kuɗin mai. Ta dinga yi mata godiya sosai, Nayla ta riƙe mata kayan ita da Salma suka fito har bakin motar.

A tsaye suka tarar da Omar shida driver da alama su suke jira. Didi ta buɗe motar sannan ta kalli Nayla ta ce, "Nayla baƙo zai yi halin sa, Mun gode da karrmawa Allah ya bar zumunci." Nayla ido ya ciki da hawaye ta ce, "Amin Didi. Allah ya kiyaye hanya." Salma ta riƙe hannunta tace, "Nayla meye na kukan?." Sai ga hawaye shar ya sakko mata, ta juya da sauri ta rungume Didi ta ce, "bana so ku tafi Didi, don Allah ku kwana." Omar da yake jin me cewa ya kalle ta yana mamaita su kwana, Lallai ma yarinyar bata da hankali.

Didi ta ce, "Nayla banda abin ki meye na kuka kuma? Ki yi haƙuri wata ran ai zan dawo in sha Allah." Nayla ta ɗago daga jikinta ta ce, "to Didi. Wallahi bana so ku tafi, ji nake kamar na bi ku."
"Ki yi haƙuri kin ji? Ai zaki zo Kano ɗin ko?." Ta ɗaga kai kamar yarinyar ƙarama Didi ta ce, "to kin gani, ki yi haƙuri kar ki saka ni kuka nima." Nayla ta goge ido ta ce, "Allah ya sauke ku lafiya."
"Amin Nayla. Allah ya baki lafiya, ji ke ki ga likita gabaɗaya kin canja kin rame kamar ba ke ba."

Nayla ta ce, "to Didi zan je in sha Allah." Didi ta shiga mota Salma ta riƙe Nayla ta ce, "ki yi haƙuri ki ta addu'a, canji zai zo daga wajan Allah."
"Ina yi Salma, kema ki dinga yi min."
"Ina yi miki kullum Nayla, Allah ya sassauta miki. Ba dan ban cewa Daddy zan kwana ba ai da nayi zamana na ɗebe miki kewa. Amma zan dawo." Ta ɗaga kai kawai tana kallo Salma ta shiga motar.

Kallon inda Omar yake tayi suka haɗa ido dan kallon ta ya ke yi yana tunanin meyasa yake yawan ganinta tana kuka, shagwaɓa ce ko sangarta ko rashin hankali?. Ganin sun haɗa ido sai tayi murmushi idonta duk hawaye ta ce, "Allah ya kiyaye hanya….Yaya Omar!.." Wani iri yaji a zuciyarsa, mace ta farko da ta taɓa ce masa Yaya kenan a rayuwarsa. Sai yaji wani irin rauni da bugun zuciya, har lokacin kallon ta yake yi hawaye suna sakko mata daga idonta.

Samun kansa ya yi da yin murmushi ya ɗaga kai ya ce, "Amin, Mun gode" daga haka ya buɗe motar ya shiga. Ai Nayla suman tsaye tayi a wajan saboda gigicewa. Na farko murmushin da ya yi mata, na biyu maganar da ya yi, na uku godiyar da ya yi mata sai take ji kamar an yi mata babban albishir.

Horn ɗin motar ne ya saka ta dawo hankalinta, ta share hawaye tana dariya tana kuka ta ɗaga musu hannu suka fita daga gidan ita kuma ta juya a sanyaye ta koma cikin gida.
[22/09, 3:26 pm] +234 906 075 3382: KRB2P012
Arewabooks@nanahaleema11.
Chapter 20 · 0% Book details