Sashe 50
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dad ya yi murmushi ya ce, "in dai wannan ne babu abin damuwa a nan, na tabbatar faɗar Narma ce babu wani rape, ki manta kawai."
"Na gani da idona ka ce babu wani rape? Ni gabaɗaya aurenta dashi ya fara fitar min daga rai wallahi, bata samun farin cikin da muka so ta samu a gidan."
Dad ya ce, "zan kira Ashraf ɗin naji abinda yake faruwa." Mum ta ce, "ya dai kamata gaskiya, zuwan mu baka ga yadda ta sake ana yawo ba. Amma lokacin da mu je tana ɗaki a kwance shi kuma yana falo. Meye hakan yake nufi? Ni kar ya ɗorawa yarinyata ciwo fa."
Dad ya ce, "gaskiya akwai damuwa, amma ki bari zamu bi komai a hankali mu gani. Zan kira shi na ji in da matsala sai ya dawo da ita nan ayi bikin kawai a huta, sai ta zauna a nan Abuja yadda zamu dinga ganinta ko yaushe." Mum ta ce, "da dai ya fi gaskiya" ta faɗa tana kawar da kai gefe dan gabaɗaya zaman Narma da Ashraf ya fita daga zuciyarta.
•••••••
Kafin sallar juma'a suka shiga Kano, kai tsaye gidan Hajja aka wuce kamar yadda aka ce za a yi. Ana ajjiye motar suka fita zuwa cikin gidan Mama na riƙe da hannun Nayla, fuskarta a buɗe dan mayafin ma ya dawo kafaɗa dan bata da nutsuwa. Gidan cike da mutane suka tarar dashi, matan su da Daddy da ƴan uwa duk dai dangin mahaifiyar Nayla suna gidan.
Nayla na shiga ta ƙarasa wajan Hajja ta zube a kan guiwarta ta ɗora kanta a jikin Hajja bata ce komai ba. Hajja ta dafa kanta ta ce, "Sannun ku da ƙarasowa Hauwa'u." Ta kalli Mama ta ce, "Zeenatu barka da hanya." Da fara'a Mama ta gaishe da kowa na wajan suka amsa mata da murmushi dan tana burge su bata da matsala ko kaɗan.
Mama ta ce, "To Hajja ga Nayla nan dai Abiy ya saka mun kawo ta, sai haƙuri da yadda abin yazo gabaɗayam mu bamu yi tunanin hakan zai faru ba." Hajja ta murmusa ta ce, "ƙaddarar kenan ai, baka sanin ta inda zata zo ba balle ka yi ƙoƙarin kiyayewa kafin zuwanta. Babu komai, in sha Allah alkhairi ne."
Mama Sa'adatu ta dafa Nayla ta ce, "Nayla sannu, jikinki akwai zafi, kanki na ciwo?." Nayla ta ɗaga kai alamun eh, Salma ta ce, "Mama ba dole tayi rashin lafiya ba, kullum cikin damuwa da kuka take. Yanzu ma tunda muka taho ko ƙala bata ce ba, sai dai tayi hawaye ta gaji ta daina." Mama Sa'adatu ta ce, "ki yi haƙuri Nayla, duk ɗan adam baya tsallake ƙaddararsa kin ji ko?."
Bata ce komai ba ko motsawa ma bata yi ba, tana jikin Hajja da take shafa kanta a hankali cikin shigar rarrashi. Lokacin sallah da ya yi ne ya tashe su gabaɗaya, akayi alwala aka yi sallah sannan aka ci abinci. A lokacin Jawad da Ahmad suka shigo suka gaisa da mutanen gidan kafin su shiga mota su tafi.
Nayla na zaune a ɗakin da take kwana tayi tagumi, Mama Sa'adatu ce ta shiga ta cire mata tagumin ta zauna kusa da ita ta riƙe hannunta ta ce, "Ki daina tagumi kin ji ko?." Nayla ta ɗaga mata kai kafin ta ce, "yanzu me ki ke so?."
"Babu komai Mama."
"Ki faɗa min in akwai abinda ki ke so na kawo miki."
"Babu Mama."
"Kin sha maganin ciwon kan?." Ta ɗaga Kai alamun eh ta ce, "to ki kwanta ki yi bacci zaki ji daɗi."
Nayla ta ce, "bazan iya baccin ba." Mama ta ce, "to me za ki yi?."
"Nima ban sani ba" ta faɗa murya na rawa alamun zata cigaba da kuka. Mama ta ce, "kar ki yi kuka mana, ni kukan ne bana so na gani." Nayla ta ce, "Abiy yana fushi dani Mama."
"Kar ki damu komai zai wuce. Ba dai kina son mijin na ki ba?." Nayla ta sunkuyar da kai ta ƙasa bata amsa ba. Mama ta ce, "Nayla ni ƙanwar mahaifiyarki ce, baki da wata uwa kamar ni. Ki faɗa min abinda yake ranki kar ki ji kunya, kina son mijin ko?."
Nayla ta ce, "Mama da dai nasan ina sonsa, amma yanzu tunda ake kiransa da mijina na kasa tantancewa." Mama ta ce, "zaki tantance sai a hankali, yanzu ma ruɗani da yadda abin yazo bazata shine ya saka ki ke jin hakan. Amma kar ki damu komai zai zo ya wuce ya zama tarihi. Abiy ba ya fushi dake, ki kwantar da hankalinki."
"Fushi yake yi Mama, tunda na furta Ina son sahikenan ya canja. Mama Abiy ne yake cewa kar na je gida sai ya ce na je, in ba fushi ya yi dani ba meye?. Mama daga zuwana Kano na koma na ji labarin wai ya aura min shi."
Mama ta ce, "to ke waye ya ce ki zo Kano baki tambaye shi ba?." Nayla ta ce, "Mama ce. Mama ce tazo zan fi samun nutsuwa a nan, itace ta saka aka kawo ni amma ni ban yi niya ba." Shiru tayi tana kallon Nayla kafin ta ce, "ita ta san kina son Omar ɗin ne?." Gaban Nayla ya faɗi, indai aka ambaci sunansa sai gabanta ya faɗi matuka. A hankali ta ce, "ta sani, itace ta ke bani goyan baya akan shi. Dan koda Abiy ya ce na manta dashi tana cemin kar na damu zata san ya zata yi."
Mama Sa'adatu ta yi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan dai ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce. Kuma mahaifinki baice kar ki je gida saboda yana fushi ba, yana so ki nutsu ki yi zaman aure, kar wannan ya dame ki kin ji?." Kai ta ɗaga almaun to. Mama ta tashi ta bar ɗakin zuciyarta cike da zargin wani abu akan Mamansu Jidda.
Bayan an idar da sallar juma'a mutane suka ɗan ragu a gari sai ga Mama Zaliha ƙanwar Abiy itama rarrashinta dai ta dinga yi. Gidan Hajja ya zama gidan biki domin kuwa an cika shi dam da ƴan uwa ana hira ana kuma cin abinci. Nayla da aminanta kuwa suna ɗaki tana kwance akan gado su kuma suna gefen suna aikin rarrashinta da kalamai masu daɗi.
Didi kuwa tana gida ta kasa shiga gidan Hajja, gabaɗaya kunyarsu Hajja take ji, sai ta ga kamar tana da laifi akan abinda aka yiwa Nayla. Tana zaune ya dawo daga masallacin juma'a ta ce, "Yauwa Omar, don Allah zuwa sallar magriba ka dawo saboda akwai abu mai mahimmaci da za a yi." Ya bita da kallo yana taɓe baki ya ce, "to zan duba na gani."
"Ba dubawa zaka yi ba, yi zaka yi don Allah."
"To" ya furta dan shima ta saka shi a tunanin abinda zai farun nan.
Fita ya yi ita kuma ta zauna tana hasaso abinda zai faru, idanunta kallo mata Omar suke yi yana tijara da rashin mutunci a gaban mutane. A bayyane ta ce, "in sha Allah bazai yi ba, zai nutsu ya saurare abinda za a ce masa in sha Allah."
Da yamma Mama Zaliha ta tafi gida sauran matan su Daddy ma sun tafi ya rage Mama Sa'adatu ce kawai su Jidda da Jalila da kuma Mamansu Jidda.
Mama Sa'adatu ta ce, "Ina Aisha ne? Ya kamata ta shigo ta bamu key mu je mu ga inda Nayla zata zauna ko Maman Jidda?" Ta faɗa tana kallon Mama. Mama ta ce, "gaskiya ne, nima a waya na dinga ganin gidan da ana shiryawa, ya kamata muje kam." Mama Sa'adatu ta ce, "bara a kirata, sai mu je mu dawo tunda an ce babu nisa."
Salma aka tura aka ce taje ta karɓo key ɗin, ta shiga ta samu Didin duk tayi tsuru-tsuru kamar mara gaskiya. Salma ta ce, "Hajiya Didi lafiya ki ke kuwa?." Ta yi murmushin yaƙe ta ce, "Lafiya lau Salma, Ya taro?."
"Alhamdu lillah. Su Mama ne suka turo ni akan ki bada key na gidan za a je a gani." Didi ta amsa a sanyaye ta ɗauko ta miƙawa Salma tare da yi mata kwance sa sannan ta ce, "Ya Nayla kuwa?."
Salma ta ce, "Tana nan a kwance."
"Bata da lafiya ko?."
"Kusan hakan gaskiya." Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "Allah ya bata Lafiya, ki gaishe ta zan shigo zuwa anjima in sha Allah." Salma ta ce, "Amin. Ni na ɗauka a gidan ma zamu zo mu same ki." Didi ta ce, "hmm Salma baza ki gane ba, ki je kawai sai na zo." Salma ta amsa mata ta fita ta kai musu key ɗin ta koma inda take zaune.
Bayan sallar magriba Omar ya dawo kamar yadda ta ce, tana ganin shigowarsa ta miƙe ta ce, "Yauwa sannu da zuwa. Ka taimaka min yadda Allah ya taimake ka kayi wanka ka canja kaya, kar kace ƙananun kaya zaka saka, don Allah ka saka manyan kaya."
Ya bita da kallo bai ce komai ba ya zauna sannan ya ce, "ni yunwa nake ji." Didi ta wuce kitchen ta kawo masa abinci ta ce, "ga abinci ka ci." Karɓa ya yi ya fara ci yana kallonta ganin gabaɗaya bata cikin nutsuwarta.
Ajjiye abincin ya yi ya kalle ta ya ce, "Didi wai me ya mayar dake haka ne? Gabaɗaya kin firgice bakya tare da nutsuwa sam. Da kin bani haushi na ce bazan sake tambayarki ba amma na kasa, meye ne don Allah?." Didi ta ce, "samun nutsuwata ka kammala mu je inda zamu je."
"Indai na je na shirya mu ka tafi zaki nutsu?." Kai ta ɗaga alamun eh ya ture abincin ya ce, "shikenan bara a yi sallar i'sha sai na shirya ɗin, bana son wannan yanayin na ki wallahi, gabaɗaya bana jin daɗi in na ganki a haka." Didi ta ce, "ka ci abincin tukunna."
"Ya fita a raina" ya faɗa yana tashi ya fita ta bishi da kallo. Hawaye taji suna sakko mata, tunaninta kawai ta ya Omar zai karɓi auren Nayla? Tuna hakan kawai faɗuwar gab yake sakata, balle ta san bakinsa da bashi da control komai ya zo bakinsa faɗa yake yi ko a gaban waye.