← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 52

Sashe 34

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta dafata cikin rarrashi da murya mai sanyi ta ce, "Kar ki damu, shima yanzu yake faɗa min da ya sani bai yi miki faɗa ba ya san ba yin kanki bane soyayya ce ta kawo hakan. Amma ki nutsu babu abinda zai faru kin ji?." Nayla ta ɗaga kai alamun to ba dan ta yarda ba. Mama ta dinga rarrashinta cikin kalamai masu daɗi har Nayla ta ɗan saki jikita kuma yarda da kalaman Mama sosai.

Haka Nayla ta kwana tana ciwon kai, da safe haka ta tashi daƙyar ta tafi aiki, da taje can ma sai da suka kai ta asibiti saboda ciwon kai ya takura mata. A asibiti ta yini aka saka mata ruwa bayan an kira gıda an faɗawa Mama. Sai yamma suka koma gida Abiy bai ce mata meye dalilin ciwonta ba ya dai yi mata sannu daga nan bai ce komai ba. Sai da daddare suna zaune gabaɗaya har su Yaya a falo tana cin abinci kamar bata so saboda har lokacin bata jin daɗin jikinta.

Yaya ne ya kalle ta da kulawa ya ce, "Nayla wai ne yake damunki ne? Gabaɗaya kin canja, bakya walwala, bakya hira, kuma kin rame. Meye a zuciyarki?." Abiy ya kalle ta sannan ya kalle shi ya ce, "Soyayya ce." Yaya ya kalli Abiy da sauri ya ce, "Abiy soyayya kuma? Wa take so?." Abiy ya sha tea ya kalle shi bayan ya ajjiye mug ɗin yana juya spoon a ciki ya ce, "Ina wani yaro da shekarun baya ya taɓa taimakon ta lokacin da za a yi raping ɗinta a Kano?."
"Wannan ɗan daban kenan, na gane shi."

Abiy ya sha tea ɗin sannan ya ce, "to shi take so. Akansa ta komai haka gabaɗaya." Jawad da ya wara idanu ya ce, "Mun shiga uku, Tiger ɗin take so Abiy?." Abiy ya ɗaga masa kai alamun eh Yaya ya kalle ta ya ce, "Nayla Tiger ki ke so?." Bata iya magana ba sai sunkuyar da kai da tayi tana juya spoon a cikin abincin ba tare da ta ci ba.

Yaya ya kalli Abiy ya ce, "Abiy kai me ka ce to?." Abiy ya kalle shi ya ce, "kaiɓa ai uba ne a wajanta, yanke naka hukuncin naji." Yaya ya ce, "Abiy ai tun wuri ta ajjiye wannan batu a zuciyarta, banda shirme da rashin hankali ta rasa wanda zata ce tana so sai wancan ɗan shaye-shayen mai kashe mutane?."

           "Wallahi baya shaye-shaye!."

A tare suka kalli Nayla jin abinda ta ce, itama sai take kallon su dan bata san abinda tayi ba ta ga dai ana kallonta. Gabanta ya yanke ya faɗi, kenan a zahiri tayi maganar tunda taga kowa kallonta yake yi har Mama da Abiy. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ta furta a sanyaye jikinta ya gama yin sanyi. Ta san halin Yayan su akwai saurin fusata yanzu sai ya gaggaura mata mari saboda wannan maganar da tayi.

Abiy yayi dariya ya ce, "to gashi nan ta baka amsa, masoyinta baya shaye-shaye." Yaya ya fusata sosai ya kai hannu kamar zai maketa sai ya fasa ya ce, "ni kike faɗawa baya shaye-shaye? Kin fini sanin sa ne!?." Sai data firgita saboda tsawar da yayi mata.

Jawad ya kalli Abiy ya ce, "No wonder ko yaushe tace zata je Kano mana, ashe shi take zuwa gani tunda maƙoncin Hajja. Ka duba ranar da suka zo gidan nan da Yayarsa, gabaɗaya Nayla ta rikice ta kasa zama, a lokacin na ɗauka murnar ganin Yayarsa ne ashe saboda shi ta fita hankalinta." Yaya ya ce, "baza ta sake zuwa Kano ba, daga yau na soke zuwan ki Kano. In kinga kinje Kano to tabbas babban abu ne da ya kamata ace kin je!" Ya faɗa da ƙarfi yana nunata da yatsa.

Yaya ya kalli Abiy yace, "Abiy ba shine wanda ka ce Senator Sagir ya kama shi a Abuja ba?."
"Shine Babana, ni tazo ta saka a gaba tana kuka tana cewa tausayin Yayarsa take ji da surutai kala-kala, ashe nima case ɗin yana nan tafe zuwa gidana."
"Ai in tayi gangancin gayyato shi gidan nan wallahi na saka anyi masa dukan da za a karshi lokaci ɗaya. Meye abin so a wannan abun don Allah? Hasken fatarsa ne ya ɗauke ki ko me?" Ya faɗa yana kallon Nayla da bata ce komai ba ko hawayen ma sun ƙafe.

Jawad ya ce, "Nayla in soyayyar ce baki wuce zuciyarki ta fara son wani ba, amma ki so wanda ya dace ya cancanta ba wannan ba. Ki ce kina son wannan ki ce kin son me don Allah? Ɗan daba mai kashe mutane ko karen yan siyasa?. Wai to shi yana sonki?." Abiy ya murmusa ya ce, "bai ma san tana yi ba Jawad." Yaya ya kalle ta cikin jin haushi da takaici ya ce, "wallahi kin bani kunya Nayla, ina Abbas, Ina Hashim, Ina sauran mutane biyun da suke sonki? Duk basu yi miki ba sai wannan mara aikin yin ne ya yi miki?."

Shiru bata tanka ba kanta na ƙasa sosai kayan jikinsu kawai take gani ban da fuska. Mama ta ce, "Yayansu ka yi mata a hankali mana, ka daina yi mata faɗa haka." Yaya ya kalli Mama ya ce, "Mama Nayla fa ba yarinya bace, tana sane duk abinda yake yi wallahi."

Yaya ya ce, "Abiy ka bani ita mu tafi Lagos, in yaso zan saka ayi mata transfer na aikinta zuwa can. Zan dawo da ita bayan na tabbatar ta bar wannan banzan tunanin."
"A'a, ka barta a nan ana gama azumin Ramadan aure zata yi. Ku fara shirin aurar da ita dan ba za a ɗauki lokaci ba."

Jawad ya ce, "shikenan an huta." Sai sake jagalgwala nmaganar suke yi ita dai Nayla bata iya ce komai ba. Ta ɗauka ma Ya J zai sassauta mata saboda shine mutuminta sai taga shima sai masifa yake yi kamar tace tana son wani ƙaton arne.

Gajiya tayi da zaman kar ta tashi ta sake yin laifi, sai da taji sun yi sanyi da maganar sannan ta miƙe ta hau sama dan ta kwanta. Bacci yaƙi zuwa idon Nayla, tana ganin kiran Salma na shigowa amma bazata iya ɗagawa ba ta kawar wayar gefe ta rasa abinda zata yi ta ji daɗi. Abin mamaki har biyu na dare idanunta biyu, sai kawai ta miƙe tayi alwala ta zo ta tayar da sallah, tana sallah tana kuka. Yadda take kuka a suujjada tana faɗawa Allah damuwarta ma abin taɓa zuciya ne. Sai gab da asuba ta fara jin bacci, ta hana idanunta bacci sai da tayi sallah sannan ta kwanta.

Sai sha biyu ba rana ta farka, bata fito ba sai da tayi wanka kasancewar alhamis ce azumi take yi baza ta fita ta karya ba. Tana nan zaune Mama ta shigo ɗakin ta bita da kallo ganin ta rame daga jiya zuwa yau, ta zauna ta ce, "Nayla kinga yadda ki ka koma kuwa?."
"Mama Ina kwana" ta faɗa tana kallon ta.
"Lafiya lau, ya ciwon kan?" Ta faɗa tana taɓa kanta. Mama ta ce, "har yanzu akwai zafi a kanki Nayla. Meyasa baza ki sassautawa kanki wannan damuwar ba?."

Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Mama ta ce, "na san kina son Omar, Allah kaɗai ya san me kike ji a zuciyarki. Kar ki damu da maganar Yayanki da mahaifinki zan san abinda zan yi."
"Mama da ace na san inda zan ajjiye son da nake masa da na ajjiye, da ace na san inda zan cire zuciyata da na cire na ajjiye Mama. Amma na kasa, nayi addu'a babu adadi amma ban taɓa jin abinda nake ji a kansa ya ragu ba Mama. Ya zan yi? Su Yaya sun kasa gane ba yin kaina bane, sai faɗa suke yi min....." ta faɗa cikin rauni.

"Ni na fahimce ki shiyasa nace Ina bayan ki a ko yaushe. Abinda nake so dake yanzu ki kwantar da hankali ki nutsu, ki tashi ki shirya kayan ki kala uku zan saka a kai ki Kano." Da sauri Nayla ta kalli Mama da mamaki ta ce, "Kano kuma Mama? Baki ji abinda Abiy da Yaya suka ce ba?."

"Na ji, duk duniya babu wanda ya san waye mahaifinki kamar ni, na san abinda zai ɓata masa rai na san abinda zai yi saurin saka shi ya bar fushi. Sannan Yayan ki abinda Abiy ya ce shi zai yi, in Abiy ya bar fushi ya amince da Omaar shikenan. Dan haka Abiy ne abin jin ba Yayanki ba."

"Mama meye amfanin zuwa Kano to?."
"Saboda ki samu nutsuwa, kuma sannan ni zan cewa Abiy saboda kin yi masa laifi ya saka ki ka tafi gidan Twiny dan ya huce. In kinje sai ki yi masa text na ban haƙuri ki turo masa,in kika kwana biyu zuwa ranar Sunday sai ki dawo shikenan." Nayla ta yi shiru tana kallon Mama kafin ta ce, "Mama anya hakan ya yi? Kar Abiy ya yi fushi dani."
"Bazai yi fushi dake ba, kar ki damu. Ki tashi ki shirya ko bakya son zuwa Kano ɗin?."

Nayla ta ce, "Ina so, amma....."
"Kar kiyi wani tunani, ki tashi ki shirya kawai na saka a kai ki. Amma ki tabbatar kin yi masa text na ban haƙuri tare da addu'a. Kuma kar ki faɗawa mutanen Kano ni na ce ki kije, sannan ko Abiy ma kar ki ce masa ni nace ki je. Abinda ya sa na ce haka in kika ce masa ni na ce ki je zai ga kamar ba ke kika yi niyar bashi haƙuri ba ni na saka ki."

Nayla tayi shiru alamun tunani Mama ta dinga rarrashi tana faɗa mata kalaman da taji a ranta zata je Kano. Nayla ta yi ajiyar zuciya ta ce, "To Mama" ta faɗa tana tashi ta haɗa kaya kamar yadda Mama ta ce ta riƙo hannunta har bakin ƙofar ɗakin sannan tace taje. Mama tana tsaye a balcony tana kallon Nayla har ta shiga mota suka wuce.
Chapter 34 · 0% Book details