Sashe 36
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayla ido ya kawo ruwa ta zubawa Salma ido ta ce, "da gaske kike yanzu Omaar ya koma yin sana'a sosai?."
"Da gaske nake wallahi, bara na nuna miki handles ɗin su da suke posting kayan. Naga didi ta saka a status, shine naje na gani ke baki ga abu ba baza ki ɗauka Omar yana da wayewar yin abubuwa haka ba" Tana faɗa tana danna waya tana duba page ɗin.
Nuna mata wayar tayi ta ce, "kin gani.. wannan shine irin takalman da Omar yake yi yanzu. Shiyasa zaman unguwar nan ma yanzu ba yi yake yi sosai ba, ko yaushe baya nan suna shago suna aiki." Nayla kalla take yi zuciyarta na rawa sosai kafin ta sauke kai ta yi ajiyar zuciya ta ce, "wataƙila babu Omar a cikin ƙaddarata."
"Calm down, ki cigaba da addu'a komai zai wuce. Kuma ba kince Mama na supporting ɗinki ba?."
"Ita kaɗai ba, Yaya cewa ya yi a bashi ni mu tafi Lagos sai na dawo hankalina na dawo gida. Yaya J ma da yake aminina shima yana bayan Abiy. Gabaɗaya jina nake wani iri wallahi."
"Ki dai yi haƙuri. Yanzu ki tashi kiyi wanka, kiyi break sai mu je gidan Didi." Nayla ta ce, "Ina so naje gidan Twiny ma."
"To ki tashi mu shirya." Nayla tayi ajiyar zuciya ta tashi ta shiga banɗaki cikin damuwa mai yawa.
Su Abiy lokacin da suka shigo Kano umartar Jawad ya yi da su wuce gidan su na Kano. Kai tsaye nan suka wuce kamar ko yaushe. Mai gadin gidan jin ana horn ya buɗe ya ƙaraso ganin mai gidan ne da kansa ya saka ya buɗe suka shiga cikin gidan. Falon gidan suka shiga bai yi dauɗa ba sai dai ƴar ƙura kaɗan mara yawa.
Abiy ya kalle su ya ce, "ku huta zuwa sha biyu da rabi zamu fita." Amsa masa suka yi ya shiga ciki. Ahmad ya kalli Jawad ya ce, "Wai me yake faruwa ne? Me muka zo yi Kano?."
"Wallahi ban sani ba Yaya, abinda na sani kawai jiya Nayla ta bar gida ta taho nan Kano. Da Fari na ɗauka gidan Hajja ɗin zamuje sai naji ya ce mu zo nan." Da mamaki Yaya ya ce, "ta bar gida ta taho nan? To Akan me?."
Jawad ya ce, "Akan wannan yaron mana, ran Abiy ya ɓaci matuƙa a jiya da daddare."
"Daman Nayla bata da hankali ban sani ba? Ana ganin ta mai kirki da hankali ashe itama ƴar iska ce?. Ta taho na saboda ance bazata aure shi ba ko me?." Jawad ya ce, "nima ta bani mamaki wallahi, ban ɗauka zata aikata haka ba. Ashe macijin sari ka noƙe ce, a haka sumi-sumi da ita kamar bazata aikata ba."
Yaya ya girgiza kai ya ce, "Lallai tana buƙatar duka, dan sai na zane mata jikinta sannan zata fahimci kuskurenta. Bara Abiy ɗin yazo, ɗauketa zan yi wallahi mu tafi lagos na koya mata hankali a can tunda ita shashasha ce" ya faɗa yana fita zuwa ɗakin da suke zama a cikin gidan.
Ba su jima sosai ba Abiy ya yi musu waya ya ce su fito, suka fito suka tarar dashi a bakin mota suka shiga kai tsaye ya ce su wuce unguwar Kundila. Can suka nufa Abiy yana basu address yadda aka faɗa masa suna tafiya sai gasu har ƙofar gidan Kawu.
A ƙofar gidan suka faka motar Abiy ya kalli gidan da aka tabbatar masa nan ne gidan Kawu. Babban gida ne mai kyau kana gani ka san mai shi yana da abin hannu sosai. Abiy ya kalli Agogo ya ce, "mu ƙarasa masallaci muyi sallah in ya so sai mu dawo." Da to suka amsa suka ƙarasa masallacin da yake kusa suka yi sallar juma'a sannan suka dawo mota.
Abiy da kansa ya tambaya aka nuna masa Kawu da yake tahowa yana amsa waya zai shiga gidan ya dawo daga masallaci. Abiy ya ƙarasa ya ce, "Assalamu alaikum." Ya dakata da wayar ya amsawa Abiy suka yi musabaha kafin Abiy ya ce, "na san baka sanni ba, baƙo ne in babu damuwa Ina so zamu tattauna." Kawu ya ce, "to bismillah shigo." Abiy ya yi musu magana alamun su shigo suka biyo bayan Abiy.
A wani babban falo ya sauke su wanda maza biyu suke a zaune ya kalli Abiy ya ce, "ƴan uwana ne, Ina fatan babu damuwa." Abiy ya ce, "babu damuwa. Na ji daɗin hakan sosai." Kawu ya ce, "Da yake yau muna ɗan ƙaramin taro, an kawo kayan lefen ƴar wajan ƙanina gashi a zaune shiyasa muke gabaɗaya" ya faɗa yana nuna masa Kawu Yusuf. Abiy ya ce, "Allah ya sanya alkhairi."
"Amin ya Allah. sai dai ban sanka ba." Abiy ya ce, "Sunana Alhaji Abdullah Ahmad, ni mazaunin garin Kaduna ne. Nazo wajanka ne akan ɗan ƙaninka Omar ƙanin Aysha." Kawu ya gyara zama ya ce, "to Allah yasa ba laifi ya yi ba." Abiy ya murmusa ya ce, "ba laifi ya yi ba, na zo ne ina nemawa ƴata aurensa a yanzu in hakan zai yu."
Duk mutane wajan mamaki ya kama su, suka bi Abiy da kallon mamaki ba tare da ya basu damar magana ba ya ce, "na san komai, kar ku tambaye ni dalili ko meyasa, ina sane duka abinda nake yi. Kawai in zai yu ina so zan bashi aurenta a yanzun nan a ɗaura auren. Tunda ku ne waliyansa ga nata waliyya a zaune" ya faɗa yana nuna su Jawad da suka yi mutuwar zaune.
Kawu ya ce, "To ai ka kulle mana baki ne, wai ka san wanne Omar ka ke magana akai kuwa?."
"Na sani, tunda kaji har nayi maka kwantacesa da Yayarsa ai ka san na sani. Ni sirikin Hajja ne maƙociyarsu."
Kawu ya ce, "ƙwarai na san Hajja, har gaisheta na taɓa shiga nayi sau biyu, kuma Ina jin labarin alkhairinta sosai a wajan Aisha." Abiy ya ce, "na auri ƴar Hajja kafin mutuwa ta raba mu, yarinyar da zan aura mata ƴata ce ta cikina kuma jikar Hajja. Amma naga kamar kuna tantama, in kuna so ku tabbatar ku kira Aisha ku tambayata ku ce ta san Nayla."
"Assalamu alaikum, Kawu ashe baƙi ne da kai bara na koma" aka faɗa daga bakin ƙofa ana ƙoƙarin komawa. Kawu ganin Didi ce sai ya ce, "Aisha shigo mana." Didi ta juyo tana takowa a hankali har tazo tsakiyar falon. Kallon Abiy tayi cikin mamaki ta ce, "Abiy! Ikon Allah kaine a nan?" Ta faɗa da fara'a tana kallon sa. Abiy ya murmusa ya ce, "ni ne Aisha."
"Barka da rana."
"Barkan ki, ya gida?."
"Lafiya lau Abiy, ya su Nayla? Tana lafiya?."
"Lafiya lau." Didi ta kalli Kawu ta ce, "Kawu mahaifin jikar Hajja ne Nayla, kuma shine wanda ya karɓo Omar daga hannun Senator kwanaki da abin nan ya faru."
Kawu ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "ya yi min bayanin komai Aisha. Wata magana yazo da ita mai girma, wai yana so a yanzu a ɗaura auren ƴarsa da ƙaninki Omar." Wara idanu Didi tayi tare da dafe ƙirji cikin mamaki ta ce, "Aure Kawu!?." Ya ɗaga mata ka ta juya ta kalli Abiy ta ce, "Abiy auren Nayla da Omar?."
"Haka nake so, yanzu kuma babu ɓata Lokaci."
Jawad da yake gefe ya ce, "Amma Abiy...." Dakatar dashi yayi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce, "kar wanda ya yi min magana yanzu" ya kalli Aisha ya ce, "Auren zai yu?." Didi ta kasa magana sai kallon Abiy da take yi dan ta rasa abinda zata ce. Abiy ya ce, "in bazai yu ba ki faɗa min kawai." Didi cikin kiɗima ta ce, "Abiy ni wallahi ban san me zance ba, abin nake ji kamar a mafarki. Meyasa ka ke son aurawa Nayla Omar?. Abiy na san ka san Omar ba sai na faɗa maka ba, meyasa haka kwatsam zaka yanke wannan hukuncin?."
"Haka nayi ra'ayi" ya bata amsa a taƙaice.
"Amma Abiy Nayla ba sa'ar auren Omaar ba ce, ka san halin sa ba sai na faɗa ba, kowa ma a nan ya san halinsa ba sai an maimaita ba. Meyasa ka ke son aurawa ƴarka shi don Allah?" Ta faɗa a sanyaye tana kallon Abiy.
Abiy yayi ajiyar zuciya cikin ɓacin ran da yake ciki, danne ɓacin ransa kawai yake yi yana magana amma Allah kaɗai ya san irin yadda zuciyarsa take tafasa akan abinda Nayla tayi masa wanda bai yi tunani ba. Ya ce, "Aisha ki amsa min tambayata kawai, in auren zai yu to in bazai yu ba ki faɗa min."
Didi ta sunkuyar da kai dan bata san me zata ce ba, auren Nayla da Omar kuma...? to akan wanne dalili kenan? Kuma ta tabbatar Omar ɗin ma bai san labarin ba, aka ɗaura auren sa bai sani ba ai an shiga tashin hankalin faɗansa, dan tsaf zai saka yi yaƙin duniya. To ita Nayla ɗin ta sani ko bata sani ba..? Meyasa lokaci ɗaya Abiy zai zo da wannan maganar?.
Kawu ya katse shirun ya ce, "zai yu mana tunda kana so, amma ka san waye Omar kuwa?." Abiy ya ce, "kaf labarin Omar na sani, har wanda baku san dashi ba na sani, har wanda kuke tunanin ban sani ba shima na sani, yanayin alaqarku da duk abinda yake yi na sani. Kawai ina so ku amince min ne yanzu babu ɓata Lokaci."
Kawu ya kalli Didi ya ce, "Aisha ya ki ka ce? Kece uwar Omar, kina ganin kin amince?." Didi tayi ajiyar zuciya bata san abinda zata ce ba wallahi, in ta amince kamar ta cutar da Nayla ne duk da bata san dalilin Abiy na aura mata Omar rana tsaka ba, in bata amince ba kuma kamar bata kyautawa Abiy ba duk da tarin taimakon da ya yi mata bai cancanci haka ba. In ta amince ma aka ɗaura auren da wacce fuska Omar zai karɓi auren?.
Numfashi ta sauke a hankali ta ce, "Ayi abinda Abiy yake so." Abiy yayi murmushi ya ce, "na gode. A yanzu nake so a ɗaura auren nan babu ɓata lokaci."