Sashe 8
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kan carpet ta zauna a sanyaye ta ce, "Ina yini." Mum ta ce, "ba gaisuwarki muka kira ki mu ji ba, ke ce Yayar ta sa?." Didi ta ɗaga kai alamun Dad ya ce, "Ina iyayen ku?." Didi ta ce, "sun jima da rasuwa."
"Na sani, na san hiv ce ta kashe babar ku, sannan baban ku ya mutu ta sanadin shan taba har huhunsa ya lalace."
Didi ta sunkuyar da kai idonta yana cikowa da hawaye. Dad ya yi tsaki ya ce, "ɗan uwanki ya yiwa ƴata asiri mai ƙarfi kin san da hakan?." Didi ta girgiza kai ta ce, "Ban sani ba." Dad ya ce, "to na faɗa miki yanzu, ya yi mata asirin da ta kusa fita daga hankalinta. Dalilin da ya saka nace ki zo shine, ki je duk inda ki ka san ya binne asirin nan ki tona shi a karya, in ba haka baza ki sake ganin sa ba har abada."
Hawaye ya sakko daga idanun Didi, ta yi sauri ta share a sanyaye ta ce, "don Allah ku yi haƙuri ku barshi ya dawo gida, nayi alƙawarin bazai sake kallon koda hoton ƴarku ba balle har wata magana ta shiga tsakanin su. Omar yana jin maganta sosai, in na ce ya yi zai yi, haka in nace ya bari zai bari. don Allah, don Annabi ka yi haƙuri ka sassautawa Omar. Maraya ne bashi da uwa bashi da uba, nima shi kaɗai ne dani, don Allah ka taimaka min."
Mum ta ce, "ya san shi marayan ne ya yiwa ƴar mu asirin da shiga wani hali mara daɗi? Ya san da bashi da kowa ya kawo kansa gidan nan cikin gadara da nuna iko?. A wajan mu bai wuce sauro ba, yadda zamu kashe sauro mu kwana lafiya haka zamu kashe shi ba tare da kowa ya sani ba. Matuƙar kina son sake ganinsa a duniya dole ki san yadda zaki yi a karya asirin nan, in ba haka ba wallahi sai mun ɓatar da shi a duniya, sai ya bar rayuwa a duniya, ke dashi sai dai a lahira wallahi!."
Didi murya na rawa ta ce, "wallahi bai yi mata komai ba, wallahi bai yi mata asiri ba. Itace ta fara cewa tana sonsa, ita ce tazo har gida ta......." Cikin tsawa mai ƙarfi Dad ya ce, "ki mana shiru! Jahila mara hankali. Mu za ki kalla kina cewa ba asiri ya yi mata ba? To me ya yi mata? Ko kina so ki ce soyayyarsa ce zata iya shiga zuciyar ƴarmu?. Waye shi da ƴar mu zata so shi? Na ce waye shi!?."
Didi ta sunkuyar da kai tana hawayen baƙin ciki da damuwa. Mum ta ce, "wai har tana ƙoƙarin faɗa mana ita taje har gida ta ce tana sonsa, to in ba asiri ya yi mata ba taya haka zai faru?. Dear ka san abinda zaka yi wannan matar ta bar falon nan kafin raina ya ɓaci na saka a yi mata dukan tsiya." Ya kalli Didi ya ce, "kina jina? Ki tabbatar da kin saka ya karya asirin da ya yi mata, in ba haka ba kema bazan bar ki ba wallahi, sai na saka miki baƙin ciki a zuciyarki." Didi murya na rawa matuƙa ta ce, "to a ina zan ganshi balle ya karya asirin?."
Mum ta kalli Dad ta ce, "in dai yana kusa a haɗata dashi su yi magana, ya tabbatar ya karya asirin in ba haka ba wallahi bazai fita ba." Dad ya kalle ta ya ce, "Ina zuwa" ya faɗa yana ɗaukar waya yana dannawa kafin ya kara a kunne ya yi magana. Babu wanda ya sake yi mata magana har wani ya shigo falon da girmamawa. Dad ya kalle shi ya ce, "gata nan, ku je tare." Mum ta miƙe tsaye ta ce, "nima zan je."
Dad ya ce, "me zaki je ki yi?."
"Ina so nayi magana dashi ne."
"Akan me?."
"Ni dai ina so naje nayi magana dashi." Dad ya miƙe shima ya ce, "mu je tare gabaɗaga." Mum shiga ciki kawai tayi ta ɗauko mayafi suka shiga bayan wata mota, ita kuma Didi suka ce ta shiga motar Escort ɗin Dad. Didi a motar ta yiwa Bashir text ta faɗa masa.
Tafiya suka yi mai ɗan nisa kafin su ƙaraso wani babban waje aka yi parking da motar suka fito suka shiga. A wani babban waje suka zauna Didi dai tana tsaye bata iya zama ba buri take ta ga Omar. Kallon inda aka buɗe ƙofa tayi ta ga Omar ɗinta ya shigo cikin yanayi mara daɗin gani.
Kayan jikinsa gabadaya sun canja kala fuskarsa ta cika da gashi haka kansa ya taru da gashi, da ganin yadda yake tafiya ka san ya wahala ko yana kan wahala, idanunsa sai lumshewa suke yi saboda wahalar da take ɗawainiya da gangar jikisa. Kai kana ganin sa ka san bayan wahala ma akwai yunwa a tare dashi, ya canja gabaɗaya kamar ba shi ba.
Kayan jikinsa sun yage kaɗan musamman rigar jikinsa, ana iya hango fatar jikinsa da ta koma wata kala ga shatin ciwo da alama dai duka ake masa da bulalai bama bulala ba. Kuka Didi ta fashe dashi ta ƙarasa inda yake ta ce, "Omar!." Jin muryar Didi sai ya ɗaga idanunsa da suka yi masa nauyi ya kalle ta, a iya laɓɓansa ta ga ya furta sunanta hakan ya saka ta rungume shi tana kuka sosai.
Ɗagowa tayi tana kallon sa ganin yadda ya dake kamar ba dashi ne yake cikin wannan yanayi ba, fuskarsa har ɗan washewa tayi saboda ganin rabin ransa. Muryarsa a ɗan dashe kaɗan ya ce, "Didi me ki ka zo yi nan? Kina lafiya? Babu abinda ya same ki?" Ya faɗa yana kallon fuskarta.
"Omar haka ka koma?." Murmushin ƙarfin hali ya yi mata ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "Ina lafiya kar ki damu. Waye ya kawo ki nan? Ina fatan ba ke kaɗai ba ce ba ko?. Babu abinda yake damun ki?."
Mum ta miƙe tana hararar Omar bayan ta sauke facemask ɗin da ta saka a hanci ta ce, "bazan iya zama mai yawa tare dashi ba, gabaɗaya dashi da wajan abin ƙyama ne" ta faɗa tana yatsine fuska tana kawar da kai. Ta kalli Dad ta ce, "Dear ka yi abinda ya kawo mu kawai." Kallon Omar Senator ya yi ya ce, "ga Yayarka nan tazo bada haƙuri dan a fitar da kai, ka faɗa mata inda ka binne asirin da ka yiwa Narma ta je ta tona shi a karya, daga nan sai nayi tunani in zan iya yafe maka."
Kallon sa yake yi dan saboda shi ya dake kamar yana lafoya duk da abinda yake ji a jikinsa. Murmushin rainin hankali yayi ya ce, "ƴarka ai bata kai matsayin da zan yi mata asiri ba." Mum ta kalle shi ta ce, "ai ba jayayya aka zo yi da kai ba, ga Yayarka nan in baka karya asirin nan ba wallahi akanta komai zai ƙare. Na lura itace weekneess point ɗinka, to wallahi duk azabtar da kai ɗin da ake yi ita sai mun ninka mata."
Didi ya kalla da yaji ta riƙe hannunsa alamun kar yace komai, yaga ta marairaice tana hawaye sai ya ce, "Didi baki ji abinda suke faɗa ba ne? Ni wanne asiri na yiwa ƴatsu? Har ta kai matsayin da zan yi mata asiri ne?. Wallahi bata kai ba, irin ta dubu basu isa nayi musu asiri dan su soni ba. Sai dai in ƴarsu ce tayi min asiri amma ba dai ni nayi mata ba."
Kulle ido tayi ta buɗe jin ya riga dai ya faɗi abinda bata so ya faɗa ɗin ta kalli Sen ta ce, "Kuyi haƙuri don Allah, tun farko na faɗa daman babu abinda ya yi mata, amma tunda kun dage a kan hakan zan koma duk yadda zan yi zan yi wajan an karya asirin."
"Didi ban san ki da ƙarya ba, dan kare ni kar ki faɗi abinda bazai faru ba. Babu asirin da na yi musu balle a karya shi. Ba ƴarsu ba, ko su ɗin ne da kansu basu isa nayi musu asiri ba wallahi, zuciyar Omar ta wuce wannan mataki, babu wata halitta da zan iya yiwa asiri a duniya. Ƴarsu ɗin banza da wofi, wacce ita da har ni Omar zan yi mata asiri?."
Mum ta fusata sosai ta kalli Dad ta ce, "ka ga rainin da ka jawo mana, anya escort ɗin na suna akin su kuwa? Tunda har yake tsaye akan ƙafarsa wallahi bai sha wahala ba" ta juyo ta kalli Didi ta ce, "kince yana jin maganar ki gashi kema ya nuna mana jahilcin nasa bai bar ki ba. Ki ja masa kunne a tabbatar an karya asirin nan in ba haka ba wallahi zaku yi dana sani gabaɗayan ku."
Didi zata yi magana Omar ya rigata ya ce, "Jahili shine wanda bai san abinda yake yi ba, ni na san abinda nake yi kuma ban yi dana sanin zuwa gidan ku a matsayin mai neman auren ƴarku ba. Ina alfahari da hakan ko babu komai zan shiga cikin tarihin rayuwarku, har abada baza ku manta da mai suna Omar yazo har falo ya ce yana son ƴarku ba. Jahilin da ku ka raina shine soyayyarsa ta hargitsa ƴarku har kuke tunanin an yi mata asiri. Ƙarfin tasirin Omar kenan ku ka gani, ƴar da kuke ji da ita zuciyarta ta gama narkewa a soyayyar wanda ku ka raina ku ke kallon sa ƙasƙantacce. Sai dai a yanzu ta makara, lokacinta ya wuce, domin in Omar ya yi gaba baya juyawa baya, Omar in ya tsallaka baya sake tsallakowa, Omar in ya tafi baya dawowa. Ku bata haƙuri, ba wai na ƙita bane kawai akwai abinda ya fita mahimmaci a gabana yanzu. Ku yi mata addu'a Allah ya bata ikon jure rashina. Na san zaku sha matuƙar wahala kafin ta jure, dan nima tasha wahala kafin na fara ko da ɗaukar kiran wayarta."