Sashe 11
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abiy ya ce, "gaskiya dai gashi nan dai kawai, dan in har yana da hankali to tabbas shaye-shayen su na ɓata gari ya taɓa masa ƙwaƙwalwa. In ba haka ba ya ɗauki ƙafa ya je ya ce yana son ƴar Sen Sagir? Ya san waye Sen Sagir kuwa?." Suka yi shiru Abiy ya ce, "To ai ko zauna gari banza wanda bashi da komai ya je ya ce masa yana son ƴarsa dole ya ɗauki mataki balle Sen. Kuma dole ya ce asiri ya yiwa mata take sonsa. Meye abin so a tare dashi har da zata fita hankalinta haka?." Nayla dai wani irin sanyi jikinta ya yi da jin kalaman Abiy, zuciyarta na bugawa, guiwarta kamar ana dukanta saboda sagewar da tayi.
Abiy ya numfasa ya ce, "well, ya taimaki Nayla a lokacin da take buƙatar taimako, ya kuɓutar da ita daga masu sharrin fyaɗe. Ya cancanci na taimaka masa a fito dashi tunda ba wani laifi ya aikata ba. Na san Sen Sagir sosai, abokina ne sosai tare muka yi ABU Zaria. Kuma ni ne class captain a lokacin, bara mu ga" ya faɗa yana ɗaukar waya yana dubawa.
A speaker Abiy ya saka kiran daga can ɓangaren Sen yana ɗauka ya ce, "Class Captain....!." Abiy ya murmusa ya ce, “ni ɗauka baka da number ta ai.” Sen yayi dariya ya ce, “Haba ni na isa nace bani da number ka?.”
“Ka isa mana Sem, ai ka kai matsayin da ba number kowa zaka ajiiye ba.”
“Ai kai kana cikin mutane na farko a wayata.” Abiy yayi murmushi suka gaisa cikin wasa da dariya na ƴan makaranta kafin Abiy ya ce, “kwanaki nazo Abuja na karɓi offer ta ƴar wajena Nayla, naso nazo wajan ka sai kuma na sha’afa wallahi.”
Sanata ya ce, “gaskiya baka kyauta ba, duk da dai nima kwanaki na shiga Zaria naso na kira ka wallahi dare ya yi min. “
“Haka ne, komai sai Allah ya yi.”
“A wacce ma’aikata ta samu aikin?.”
“FIRS.”
“Haba Captain, me zata yi da wannan ƙaramin aikin da salary sa bai wuce 400k per month ba? Ga aiki a nan Abuja da zata samu kuɗi me zata yi da 400k kamar wata almajira?.” Abiy ya yi dariya kafin ya yi magana Sen ya ce, “ka turo ta Abuja akwai aikin da zan bata, 900k ne per month banda allowances da suke shigowa. Shima dai tayi manage kawai.”
Abiy ya yi dariya ya ce, “Senator! Ai ba dan salary take aiki ba, hakan burinta ne shiyasa kawai na bari tana yi.” Sen ya ce, “Sai ta cika burinta da abu mai kyau ba wannan ba, ka rasa aikin da zaka bata sai wannan ƙaramin aikin? Me zata yi da kuɗin da bai wuce albashin house maids ɗin gidansu ba?…Ka turo min ita kawai, zan cika mata burinta da aiki mai kyau, in kana tunanin baka so ta zauna ita kaɗai a guest house sai ta zauna a gidana wajan Narma da Najwa.”
Abiy ya ce, “A’a, barta a Kaduna kusa dani ya fi. Nayla me zata yi da kuɗi tana yarinya ƙarama?. Tana da shop fa.” Senator ya yi dariya ya ce, “Najwa ba ma Narma ko Nabil ba, itace take kula da ɓangare guda na companyna, kuma tana aiki sannan itama tana da shops. Ai yaran yanzu sai da kuɗi Captain, haka duniyar ta zama.”
Abiy ya ce, “kana Abuja ne?.” Sen ya ce, “A’a ina Kano, nazo ɗaurin aure ƴar sarkin Kano da za a yi gobe.” Abiy ya ce, “nima Ina Kano ɗin, gobe zan kuma shiga ɗaurin auren in sha Allah.” Sen ya ce, “to ya kamata mu haɗu gabaɗayan mu, dan yawancin ƴan class ɗinmu duk suna nan goben.” Abiy ya ce, “Allah ya kaimu goben, sai mu haɗu gabaɗaya yi zumunci a samu lada.” Sen ya amsa yana dariya kafin su yi sallama Abiy ya kashe wayar.
Kallon Nayla ya yi da ta sunkuyar da kai ya ce, “Gobe zan yi masa maganar Omar ɗin, in sha Allah zai dawo.” Nayla farin ciki take ji a zuciyarta har hakan ya bayyana akan fuskarta, ta ce, “to Abiy na gode.” Abiy ya kalle ta a nutse ya ce, “ga murmushi nan kina yi, da alama dai shima kina shiri dashi sosai ko?” Ya tambaya da niyar bugun cikinta.
Sunkuyar da kai tayi ta ce, “A’a Abiy, ko magana bamu taɓa yi ba, ni saboda Yayarsa kawai nake so ya fito.” Abiy ya girgiza kai ya ce, “ko dan taimaka miki da ya yi a shekarun baya ai ya cancanci ki so ya fito. Kar ki damu komai ya ƙare.” Nayla ta yi dariya tana kallon Mama da ta zuba mata ido tana kallon ta.
Da sauri ta tashi ta shiga ɗaki Salma da Jidda suka bita. Murmushi suka samu tana yi a bayyane tana cewa, “zan zama silar fitowar Omar in sha Allah, in sha Allah zai fito. Wayyo daɗi, Allah na gode maka.” Jidda ta kalli Salma da suke kallon Nayla da mamaki, Jidda ta girgiza kai tana gasgata abinda take zargi a zuciyarta. Jidda ta ce, “Twiny ko dai Omar shine wanda ki ke so?!.”
[20/09, 4:25 pm] +234 906 075 3382: KRB2P006
Arewabooks@nanahaleema11.
Nayla gabanta ya faɗi sosai, ta jiyo a firgice tana kallon su dan tambayar tazo mata babu zato babu tsammani. Duk sun tsare ta da ido suna jira su ji abinda zata ce. Kallon kallo ake a tsakanin ta su, suna jiran amsarta ita kuma duk ta firgice. Salma ta ce, "tambayar ki mu ke yi Nayla, Omar ƙanin Didi shine wanda ki ke so ɗin?." Tayi ƙoƙarin dakewa da son ɓoye damuwarta ta ce, "Wacce irin magana ce wannnan? Ni ba haka bane ba."
Jidda ta ce, "to meyasa muryarki take cracking? Meyasa ki ka ji tsoron tambayar da muka yi miki?. Sannan meyasa hankalinki ya tashi a kan ance yana cikin wahala?, gudu kika dinga yi da mota sai da kika zo ki ka samu Abiy sannan hankalinki ya kwanta. Ki faɗa mana shine wanda ki ke so ɗin?. Duk alamomin soyayya ya bayyana a yanayin ki, yadda ki ka zaƙe a kansa ya saka muna zargin shine wanda soyayyarsa take wahalar dake, ki amsa mana Nayla."
"Eh shine!" Ta faɗa a sanyaye tana zubewa a kan gado tana sake fashewa da kuka. A tare suka wara idanu Jidda ta ƙarasa inda Nayla take dan Salma tayi suman tsaye. Jidda ta zauna kusa ta da ita ta ce, "Twiny da gaske shi ki ke so?." Kai ta ɗaga tana kuka ta ce, "Shine Twiny. Ban san ya akayi hakan ta faru ba, na san dai tsoronsa nake ji amma ban ya akayi na fara sonsa ba. Nayi kuka, na yi addu'a amma na kasa cire shi daga zuciyata. Bai san ina yi ba, tunda shi Abuja ya je neman aure a gidan su wata bani ba, amma duk da haka bana jin haushinsa Twiny."
A kan kafaɗar Jidda ta ɗora kanta tana kuka sosai Jidda tana shafa kanta dan bata san ne zata ce mata ba. Salma daƙyar ta iya motsawa tazo wajan da suke ta zauna a ɗaya gefen ya zama sun saka Nayla a tsakiya kenan. Salma ta ce, "Nayla wai Omar ɗin Didi ki ke so?."
Bata iya bata amsa ba sai numfashi da take saukewa a jikin Jidda. Salma ta ce, "Innalillahi! Mun shiga uku." Nayla ta ɗago daga jikin Jidda idanunta sun jiƙe da hawaye ta ce, "shiyasa naƙi faɗa muku saboda faɗar babu amfani Salma. Babu ribar da zan samu da soyayyarsa, wahalar da ni kawai take yi wataƙila tayi ajalina. Wallahi duk samarin da Abiy yake basu damar ganina na kasa kallon kowa da fuskar so, shi kaɗai nake so, shi kaɗai zuciyata take da burin aure, shi kaɗai nake ji a raina in ban aura ba kamar bazan iya zaman aure da kowa ba, na kuma san bazan taɓa mallakarsa ba har abada."
Jidda a sanyaye ta ce, "Meyasa ki ka ce haka?." Tayi murmushi ta ce, "baki ji me Abiy ya ce bane? Ko zauna gari banza yaje yace yana neman aure a gidansa baza a bashi ba balle gidan Sen. Dame Sen ya fi Abiy Twiny? Mulki kawai ya fi Abiy, amma duk abinda ya mallaka a duniya Abiy ma ya mallaka. Kinga kenan harda gidan mu a cikin gidajen da baza'a bashi aure ba, ni daman na san aurena dashi bazai yu ba shiyasa ban sakawa zuciyata zan aure shi ba. Kuma shi bai ma san ina sonsa ba."
Salma tayi ajiyar zuciya ta ce, "gaskiya ne zancen ki Nayla, auren Omar bana hango yuwarsa a rayuwarki. Gwara mu faɗa miki gaskiya kar mu cuce ki mu yaudari zuciyarki da kalamai na ƙarya dan mu kwantar miki da hankali. Omar ba irin wanda ya cancanci a bashi aure bane, sam ba tsarin auren ki bane."
"Na sani Salma. In ba dan ɗabi'arsa ba ni zan iya zama dashi, ban damu da bashi da kuɗi ko bashi da wani abu ba. To ɗabi'a sa baza ta taɓa sakawa Abiy ya amince ba, Inda Abiy zai amince ni zan iya zama dashi a haka, koda zai dinga bani tsoro kamar yadda yake yi ko yaushe na shirya Salma...." ta sake faɗa a sanyaye hawaye na sakkowa. Jidda ta kalle ta da kulawa ta ce, "kuma kin ce bai ma san kina sonsa ba ko?."
"Bai sani ba, kuma bana fatan ya sani ɗin. Domin Didi ta faɗar min kalar wulaƙancin da ya yiwa Narma a lokacin da ta je gidan su ta ce tana sonsa. Daƙyar ta iya samun kansa har ya amince mata, jin kunnena naji yana waya yana yi mata faɗa kamar ba wacce yake so ba. Wataƙila soyayyarsa kashe ni zata yi, dan wallahil azim ina matuƙar son Omar, Ina matuƙar ƙaunarsa, ina yi masa ƙaunar da ban taɓa yiwa wata halitta a duniya ba sai shi. Matuƙar dauriya nake yi, juriya da haƙuri da jajircewa nake yi nake iya sarrafa zuciyata akansa. Amma haƙuri na ya fara ƙarewa, gab nake da karaya..." ta faɗa tana kuka sosai.