← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 52

Sashe 21

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai la'asar suka shiga Kano, Didi sai da ta shiga wajan Hajja ta bata labarin duk abinda ya faru har kayan da Mama ta bata da kuma kuɗin da Abiy ya bayar ta nuna mata. Hajja ta dinga murmushi dan ta san daman baza ta ji kunya ba dan Didi ta je gidan su Nayla ba, saboda kirkin Abiy da matar gidan. Dubu hamsin ta lissafa a dubu ɗari biyun da Abiy ya bayar ta bawa Salma ta ce, "Salma ga na saka data." Salma tayi dariya ta ce, "Haba Didi, wallahi bazan karɓa ba, na gode sosai."

Didi da mamaki ta ce, "Meyasa baza ki karɓa ba?."
"Haba Didi, dan na raka ki sai kin bani kuɗi? Wallahi bazan karɓa ba." Didi ta ce, "to ki bawa Sayyadi driver Hajja ya saka kati." Salma ta karɓa ta ce, "zan bashi in sha Allah." Didi ta dinga godiya sannan ta tashi ta shiga gidan su.

Sallar la'asar tayi tare da yin wanka sannan ta dawo falo ta zauna. Yunwa take ji amma bata tunanin zata iya girki a gajiye take sosai. Baccin gajiya ne ya ɗauketa sai kiran sallar magriba ne ya tashe ta. Miƙewa tayi tana salati ta yi alwala ta dawo ta tayar da sallah, bayan ta idar ne ta iya tashi ta dafa musu indomie ta zuba a plate kenan ta fito falon ya shigo da sallama.

Amsawa tayi sai ta bashi plate ɗin hannunta ta ce, "tun ɗazu na so nayi mana girki sai nayi baccin gajiya." Karɓa ya yi ya zauna ta koma ta ɗauko ragowar da ta ajjiye masa ta dawo ta zauna ta fara ci kamar yadda yake ci shima. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta tura masa ragowar kuɗin da Abiy ya bayar ta ce, "Mahaifin Nayla ya bada dubu ɗari biyu ya ce mu zauna mai a mota, na bawa Salman Hajja dubu hamsin taƙi karɓa, amma na ce ta bawa driver da ya kaimu shima ya siyi kati. Ga ragowar nan, ga kuma kayan da Mamanta ta bani. Lace ne da atampa sababbi da turaren wuta, humra da mayafi" ta faɗa tana nuna masa kayan akan kujera.

Bai ce komai ba sai da ya kusa cinye indomie ɗin sannan ya ajjiye plate ɗin ya kalle ta ya ce, "Didi baki kyauta min ba, abinda kin ka yi min sam ban ji daɗi ba." Didi da mamaki ta ce, "me nayi maka?."
"Meyasa baki faɗa min in za a ce waje irin wannan ana siyan abu a kai ba? Sai gani nayi kawai kin bada tsaraba ba tare kin faɗa min ba. Shiyasa ake cewa ke ce kike ɗaukar ɗawainiya ta bana yi miki komai." Didi da mamaki ta ce, "Omar da girman ka da komai sai na faɗa maka? Baka san ya kamata ba dai?."

"Didi ban sani ba, ban sani ba. Bani da mahaifiyar da zata faɗa min abinda ya kamata da wanda bai kamata ba. Ban ji a raina ya kamata ace na siyi wani abu na kai ba saboda ban saba zuwa ba, ban taɓa yiwa wani godiya a duniya ba daga shi sai Hajja. Da nake zaune a gabansa ji nake kamar ana ɗaure ni, ban taɓa jin nauyi da girman mutum a idanuna kamar yadda na ji na shi ba. Na ji na kasa haɗa ido dashi balle na yi magana, a karo na farko a rayuwata da naji girma da nauyin wani mutum, duk na ɗauki hakan a rashin sabo saboda ban taɓa zuwa wajan wani da sunan godiya ba. Meyesa kafin mu tafi baki faɗa min ana siyan abu a kai ba?."

Didi kallon sa take yi har ya kai ƙarshe ganin da gaske yake maganar sannan ta ce, "shikenan naji laifina ne ban faɗa maka ba, nan gaba sai ka aikata ba tare da an faɗa maka ba. Kuma in na siya kamar ka siya ne ai." Omar ya ce, "ni dai ban ji daɗi ba, da kin faɗa min da ko wani abun an siya an haɗa an ka. Da kin faɗa min da ni zan bada kuɗin abinda zaki yi." Didi ta ce, "shikenan ai ya wuce."

Ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Nawa ki ka kashe?."
"Gurasa ce fa ta dubu goma ba wani abun ba." Hannu ya saka a aljihu ya ɗauko dubu bakwai ya ajjiye mata ya ce, "ga kuɗin da ki ka kashe. Sannan ki haɗa da wannan ma ki riƙe hidima ce a gabanki" ya faɗa yana nuna mata wanda ta turo masa kusa dashi. Didi tayi murmushi ta ce, "to na gode."

Wayar Didi ce ta katse masa maganar da ta yi niyar yi, ta duba taga Nayla ce sai ta saka a speaker daga can ɓangaren Nayla ta ce, "Didi ina fatan kin sauka lafiya, Ina ta kiran ki ɗazu baki ɗauka ba." Didi ta ce, "mun sauka lafiya lau Nayla. Bacci nayi shiyasa baki same ni ba. Ya jikin naki?."
"Jiki da sauƙi Didi."
"Kin daina kukan?." Nayla ta ɗan murmushi ta ce, "Didi na daina" ta faɗa a sanyaye. Didi ta ce, "ai gwara da ki ka daina, gabaɗaya duk na damu wallahi:"

Ƴar dariya tayi ta ce, "An gode Didi, na ji daɗin zuwan ku sosai." Didi ta ce, "mu ne da godiya Nayla. Yadda aka karɓe mu a gidan ku wallahi ya fi min komai daɗi."
"Babu komai Didi. A gaishe da.....Yaya Omar" ta faɗa a rabe muryarta har rawa take yi. Didi tayi murmushi ta kalli Omar da yake suraren su ta ce, "Yaya Omar yana jinki." Nayla tayi murmushi ta ce, "na san bazai yi magana ba, amma ki ce ina  yi masa bangajiya mun gode sosai."

Didi ta ce, "to Nayla, mun gode da tarba mai kyau Allah ya ƙarawa Abiy tsahon rai." Nayla ta amsa da amin tayi shiru ko Omar zai yi magana amma bai ce komai ba dole ta yanke wayar. Murmushi Didi tayi bayan ta kashe wayar ta ce, "Wai Yaya Omar, Nayla akwai ta da bin dariya. Ko yaushe ya zama Yaya ɗin oho mata."

"Ban cancanci ace min Yayan bane shiyasa har sunan ya baki dariya?." Da mamaki ta kalle shi dan bata ɗauka zai yi magana ba, sanin halin sa ba tankawa zai yi ba musamman Nayla da yake yawan faɗar haushinta yake ji.

Didi ta sake yin dariya ta ce, "A'a ni ban ce ba Malam Omar, meye nawa na cewa baka cancanta ba? Kawai na san haushinta ka ke ji ne." Bai yi magana ba ya share ta Didi ta ce, "anyi kiran sallar i'sha, sallah zan yi" ta faɗa tana tashi ta shiga ciki ya bita da kallo.

Yaya Omar ɗin da Nayla ta faɗa a lokacin da zasu bar gidan su da yadda hawaye yake zuba a idonta kawai ya tuna, ajiyar zuciya ya yi ya rufe ido sai kuma Narma ta faɗo zuciyarsa itama lokacin da take kuka lokacin da ta je wajansa. Tashi ya yi ya bar falon zuciyarsa cike da tunani kala-kala.

Bayan Kwana biyu.

Bikin Didi ya matso sosai an kai lefe gidan Kawu akwatina goma sha huɗu kaya masu yawa sosai. Baba Adamu kamar yadda ya ce an gama zuba komai na gidan Didi, hatta kayan kitchen ya zuba sai abinda Didi ta siya ta ajjiye aka kai can. Gida ne babba da falo biyu da bedroom uku, sai dai unguwar babu jama'a sosai amma gida kan ya yi kyau sosai.

Didi ana ta yi mata gyaran jiki duk da ita kaɗai take yi komai, sai Hajja da Salma da suke taimaka mata dan bata da wani dangi da yake taimakon ta tunda ba sabawa suka yi sosai ba. Har gwara Umma Sarood ƙanwar mahaifiyarta ta kawo mata turaren wuta irin nasu na mutanen Chad, har kayan gyaran jiki ta haɗo ta kawo mata. Mama Zainab Yayar mahaifiyarta ita kuma ta ɗauƙi nauyin zuba turaren wutar gidan, ta ce duk wani abu indai na ƙhamshi ne ita zata yi amma bata so Omar ya sani. Didi ta ji daɗi sosai har ta nuna musu, kuma suna yawan kiranta su ji shirin biki, zuwa ne dai basa yi saboda haɗuwa da Omar baya zama alkhairi. Duk wani shiri ita da Hajja ake yi sai Salma da ta kasance tana tare da Hajja ko yaushe.

Ɓangaren Omar ya watsar da duk wani abu da yake yi a baya, duk da daman ya jima da watsarwa amma yanzu yana ƙoƙarin ganin ko cikin ƴan uwansa ƴan daba na baya ya daina shiga. Ya tattara kayan sana'ar da yake so ya fara kawai yake yi, shida yaran sa su uku gabaɗaya sun bashi haɗin kai wajan yin sana'ar da suke fatan zata kai su inda basu yi tunani ba. Duk abinda ake saka shi a ciki a ɓangaren daba yanzu an daina, ko an zo masa da maganar zai ce babu ruwansa a kai maganar gaban hukuma. Duk da hakan dai ba a kawo masa wargi saboda lasar yaji baya hana gyaɗa yin garɗi, duk da haka akwai sauran tsoro da kwarjinin da yake dashi a wajan mutanen gari. Halayyarsa baby abinda ya canja, baya shiga harkar kowa kuma baya sauraren kowa, fuskarsa kullum a haɗe magana ma ba ya yi.

Lamarin Narma ya ajjiye a gefe, duk da yana tunawa musmaman yadda abubuwa suka faru a gidan su, kuma yana matuƙar tausayinta in yaga tarin messages da kiran da take yi masa baya ɗauka. Wani messages ɗin ya karanta kamar ya yi mata kuka haka yake ji dalilin da ya saka ya daina buɗewa gabaɗaya, dan in yana buɗewa zata iya karya masa zuciya wata ran ya saurareta, shi kuma in yayi gaba baya komawa baya, in tsallake baya sake tsallakawa.

••••••

Nayla kuwa duk yadda ta kai ga dauriya ɓoye abinda yake ranta ta kasa, gashi Abiy ya matsa mata da tambaya abinda yake damunta, da ya gaji ya haɗa ta da Jawad suka je asibiti, da ta faɗawa likita abinda yake damunta ya tabbatarwa da Jawad tana tare da damuwa a tambaye ta aji abinda yake damunta. Duk ta tsorata saboda kar Abiy ya tambaye ta dan gaskiya bazata iya cewa ga abinda yake damunta ba dan ta san ba abu bane mai yuwa.
Chapter 21 · 0% Book details