← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 52

Sashe 12

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma ta rungume ta tana kuka itama cikin tausayin ƴar uwarta. Jidda a bayan Nayla ta ɗora hanunta cikin tausayin Nayla, dan yanda Naylan take yin maganar zai baka tabbacin daga zuciyarta maganar take fitowa. Sun jima a haka ko wacce na kuka kafin Nayla ta tsayar da kukan ta ce, "Abiy ya bani lokaci na fitar da wanda nake so a cikin mutune huɗu. Wallahi bana son su duka, bana tunanin zan iya zaman aure da ɗaya daga cikin su, ko na zauna zuciyata tana ga Omar ba ga wanda na aura ba. Ya zanyi? Ku faɗa min abinda zan yi na daina sonsa don Allah!" Ta faɗa da rauni wanda ya saka su Jidda sake fashewa da kuka.

Duka kuka suke yi daƙyar Salma ta iya dakatawa ta ce, "Addu'a zaki yi Nayla, addu'a zamu dage da yi Allah ya kawo mana mafita." Nayla ta ce, "Ina addu'a Salma, Ina yin addu'a babu dare babu rana. Wallahi zuwan mu umra ban san adadin addu'ar da nayi akan lamarin nan ba, kuka na ke yiwa Allah Ina faɗa masa ya cire min son Omar daga zuciyata amma soyayyar taƙi fita. In ina kuka a cikin sujjada ina faɗawa Allah damuwata sai na yi awa ɗaya a haka ban san nayi ba. In aka cigaba da haka zan mutu ne kawai, dan na san bazan same shi a matsayin miji ba mutuwar itace hutu a gare ni."

Jidda ta ce, "kar ki sare, ki cigaba da addu'a Allah zai miki magani Nayla. In kika roƙa yau Allah bai baki ba ki ƙara roƙa gobe, yana ji kuma yana gani, shi ya ƙaddara miki kuma shi ya nufe ki da fara son Omar. Allah ya san damuwarki amma yace ki roƙe shi zai yaye miki, kar ki sare Nayla, kar guiwarki ta yi sanyi akan addu'a, ki cigaba kar ki tsaya. Ki yi haƙuri." Basu hanata kuka ba dan ya cancanci tayi kukan, zuciyarta ta yaudare ta da ta fara son wanda auren ta dashi bazai taɓa yuwa ba. Shiyasa suka barta tayi kukan son ranta ko dan taji daɗi a zuciyarta. Ai kam ta kwashe sama da mintina ashirin tana kuka, zuwa lokacin kanta ya yi nauyi zazzaɓi ya rufe ta ruf.

Salma ce ta kwantar da ita ta tashi ta samo towel a banɗaki ta jiƙa shi da ruwan sanyi tana goge mata fuska da wuyanta. Rarrashin ta suka dinga yi har ta daina kukan Salma ta takura mata ta sha magani suna zaune a gefenta. A hankali kuma sai tayi bacci su dai kallon ta suke yi cikin tausayi.

Salma da Jidda fita suka yi zuwa harabar gidan dan su tattauna abinda ya kamata su yi. Salma ta ce, "Zuciyar Nayla bata yi mata adalci ba da ta fara son Omar Jidda, gashi bai ma san tana yi ba, sannan ko ni bazan goyi bayan ta aure shi ba duk da son da take masa."

Jidda ta ce, "yanzu meye abin yi? Wanne abu ki ke ganin zamu yi da zai taimaka mata?. Tana cikin halin azabar so da raɗaɗi mai ciwo, ya ki ke ganin zamu yi?."
"Addu'a kawai zamu taya ta Jidda, to in ba addu'ar ba me zamu yi mata?. Zamu je mu samu Omar in ya fito mu ce masa Nayla na sonsa ne?. Ko zamu je mu samu Didi mu faɗa mata?."

Jidda ta ce, "Amma tana buƙatar ɗauki Salma." Salma ta ce, "shiyasa na ce addu'a itace mafita." Jidda ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba Salma ta ce, "ikon Allah, shi kuma farin jinin mata masu hankali da kyau Allah ya bashi. Ki dai duba Nayla da Narma, a cikin babu wacce tayi sa'ar aurensa, amma lokaci ɗaya duk sun birkice a kansa kamar wani mutumin kirki? Anya ma ba asirin ya yi musu ba kuwa?." Jidda tayi dariya ta ce, "Wanne asiri ana zaune lafiya?."

"Allah Jidda abin da mamaki, ƴan mata zuƙa-zuƙa kamar Nayla da Narma ace sun birkice akan sa? Ƴan mata masu asali, kyau, ga arzuƙi amma su rasa wa zasu fara so sai wani Omar....Omar ɗin ma na gidan Didi ɗan daba wanda ko sana'a bashi da ita?. Allah lamarin nan abin dubawa ne, dan ni zuciyata ta fara amincewa da batun sanata akan asirin nan wallahi. Kuma da alama wanda sunan su fara daga N ne suke faɗawa tarkonsa, wataƙila wani malamin ne ya bashi sa a akan Nayla da Narma. Aniyarsa ta bishi, in sha Allah Nayla tafi ƙarfinsa." Ita dai Jidda dariya kawai take yi jin kalaman Salma na asiri.

Sai yamma Nayla ta farka a lokacin har sun shirya tafiya bikin Shayida, ta bisu da kallo ta ce, "har kun shirya?." Jidda ta ce, "ya ciwon kan?."
"Ya yi sauƙi sosai."
"To ki tashi ki yi sallah da wanka mu tafi."
"Anya zan iya zuwa Twiny? Ku je kawai basai naje ba." Salma ta ce, "A'a tashi ki shirya sai kin je, ganin mutane zai iya rage miki damuwa." Ta dole suka saka ta wanka ta shirya suka fita zuwa wajan bikin gabaɗaya.
[20/09, 4:25 pm] +234 906 075 3382: KRB2007
Arewabooks@nanahaleema11

Washe gari bayan sallar azahar Abiy da Senator da wasu manyan mutane su shida gabaɗaya suna zaune a wani babban falo na alfarma suna hira da nishaɗi ana tuna rayuwar makaranta. Su huɗu a ciki duk ƴan siyasa ne, Abiy da wani ne kawai ba sa harkar siyasa.

Ana cikin hira Abiy ya kalli Senator ya ce, "Senator daman akwai maganar da zamu yi da kai." Sen ya ce, "Ina ji." Abiy ya ce, "Akwai wani yaro Omar da ka kama ya je Abuja gidan ka haka ne?."

Sen ya ɗaure fuska yanayin sa ya canja lokaci guda ya ce, "Haka ne." Abiy ya ce, "Ina neman alfarma ka taimaka ka bani shi." Sen ya kalli Abiy ya ce, "ka san abinda ya aikata min kuwa? Narma fa ya je har gida ya ce yana so yana kallo na ina kallon sa." Abiy ya ce, "na sani, naji labarin komai. Ya yi tsaurin ido sosai bai kuma kyauta ba, amma kaima matsayin ka na babban ɗan siyasa ajjiye a wani waje ana azabtar dashi hakan bai kamace ka ba."

Sen ya ce, "Babu yadda na iya ne, ina so a koya masa hankali shiyasa na aikata hakan. Na so na tura shi prison kawai na ƙyale shi ne."
"Amma abinda kayi a yanzu zai iya taɓa maka siyasarka, da zarar maganar ta fita shikenan za a dinga yaɗawa ana faɗar ƙarya da gaskiya. Ka fini sanin meye siyasa, ka san yadda ƙaramin abu yake zama babba, ka san yadda ƙaramar magana take zama babba a gare ku."

Sen ya yi ajiyar zuciya ya kalli sauran ya basu labarin Omar kaf har zuwan Narma Kano da komai ya faɗa musu, kana ya ce, "in ban saka an killace shi an wulaƙanta shi ba ta ya zai fahimci ya yi kuskure?."

Mai girma gwamnan jahar Katsina kuma mahaifi ga Ashraf ya ce, "hakan ya yi, amma da ka sani baka saka ana wahalar da shi ba gaskiya, kai ka faɗa mana tasiri da ya yi maka a lokacin zaɓe, baka ganin zai zama tasiri nan gaba wajan lalata komai?." Senator ya yi shiru yana tunani kafin ya ce, "shiyasa zan san abinda zan yi a kai shi kotu a yanke masa hukuncin da bazai fito ba har abada."
"Wannan ba shawara ce mai kyau ba, kafi kowa sanin meye siyasa da yadda harkokinta suke gudana" Abiy ya faɗa yana kallon sa.

Senator ya ce, "asiri ya yi mata, in ba haka ba tana matuƙar son Ashraf, rana tsaka ta daina wai shi take so." Abiy ya yi dariya ya ce, "babu wani zancen asiri ni a ganina gaskiya, kawai tasirin soyayyar ne ba komai ba. Kuma yanzu ai komai ya wuce tunda ka tura ta london, a shawarata kawai ka aura mata Ashraf ɗin ya bita can su zauna a hankali zata manta dasahi."

Mahaifin Ashraf ya ce, "Abinda zan ce kenan, tunda ka ce ka tura ta Londan ayi auren au sai Ashraf ɗin ya bita can. Su samu good one year basa ƙasar nan, in suka dawo sai ayi biki tunda babu wanda ya san ma sun yi aure. Amma barin sa a kulle ana wahalar dashi zai iya taɓa ka nan gaba wallahi. In ƴan uwansa suka shiga gidajen yaɗa labarai suna cewa dan ya ce yana ƴarka ka yi masa haka ka yi tunanin maganar da zaka jawo." Wajan ya rabu biyu, Abiy da mahaifin Ashraf suna ganin riƙe omar bai kamata, ba sauran suna ganin hakan shine daidai.

Senator ya kalli Abiy ya ce, "A ina ka san shi?." Abiy ya ce, "Unguwar su a nan kakar Nayla take mahaifiyar Bilkisu matata da ta rasu. Shekaru kusan goma baya an taɓa yunƙurin yiwa Nayla fyaɗe, shine ya kuɓutar da ita har aka yi ƙoƙarin kai shi prison saboda ya zubarwa da yaron jini aka ce ya ɗauki doka a hannunsa, ni na san yadda akayi dai bai je prison ba. Yayarsa sun saba da Nayla sosai, halin da take ciki shine ya tashi hankalin Nayla tazo tana yi min kuka, kuma ko bata zo ba nayi niyar bin maganar saboda na rama alkhairin da ya yi min da alkhairi. Ina neman alfarma ayi masa afuwa bazai sake wannan gangancin ba."

Sen ya yi ajiyar zuciya ya kalli Abiy ya ce, "kuma ka tabbatar itama ba asirin ya yi mata ba?." Abiy  ya yi dariya mai sauti ya ce, "babu asirin da ya yiwa Narma ma balle Nayla ta shigo ciki, Babu abinda ya yi musu. Kuma ni dan ina bibiyar good background da good manners a aure ne, da ace yana dasu tsaf zan ce ka bawa Narma shi ɗin. Ai kana da arzuƙin da zaka iya sakawa ya tashi daga nobody to somebody."
Chapter 12 · 0% Book details