Sashe 43
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AbdulHamid ya ce, "Wannan duk ba abin damuwa ba ne, indai zai karɓi auren ai shikenan. Ni yarinyar ma nake jin tausayi wallahi, na farko baya sonta, na biyu ga yanayin halinsa, na uku bai ma san da auren ba, na huɗu bazata ta taɓa jin daɗin zama dashi ba. Kiyi haƙuri, amma wallahi wahala zata sha a zama tare da Omar, ban san meye dalilin mahaifinta na aura mata shi ba amma ya dakusar da rayuwarta, ba dan Omar bai cancanta ba sai dan yadda auren yazo."
Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "meye na bani hakuri? Gaskiya ka faɗa, ni kaina na san da haka. Ni kaina tausayin Nayla nake ji, yarinya ƴar gata, yarinya kyakykyawa, yarinya mai ilimi da wayewa ta ƙare a auren Omaar. In ba ƙaddara ba meye zai kawo haka?."
AbdulHamid ya murmusa ya ce, "ilimi, wayewa, kyau, gata ko kuɗi duk ba shi bashi ne damuwar ba. Inda ace zai karɓi auren hannu biyu duk abinda ki ka lissafa baza suyi tasiri ba, rashin karɓar da bazai yi ba ya fi komai illa a rayuwarta. Koda ya karɓa baza taji daɗi ba, kinga an dakusar da rayuwarta an lalata mata ƙuruciya."
Didi ta kulle ido ta buɗe ta ce, "bara na kira Kawu naji batun gidan sannan na san abinda zanyi akan batun Omar." Tashi yayi ya ce, "zan je na gaishe da Hajiya, in zaki fita wajan Omar ɗin kije sai ki yi min waya." Amsa masa tayi ya fita ita kuma ta kira Kawu akan maganar gidan kamar yadda ya ce.
A gidan Hajja suna zaune kamar Kullum ita da Salma Daddy yayi sallama ya shigo bayansa ƙanensa ne guda biyu Abba da Baba. Suka amsa Salma ta gaishe su suka amsa mata kafin su zauna su gaishe da mahaifiyarsu. Hajja ta amsa ta ce, "yau ku ne tare gabaɗaya?." Daddy ya ce, "eh Hajja, mu ne a tafe."
Hajja ta ce, "Allah ya sa dai Lafiya, dan nasan baku cika zuwa tare ba sai wani abun ya tashi." Abba ya ce, "Gaskiya Hajja ba lafiya ba." Hajja ta ce, "to me ya faru?." Daddy ya ce, "Alhaji Abdullah ne ya kirani, mahaifin Nayla kenan. Shine yayi min waya yana sanar dani yayi mana laifi, Nace laifin meye ya ce ya aurar da Nayla a shekaran jiya juma'a." Hajja cikin mamaki ta ce, "Ya aurar da Nayla kuma? Wanne irin ya aurar da ita ban gane ba?."
Baba ya ce, "mu ma bamu gane ba Hajja,
Mamaki muke yi wanne irin aure ne haka lokaci ɗaya?." Daddy ya ce, "Na tambaye shi na ce wanne irin ka aurar da ita kuma, ya ce min eh da gaske ya aurar da ita yanzu haka matar aure ce. Na ce lafiya wani abu ya faru ne? Ya ce ya faru, shiyasa ya yanke hukuncin aura mata shi." Hajja ta tafa hannu tana salati ta ce, "Waye shi to? Meye dalilin auren kuma?."
"Hajja bai faɗa min dalili ba, amma a yanayin maganarsa na tabbatar da bata daɗin rai ya aurar da ita ba, duk yadda aka yi ɓacin rai ne."
Hajja ta ce, "to ɓacin rai sai ya saka ya aurar da yarinya budurwa lokaci ɗaya haka?. Waye wanda ya aurawa ɗin?." Daddy ya sauke numfashi ya ce, "yaron nan maƙocin ku, ban san asalin sunansa ba amma Tiger ake ce masa." Salma da take ji tana faga tsaye ta wara ido tare da dafe ƙirji ta ce, "Tiger Daddy!?." Babu wanda amsa mata Hajja tayi shiru kafin ta ce, "Wai Omar ƙanin Aisha ta nan kusa damu?." Daddy ya ce, "Shi fa."
Hajja ta ce, "Omar ya aura mata? Abdullahi ya aurawa Hauwa Omar?. To akan me? Omar ɗin ne yaje neman aurenta ko me?."
Daddy ya ce, "Wallahi ban sani ba Hajja, iya abinda na sani kenan na faɗa miki. Shiyasa muka zo gare ki dan ki sani, amma gaskiya bai yi kyauta mata ba, duk da ban sani ba ko da sanin Nayla ɗin." Abba ya ce, "Koda sanin nata aure haka lokaci ɗaya haka kamar auren yaƙi? Kuma a rasa dawa za a ɗaura mata auren sai wannan taqadarin yaron?. Haba ai matsayin sa na mahaifin bai zaɓa mata miji na gari ba wallahi, bai sauke haƙƙin da Allah ya ɗora masa ba."
Hajja ta girgiza kai take yi cike da mamakin wannan lamari mai ɗaure kai ta ce, "A yadda Abdullahi yake matuƙar son Nayla bana tunanin haka kawai zai bata auren Omar, akwai dalilin da yasa ya aikata hakan, amma meye dalilin? Meyasa bai yi shawara da kowa ba ya yanke hukunci haka?."
Abba ya ce, "Hajja ni banga dalilin da zai saka ya ɗauki ƴar cikin sa ya aurawa wannan yaro ba, duk laifin da tayi ai shi ya haifeta, yana da ikon da ita, yana da ikon da zaiyi mata hukunci amma ba ta wannan hanyar ba. Me ye ma ya kawo Omar cikin rayuwarta? Wanne laifi zata yi masa kawai yaji a ransa shi zai aura mata?. Sai dai in akwai wani abun a ƙasa, tabbas Omar ɗin ya shiga rayuwarta ne shiyasa ya yi haka. In ba haka ba haka kawai bazai aura mata shi ba ba tare da dalili ba."
Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma na san kin san komai, Faɗa mana me ya faru?." Salma ganin iyayenta maza sun tsare ta da ido sai ta ruɗe ta ce, "Hajja ni ban san komai ba, yanzu naji labarin auren."
"Ai ba labarin aure na tambayeki ba, meye alaqar Omar da Hauwa?." Tayi shiru bata amsa ba ƙirjinta na bugawa. Baba ya ce, "ba magana akeyi miki ba ne?."
Salma ta ce, "Daman gaskiya Nayla ta jima tana son Omar, duk wannan damuwar da take shiga ana tambayarta meye taƙi faɗa duk akan sonsa ne. Amma babu wanda ya sani daga ni sai ita sai kuma Jidda." Hajja ta sauke numfashi bata ce komai ba cikin ruɗani. Abba ya ce, "iya son da take masa bai isa ace shine ya jawo ya aura mata shi ba, kodai akwai wata alaqa da ta taɓa haɗa shi da Nayla Salma?. Nayla ta bashi kanta ne?."
Salma ta wara idanu tana girgiza kai ta ce, "Wallahi Abba bata taɓa ba, ko magana ma basa yi wallahi, kuma bai ma san tana sonsa ba." Abba ya kafawa Salma ido yana kallo kafin ya ɗauke ido daga kanta. Hajja ta ce, "Bana wannan tunanin akan Nayla Ali, na san bazata taɓa watsar da kanta a waje ba, akwai dalilin mahaifinta na yanke wannan hukuncin ba iya dan tana sonsa bane."
Abba ya ce, "ni fa Hajja banga laifin da zata yi har ya saka shi ya yanke wannan hukunci akanta ba, dan tana sonsa ba hakan yana nufin zai aura masa ita bane, kawai yayi aiki da zuciya ne shiyasa hakan ya faru. Yazo a zauna gabaɗaya, dan gaskiya in akwai damuwa akan auren a saka yaron ya sake ta, bazai yu a cutar da ita dan mahaifiyarta bata raye ba."
Hajja ta ce, "yanzu ya ake ciki?."
"Ya ce zai zo har nan, wai kunyarki yake ji akan abinda ya aikata." Hajja ta ce, "to sai yazo, zan ji dalilinsa na yanke wannan hukunci. Dan Nayla na son Omar ba hakan yana nufin a aure mata shi gabagaɗi ba. Itama sanin akwai tazara tsakaninsu dashi ne ya saka ta ɓoye son da take masa. Ina da tabbacin babu wata mummunar alaqa da ta haɗa shi da Nayla, kamar yadda Salma tace ko magana na san basa yi. Inda ace wani abun ya faru tsakaninsa da ita sai ace shine dalilin Abdullahi, to ni na tabbatar da babu komai."
Salma ta kalli Hajja cikin rauni ta ce, "Hajja don Allah zan je Kaduna yau, Ina so naje naga halin da Nayla take ciki." Hajja ta ce, "kije ki shirya, sai a kai ki ai lokaci bai ƙure ba." Daddy ya ce, "in ta tafi ta barki da wa Hajja?."
Hajja ta ce, "ni kaɗai zan iya zama."
"A'a gaskiya, sai dai in zamu tafi gida tare dake, in yaso duk lokacin ta dawo sai ki dawo."
Hajja ta ce, "to me zai ci ni dan na zauna ni kaɗai? Naga Salma nan gaba kaɗan aure zata yi ko?. Kuma ko bata yi aure ba takardun makarantarta na fitowa aiki zata fara, gwara na fara sabo da zama ni kaɗai ɗin." Abba ya ce, "duk tarin ƴan matan da muke dasu? Ai sai wacce ki ka ce kina so tazo ta zauna da ke Hajja. Amma yanzu indai har zata je Kaduna to sai dai ki bar gidan nan gaskiya." Hajja ta yi shiru kawai bata ce komai ba tana tunanin wanne irin hukunci Abiy ya yanke haka?.
Salma dai kaya ta haɗa har na kwanaki ta ɗauki duk abinda ta san zata ɗauka ta fito. Tana fitowa aka kira mata drivern Hajja ya tabbatar da motar
lafiyar lau ta yi musu sallama ta fita dan gabaɗaya hankalinta yayi kan Nayla, so take taji abinda ya faru ta kuma ga halin da yake ciki.
[24/09, 3:38 pm] +234 906 075 3382: KRB2P024
ArewaBooks@nanahaleema11.
Tafiyar Salma ba jimawa Didi tayi sallama ta shigo falon Hajja. Hajja ta amsa da murmushi ta ce, "Aisha sannu da zuwa." Didi ta ƙaraso ta durƙusa ta gaishe ta amsa ta ce, "ya mai gidan naki?."
"Lafiya lau Hajja. Ina Salma?." Didi ta ce, "Salma ta tafi Kaduna wajan Nayla ɗazu. Kin san ta koma jiya." Didi ta ce, "Allah sarki, Allah ya kiyaye hanya."
Hajja ta ce, "Amin. Kin yi sa a AbdulHamid baya yi miki kulle yana barin ki fita, in ba haka ba ranar juma'a ma fa kinzo." Didi tayi dariya ta ce, "dole ce ta saka ni na fito yau ɗin ma Hajja." Hajja ta ce, "Amma dai lafiya ko?." Didi ta ce, "eh lafiya zance, nazo wajan Omar ne na tarar baya nan, gidan ma a kulle yake shiyasa zan zauna a nan na jira shi." Hajja tayi murmushi ta ce, "Malam Omar kenan, carbin ƙwai janka sai mai nutsuwa."