← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 52

Sashe 33

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta ce, “Nayla kar ki ji tsoro mahaifinki ne, ki faɗa masa abinda yake zuciyarki.” Nayla ta kalli Mama ta sake kallon Abiy ta sunkuyar da kai tana ajiyar zuciya. A kasalance ta ce, “Abiy…” Sai ta kasa ƙarasawa ta sunkuyar da kai. Abiy ya sauke numfashi ya ce, “faɗi ina jinki.” Mama ta kalle shi ta ce, “tana jin nauyin ka sosai, ka bari na tambaye ta zata fi sakewa ta faɗa min.” Abiy ya kalli Mama ya ce, “ni baƙonta ne da take jin nauyina?.”
“Amma ka san maganar aure ce, dole zata ji nauyi sosai.” Abiy ya ce, “to ki tambaye ta sannan ku dawo tare.” Mama ta miƙe ta riƙe hannun Nayla suka shiga ɗaki.

Suna shiga dakin Mama ta kalli Nayla ta ce, “Meyasa kike jin tsoron faɗar abinda yake zuciyarki ne? Na faɗa miki kar ki ji tsoro Ina tare da ke amma kin ƙi ji ko?.” Nayla ta ce, “nauyin Abiy nake ji, kuma sai nake ganin kamar bazai ji daɗi ba.”
“Baki yarda dani ba ne?.”
“Na yarda Mama.”
“To ki faɗa masa ke Omar kike so, shine wanda ki ke burin aure.”
“To Mama, Allah ya sa na iya.”
“Zaki iya. Indai da gaske kina sonsa zaki iya, ki rufe ido kar ki kalli idon mahaifinki, ki saurare zuciyarki duk abinda yazo zuciyarki kawai ki furta.”

Nayla cikin gamsuwa da ƙarfin guiwa ta ce, “To Mama zan yi.” Mama ta ce, “nutsu ki biyo ni” ta faɗa. tana fita ta bar Nayla. Nayla addu’a ta fara yi a zuciyarta sannan ta fito ta samu Mama a zaune inda ta tashi itama taje ta zauna inda ta tashi. Abiy ya kallli Mama ya ce, “me ta yanke?.” Mama ta kalle shi ta ce, “Omar ɗin dai.”

Abiy ya kalli Nayla bayan ya ɗan ɗaure fuskq ya ce, “Nayla bani amsa.” Nayla ta rufe ido kamar yadda Mama tace, ta yi shiru tana sauraron bugun zuciyarta sannan ta ce, “Eh Abiy. Shi nake so kuma shi nake so na aura.” Shiru tayi kuma bata buɗe idon ba. Jin shiru yayi yawa ya saka ta buɗe ido taga yadda Abiy ya kafa mata ido yana kallo ko kiftawa baya yi. Ajiyar zuciya yayi ya tashi zaune sosai ya haɗe hannayensa waje ɗaya ya ce, “Omar ɗin Kano kike so ko?.” Ta sunkuyar da kai tare da ɗaga kai alamun eh.

“Faɗa min meye sana’arsa?.” Nayla tayi shiru bata ce komai ba. Abiy a kausashe ya ce, “kar na sake tambayar ki kiyi min shiru!.” Nayla ta gyara zama cikin rauni da sanyin murya ta ce, “ance yana sana’a yanzu.”
“Okay, da fa?.” Nayla ta diririce sosai a raunane take magana ta ce, “ban sani ba Abiy.”

Abiy ya ce, “Faɗa min aikin da ke kika san yana yi.” Nayla saboda tsoro har zufa take yi duk da sanyin a.c da yake tashi a falon, ta ce, “ban san yana ko wanne aiki ba.” Abiy ya ce, “yanzu in kika je neman sa unguwar su Hajja wanne suna za’a faɗa da za a gane shi?.” Nayla ta ce, “Tiger.”
“Meyasa ake ce masa Tiger?.”
“Saboda ɗan daba ne.”
“Meye aikin ƴan daba?.” Tayi shiru bata amsa ba, cikin tsawa Abiy ya ce, “ba magan nake miki ba!?.” Nayla ta tsorata ta ce, “ɗaukar wuƙaƙe.”

“Su yi me da wuƙar in sun ɗauka?.” Nayla hawaye ya sakko mata cikin muryar kuka ta ce, “su yanki mutane.”
“Ko su kashe su ko?” Ya tambaya yana tsare ta da idanu. Ta ɗaga kai alamun eh. Numfashi ya sauke ya kalle ta yayi shiru zuwa wani lokaci kafin ya ce, “duk da tarin abubuwan nan da kika faɗa a kansa kike iya kallona kina cewa kina sonsa Nayla?.” Ta sunkuyar da kai tana goge hawaye cikin karayar zuciya.

Abiy ya canja murya zuwa tausasawa ya ce, “Akwai abinda na rage ki dashi a gidan nan?.”
“Babu komai Abiy.”
“Meyasa kika sake maimaita min kina son ɗan daba Nayla?.” Muryarta fara rawa sai ta kasa magana ta fara kuka sosai. Abiy ya ce, “Nayla! Daga yau, daga yanzu, daga wannan lokaci kar na sake jin kin furta wannan maganar, in har na isa dake kar na sake ji kince ke shi kike so in ba haka ba wallahi zaki dana sani a cikin rayuwarki. Sannan ki yi gaggawar mantawa dashi kafin na saɓa miki. Zan iya ɗaukar ko wanne shirme amma banda wannan, zan iya baki aure mai gadin gidan nan amma banda shi.”

Kuka take yi bata iya cewa komai ba. Abiy ya fusata matuƙa ya ce, “akan sa ki ke kuka!? A kansa kike zubar da hawaye!?.” Nayla ta girgiza kai alamun a’a tana kuka.
“To kiyi shiru ki goge wannan hawayen.” Da sauri ta goge idanunta jikinta har rawa yake yi dan bata da tsawar abiy ba.

Abiy ya ce, “inda ace mutum ne gari na sai na amince miki ki aure shi, inda mutum ne kamar kowa sai amince miki, inda mutum ne mai hankali da ɗabi’a mai kyau sai na amince miki. Amma bazan aurar dake ga namiji irin sa ba, in ma kina wannan mafarkin ki daina, dan baza ki aure shi ba sai dai in bani da rai!!.”

Abiy ya sake cewa, “Dan haka ki goge labarinsa a zuciyarki shine kwanciyar hankalinki kin ji ko?.” Ta ɗaga kai alamun to tana share hawaye. Abiy ya kausasa murya ya nuna ta da yatsa ya ce, “gargaɗi na ƙarshe Hauwa, wallahi kar na sake Jin wannan maganar a bakinki, in dai na isa dake ki ajjiye batun nan, in kuma ban isa dake ba na sake jin wannan maganar Nayla!.”

Nayla tana kuka ta ce, “bazan sake ba Abiy, bazan sake ba. Ka yi haƙuri. Nima ban san na fara sonsa ba, ban san ina sonsa ba. Wallahi Abiy da zan iya mantawa dashi da tuni na manta, na kasa Abiy, na kasa mantawa!” Ta faɗa cikin fitar hankali ta manta ma abinda take cewa.

Zuba mata ido yayi jin abinda take cewa kafin ya ce, “kina faɗa min kin kasa mantawa dashi ni kuma nace ki manta dashi Hauwa! Dole ki manta dashi, ko kina so ko bakya so. Ba sa’an aurenki bane, ba daidai yake yake ba, rayuwarsa da taki ba iri ɗaya ba ce!.” Sai da ta firgita jin tsawar da Abiy yayi mata ta sake fashewa da kuka cikin ƙunar zuciya da tsoro.

Abiy ya tausasa murya ya ce, “ki daina kuka, ki tashi ki bani waje, kije ki cigaba da addu’a Allah ya cire miki shi daga zuciyarki. Sannan ki tabbatar da kin fitar da wanda kike so in ba haka ba wallahi zan bayar dake ga wanda na ga dama.” Kuka take yi har lokacin cikin wani yanayi da bata san na meye ba. Abiy ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita sai ransa ya sosu yaji kamar tausayinta, ya san bai saba yi musu tsawa ba dole ta yi kuka tunda bata saba ba, yayi tsaki ya kalleta ya ce, “tashi ki bani waje.” Da sauri ta miƙe ta fita daga falon a guje har tana tuntuɓe.
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P019

Da kallo Abiy ya bita har ta fita yaja dogon tsaki cikin ɓacin rai ya ce, "wai tana sonsa, kuma bai ma san tana yi ba. Mtsw! da gaskiyar Senator da yace asiri yake yi, nima gashi ya yiwa tawa ƴar. To in ba asiri ba me zai kai Nayla ta ce tana sonsa?. Sai yanzu naji irin abinda Sagir yaji a lokacin da yaje gidansa ya ce yana son Narma. Ashe abun akwai ciwo da ƙunar rai, amma a lokacin da ya faɗa min ɗauka nake rashin haƙurinsa ne kawai." Mama da take gefe ta ce, "ni babban tashin hankalina ma kar ta aikata wani abu wallahi, yanayinta da maganarta kawai zaka ji ka san bata haƙura dashi ba."

Abiy ya ce, "babu abinda zatayi. Kuma da ace yana da halayya mai kyau da background mai kyau me zai hana a bashi ita tunda tana so? To bashi da shi, taƙadarin ɗan daban ne lamba ɗaya wanda ake jin tsoronsa a ko ina, ko meye abin so a wajansa oho."
"Ai ko yana da hali mai kyau meye amfanin bashi aure? Babu wanda ya san asalin su fa, su biyu kawai suke rayuwa. Ga samarin da suka kasance daidai da ita shi ɗin banza? Don Allah ka daina wannan maganar raina ɓaci yake yi."

Abiy ya sauke zuciyar ya ce, "kawai ku fara shirye-shiryen biki, dan bazan sake bata Lokaci ba a wannan karon, zan aurar da ita kawai. Da zarar ta san ta yi aure ai baza ta sake ambatar sunansa ba." Mama tayi ajiyar zuciya itama kafin ta ce, "Allah sarki, amma tana sonsa da gaske." Abiy ya kaawar da kai bai ce komai ba amma zuciyarsa gabaɗaya babu daɗi. Bai saba yiwa yaransa faɗa ba, bai saba saka su kuka ba shiyasa da ya ga Nayla tana kuka sai ya ji zuciyarsa babu daɗi gabaɗaya.

Mama wajan Nayla ta shiga ta same ta a zaune tayi tagumi amma ta daina kukan. Mama ta zauna a gefenta cikin rarrashi ta ce, "Nayla kar ki damu da faɗan da Abiy yayi miki, zai dawo daidai." Nayla a sanyaye ta ce, "ni na haƙura Mama, zanyi abinda Abiy yake so." Mama ta ce, "baza ki haƙura ba, na faɗa miki sai kin samu cikar burin ki tare da amincewar mahaifinki. Abinda nake so dake kawai ki kwantar da hankalinki, ki  cigaba da harkokin ki zan san abinda zan yi."
"Mama Abiy yayi fushi, kina ganin Abiy dai faɗa yake yi min abinda baya yi, ni na haƙura kawai. don Allah Mama ki bashi haƙuri ki faɗa masa da gaske na manta da wannan batun har abada."
Chapter 33 · 0% Book details