Sashe 35
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da hanzari ta koma ciki ta ɗauki waya hannuta na rawa ta kira Abiy yana ɗauka ta ce, "Abiy Nayla na cikin damuwa, Nayla tana cikin damuwa tana ta maganganun cewa in ba a barta aurensa ba zata iya kashe kanta. Don Allah ka dawo."
"Mtsw ƙyaleta, babu abinda zata iya,
In na dawo zamu yi magana" yana faɗa ya yanke wayar Mama tayi murmushi ta ce, "Bye bye Nayla" ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "mu jira dawowar Abiy."
••••••••
Nayla sai bayan la'asar ta shiga gidan Hajja, Baba Salisu ya sauketa ta shiga cikin gidan da sallama. Salma na ganin ta miƙe ta ƙaraso ta rungumeta tana cewa, "Oyoyo Nayla, sannu da zuwa." Nayla ta ɗaga kai ta ce, "Salma bani ruwa na kaiwa Baba ya sha." Amsawa tayi Salma ta fita da kanta ta kaiwa Baba ruwa sannan ta dawo ta zauna.
Nayla ta kalli Salma ta ce, "bara na yi sallar la'asar." Ɗaki ta shiga tayi wanka tare alwala tayi sallah ta canja kaya zuwa marasa nayi ta fito. Baba Salisu ta tarar yana gaisawa da Hajja sannan ya yi mata sallama ya koma Kaduna.
Nayla ta kalli Hajja ta ce, "Hajja Ina yini."
"lafiya lau Hauwa, ya jikin naki?."
"Da sauƙi" ta faɗa a sanyaye kai da ka ganta ka san bata cikin nutsuwarta. Salma ta kalleta ta ce, "Me ya faru na ganki katsam haka? Kuma gobe juma'a akwai aiki?." Nayla ta girgiza kai ta ce, "bani da lafiya ne bana zuwa ma aikin Kwana biyu, Nazo nan na huta, in na huta sai na koma."
Salma ta ce, "amma ana ganinki a san akwai damuwa a lamarinki." Nayla tayi ajiyar zuciya ta ce, "babu komai" ta faɗa tana tashi ta shiga ɗaki. Hajja ta ɗaga murya ta ce, "baza ki ci abinci ba?." Daga ɗakin ta ce, "azumi nake yi."
"Kina azumi ki ka yo tafiya Hauwa?" Hajja ta faɗa amma Nayla bata amsa ba. Hajja ta kalli Salma ta ce, "me yake damun Nayla ne haka?:"
Salma ta sauke numfashi ta ce, "bara ta huta yau sai ta faɗa min abinda yake damunta, bara na bata lokaci ta samu hutu." Hajja ta ɗaga kai kawai bata ce komai ba amma zuciyarta na faɗa mata akwai wani abun da yake damun Nayla.
A can Kaduna sai bayan sallar i'sha kamar ko yaushe suna zaune an gama cin amma babu Nayla. Abiy ya kalli Jalil ya ce, "jeka ka kira min Yayarka Nayla." Da sauri ya tashi ya hau sama zuwa ɗakinta, ba jikawa ya dawo ya ce, "Abiy bata nan." Abiy ya ce, "bata nan kuma?" Ya faɗa yana kallon Mama. Mama ganin yana kallonta sai ta ce, "tun ɗazu ban shiga ɗakinta ba ban san ita take ba, tun lokacin da muka yi waya da kai ban sake shiga wajanta ba gaskiya."
Jalila ƙanwar Nayla da ta shigo falon a lokacin ta ce, "A'a Mama ni ɗazu naga Anty Naya ta shiga motar Baba Salisu fa, na kuma ganta da jaka a hannunta na ɗauka ma kano ta tafi." Mama ta ce, "jaka kuma? Nayla ɗin?."
"Eh Mama." Abiy bai ce komai ba ya ɗauki waya ya kira Baba Salisu nan yake tabbatar masa da ya kai Nayla Kano.
Mama ta ce, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ba dai maganar da ta faɗa ɗazu ta aikata ba? Na shiga uku, daman tace zata bar gidan nan in dai ba a yi mata abinda take so ba kuma baza ta sake dawowa ba" ta faɗa hannu na rawa tana kiran wayar Nayla. Da yake a speaker ta saka kowa yana jin lokacin da wayarta ce baza ta shiga ba.
Yaya da ya shigo a lokacin yaji abinda ake faɗa ya ce, "Wai Nayla ce ta bar gidan nan saboda ɗan daba?." Mama ta ce, "ta tafi Kano ba tare da sanin mu ba gabaɗaya, Allah ya sa tana lafiya." Abiy dai ya kasa magana ya yi shiru bai ce komai ba dan bai san me zaice ba, zuciyarsa zafi take yi akan abinda Nayla ta aikata wanda bai taɓa tunanin zata yi ba. Ƙarar shigowar message yaji a wayarsa, ya ɗauki wayar ya duba yaga ta Whatsapp ne kuma sunan Nayla. Da sauri ya bue yana karanta abinda ta rubuto masa a zuciyarsa.
Abiy ajiyar zuciya yayi bayan ya gama karantawa yayi shiru na wani lokaci. Kallon Jawad da Ahmad yayi ya ce, "Gobe da safe kuzo zaku raka ni wani waje, amma kuzo da wuri ina so mu isa kafin lokacin sallar juma'a" Abinda yace kenan kawai ya miƙe ya shiga ɗaki zuciyarsa cike da ɓacin ran abinda Nayla tayi masa.
Da sauri Mama ta bi bayan sa ta ce, "Abiy me ya faru?."
"Babu komai, ki bani waje zan huta."
"Ka gwada kiran Nayla ko zaka same ta, Ina so na tabbatar da tana lafiya." Cikin tsawa Abiy ya ce, "nace ki bani waje ko!?." Da sauri ta fita daga ɗakin ya kulle ƙofar.
Bayan fitar Mama waya ya ɗauka ya saka a kunne ya ce, "zan turo maka sunan wani yaro a nan cikin Kano unguwar ƙofar nasarawa, ka tabbatar a daren nan ka nemo min waye shi" yana faɗa ya yanke wayar ya cillar da ita a kan gado zuciyarsa na yi masa zafi.
Babu abinda ya ɓata masa rai a abinda Nayla ta turo masa kamar da tace tayi zata iya barin kowa saboda Omar, In ya tuna irin kalaman da ta yi amfani dasu wajan a saƙon da ta turo masa sai yaji kamar ana soka masa kibiya a zuciyarsa saboda ɓacin rai da baƙin ciki da takaici.
Ranar a gidan gabaɗaya kowa zuciya babu daɗi, Mama ce kawai take farin ciki amma dukkan su babu wanda yaji daɗin abinda Nayla tayi.
Washe gari.
Wai me Nayla ta aikata ne? Wanne irin saƙo ta turowa Abiy haka? Ina su Abiy zasu je?......A kafta💃🏻
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P020
Arewabooks@nanahaleema11
Ƙarfe takwas na safiyar ranar juma'a Abiy ya sakko daga sama yana ɗaura agogo a hannunsa. A ƙaramin falon ƙasa ya tarar da Mama ta kalle shi ta ce, "Ina zuwa haka da sassafe? Kun yi magana da Nayla kuwa? Ina kiranta har yanzu bana samu." Abiy ya kalle ta ya ce, "ba mu yi waya ba, bana buƙatar yin wayar da ita. Ina su Jawad?." Mama ta ce, "suna main parlor tun ɗazu." Abiy bai ce komai ba ya wuce zuwa falon.
Yana shiga duk suna tashi suna kallon sa suka gaishe shi ya amsa kana ya ce, "Ku zo mu je." Ba musu duk suka bi bayan sa. Jawad ya shiga mota mazaunin driver Abiy ya shiga baya Yaya ya zauna a gaba suka fita daga gidan. Sai da suka hau titi sannan Jawad ya ce, "Abiy ina zamu je."
"Kano" ya bashi amsa ba tare da ya kalle su ba. Basu tambaye shi ba kawai Jawad ya ɗauki hanyar fita daga Kaduna.
Nayla kuwa a lokacin idanunta biyu ta kasa komawa bacci, ganin ƙarfe tara na safe tayi sai ta miƙe tayi alwala ta tayar da sallar walha. Sai da tayi raka'a ashrin sannan tayi addu'a zuwa lokacin har goma na safe ta kusa. Wayarta jawo dan tun jiya bata duba ba ta shiga WhatsApp ɗinta. Abin mamaki an yi hacking account ɗinta, tsaki tayi ta fita ta shiga Google ta duba yadda zata dawo da account ɗin tana karanta yadda zata bi ta dawo dashi.
Salma ce ta shigo hakan ya saka ta ajjiye wayar ta ce, "wai WhatsApp ɗina aka yi min hacking." Salma ta ce, "ai zaki iya dawowa dashi ba wahala ne dashi ba, ki dai yi gaggawa kar a fara tambayar mutanen contact ɗinki kuɗi." Nayla ta ɗauki wayar ta ce, "bara na gani" ta faɗa da tana bin steps ɗin da ta gani a google har ta dawo dashi. Tsaki tayi ta ce, "ikon Allah, an goge min wasu messages ɗin, suka sani dai" ta faɗa tana ajjiye wayar a kusa da ita.
Kallon Salma tayi da take kallonta sai ta ce, "yaushe zamu je gidan Didi? Ina so naje kafin na koma Kaduna." Salma ta ce, "sai muje anjima in zaki iya. Amma kafin nan Nayla me yake damunki?." Nayla ta ce, "Salma nima bana ce ba wallahi, komai baya yi min daɗi. Babban abin tashin hankalin ma Abiy ya san maganar Omar." Zaro ido Salma tayi ta ce, "mun shiga uku! Kamar ya ya sani? Ta wacce hanya ya sani?."
"Ashe lokacin da muke maganar nan a gidan mu na Kano Mama taji. Mama tana goyan bayana akan soyayyata dashi, hakan ya saka ta sanar Abiy shi nake so ko zai amince. Hmmm Salma! Abiy bai taɓa yi min faɗa kamar lokacin ba, kai tsaye ya ce min Hauwa sunan da bai taɓa faɗa ba."
Salma ta dafe ƙirji ta ce, "Innalillahi wa'jnna ilahir raji'un!. Yanzu ya ake ciki?."
"To bana ce ba dai, ya ce dai duk yadda zan yi nayi na fitar da mijin aure in ba haka ba zai bani wanda ya ga dama. Daman na san bazan taɓa mallakar abinda nake so ba Salma, shiyasa ni zan bawa Abiy haƙuri ya zaɓa min duk wanda ya ga dama. To Mama ce take bani bani ƙarfin guiwar zai iya amincewa da Omar."
Salma ta ce, "Gaskiya Abiy bazai amince da Omar ba, gwara ma ki daina yaudarar kanki. Duk dani shaida ce Omar ba kamar da ba yake ba yanzu ya canja, harkar sana'arsa yake yi kuma Allah ya saka masa albarka. Ke in kika ga takalman da Omar yake yi sai abin ya baki mamaki, sai kin ce daman yana da wannan talend ɗin ya zauna yana ɓata rayuwarsa a banza da wofi.....huhh amma duk da haka rayuwarsa ta baya zata saka a ƙi bashi aure Nayla. Musamman auren irin ki, mai ilimi, nasaba, kyau da sauran su."