← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 52

Sashe 52

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Omar ya yi shiru tare da yin ajiyar zuciya ya ce, "aure dai, kuma dani. To akan me? Meyasa sai ni?." Daddy ya ce, "na faɗa maka tun farko, ɓacin rai ne ya jawo mahaifinta ya aikata hakan, yanzu zaman da muka yi akan mafita ne."

Shi wallahi har lokacin bai gamsu sosai ba shiyasa hankalinsa bai wani tashi ba, to haka kawai za a tara mutane ace wai ga matarsa an ɗaura masa aure tun waccan juma'ar? Hauka yake yi da zai amince da wannan wasan yaran?.

Didi ta fahimci bai yarda ba har lokacin hakan ya saka ta ce, "Omar kalle ni." Ba musu ya kalleta ta ce, "ka daina jin abin kamar ba gaske ba, da gaske an ɗaura maka aure tun waccan juma'ar, ni shaida ce dan har goron daurin aurenka na saka a bakina na tauna. Ka san bazan maka ƙarya ba, Wallahil azim Nayla matarka ce tun kwana bakwai da suka wuce."

Sai a lokacin ya dawo hayyacinsa, ya zubawa Didi firgitattun idanunsa cikin kakkausar murya ya ce, "Akan me? Wacece Nayla? Meyasa sai ni, Meyasa baki faɗa min tun ranar ba!?" Ya faɗa cikin murya mai amon gaske.

Didi ta ce, "ka nutsu kar ka...." Katseta ya yi ya ce, "bazan nutsu ba, bazan nutsu ba Didi!. Kin san da wannan maganar ki ka ɓoye min? Kin san da wannan abin ki ka bari har aka kai yanzu ban ɗauki mataki ba?." Daddy ya ce, "Omar ka nutsu mu yi magana duk akan hakan aka taru."

Kallon Daddy ya yi ya ce, "abinda ya ɗaure min kai akan me aka yi haka? Saboda ran mahaifinta ya ɓaci kawai sai a ɗaura min aure da wacce ban sani ba?. Auren hukunci ne a gareta kenan? Hukuncin ɓatawa mahaifinta ran da tayi ko me ye?. In hakan ne kenan ni ne ƙarshen hukuncin da za a yi mata ranta ya ɓaci ko a ƙunatata mata tasan ta yi laifi kenan?" Ya sake kallon Didi ya ce, "kuma wai kin san da wannan maganar amma ki ka kasa faɗa min har aka zo yanzu ban sani ba. Su waɗanda aka ƙulla abin dasu sun san ai nafi ƙarfin hakan, shiyasa aka yi ba tare da na sani ba. Babban abin haushin ma da aka haɗa kai dake aka munafurce ni Didi.......!" Ya ƙarasa faɗar maganar a hankali yana zazzaro idanunsa waje.

Didi ta ce, "kaga Omar ka tsaya ka ji abinda za a ce maka mana, ka yi shiru baka ganin manya ne a gabanka?."

"Sanin su ɗin ne a gabana ya saka nake wannan maganar, tunda na shigo girman su da kwarjininsu ya cika min ido, a karo na biyu a rayuwata da naga wanda nake jin girmansu a idona tunda nazo duniya, in ba dan haka ba babu yadda zan yiwa magana. Aure Didi? Na ce miki ina son aure ne? Ko na ce miki Ina buƙatarsa nan kusa?. Ya muka yi dake? Bana faɗa miki ko da wasa kar kiyi wannan gangancin ba?." Didi ta dafe kai ta rasa abinda zata ce, gashi ta san in bata katse shi ba wallahi zai yi abinda bazata daina jin kunyarsu Daddy ba har abada.

Daddy da yake kallon Omar ganin yadda yake zarewa Yayarsa ido sai yayi murmushi yana girgiza kai ya ce, "mu ne iyayen yarinyar da aka ba ba, duk da mahaifinta baya wajan nan amma mu ma iyayenta ne. Shiyasa muka zauna a nan domin ka san da auren ka kuma tsayar da matsaya akan auren." Abba ya ce, "mu ma duk ba mu ji daɗin hakan ba, yadda ka ke ji ba a kyauta maka ba haka muke ji, itama yarinyar haka taji a ranta, amma babu wanda zai yi kokawa da ƙaddara a cikin mu, yadda Allah ya rubuta sai ta zama matarka sai ta zama koda na kwana ɗaya ne. Don haka yanzu me ka yanke?."

Omar kai tsaye ya raunana murya ya ce, "bana so! Ni ban san ma yarinyar da ake magana a kai ba dan haka bana so. Daman munafurta ta aka yi aka ɗaura auren, to yanzu na sani kuma ban karɓa ba!." Daddy ya ce, "ka tabbatar da hakan?." Kamar ya yi tsaki amma sai ya fasa, wai ya tabbatar da hakan, kamar shi ake yiwa wannan tambayar tsabar rainin hankali.

Mama su Jidda sai a lokacin tayi magana ta ce, "a dai bi komai a hankali." Mama Sa'adatu ta ce, "babu zancen abi komai a hankali Maman Jidda, tunda baya so kawai a datse auren yanzun nan."

Ta kalli Omar ta ce, "kawai ka saketa!." Babu ɓata lokaci Omar ya buɗe baki zai yi magana......!

End of book 2

Book 2 ya ƙare a nan. Ya ku ke ganin lamarin zai kasance? Omar zai amince da auren nan ko a'a? Zai saki Nayla ko zai zauna da ita? In ya zauna da ita zata ji daɗin zaman aure dashi kuwa? Zai kyautata mata ko burin Mama zai cika?. Me ya haɗa Omar da ahlinsu? Ina labarin Narma? Omar zai aureta ko ya ya?. Ko baki karanta book 1&2 ba ina baki shawara ki karanta book 3, ya tara abubuwa da yawa a cikin wanda zai saka nishaɗi da farin ciki.

Sai mun haɗe....❤️❤️❤️
Chapter 52 · 0% Book details