← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 52

Sashe 32

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“In da ace ya dace ya kuma cancanci ya zama mijinki zan iya amince miki, amma yanzu ki adana kalamanki bana son sake jin magana irin wannan daga cikin gidan nan, ki ɗauka baki san shi ba, ki kuma manta dashi a cikin zuciyarki. Kin ji abinda na ce ko?.” Nayla ta ɗaga kai kafin ta ce, “Naji abiy, zan yi in sha Allah.”
“Yafi miki” yana gama faɗar hakan ya fita daga ɗakin ya barta a ita da Mama.

Mama ce ta riƙeta ta miƙar da ita tsaye ta ce, “ki kwantar da hankalinki komai zai zama daidai nayi miki alqawarin hakan, kar ki damu da kalaman mahaifinki zan san yadda zan yi ya sakko ya fahimce ki.” Nayla ta ce, “Mama kawai ki ƙyale shi, ni daman sai da nace tsoro nake ji kar a faɗa masa kika ce a faɗa masa, kinga ransa ya ɓaci yanzu ni kuma bana son hakan. Don Allah ki ƙyale shi kawai Mama ni na haƙura, zan ɗauki mutum ɗaya a cikin waɗancan kawai na huta.” Mam ta ce, “kar ki cuci kan ki, kar ki cutar da zuciyarki saboda faɗan mahaifinki na yanzu. Zai sakko na yi miki wannan alqawarin, zai amince da auren ki da Omaar kar ki damu.”

Nayla dai hawaye take gogewa tana ji zafi a zuciyarta da ta fara son wanda soyayyar sa bata da wani amfani a gareta da cikin rayuwarta baki daya.

Mama fita tayi zuwa wajan Abiy ta same shi a zaune da alama har lokacin ransa a ɓace yake sosai ta zauna ta ce, “Lamarin Nayla ya fara bani tsoro wallahi, da gaske sonsa take yi fa. Ka ji irin kalaman fitar hankali da take faɗa bayan fitar ka? Ita sai ta aure shi, shine farin cikinta, kalamai dai barkatai. Allah ya kawo mana mafita a wannan lamari kawai.”

Sake tunzura zuciyar Abiy Mama tayi ya yi ƙwafa ya ce, “Ashe da gaskiyar Senator Sagir da ya ce na bincika anya nima bai yiwa Nayla asiri ba, a lokacin sai nake ganin ba haka bane ashe da gaske dai asirin yake yi, tunda ga Nayla ma tana neman fita daga hankalinta saboda shi.”

Mama ta ce, “ni wallahi gani nake ba wani asiri da yake yi, kawai zuciyarsu ce bata yi musu adalci da take fara son wanda bai kamata ma ace ta so ba. Ɗan shaye-shaye, ɗan daba, karen ƴan siyasa, wanda ya yi zaman prison, abubuwa da yawa marasa daɗi akan mutum meye abin so a wajan?. Allah yasa kar ya shirya ya ɗauko ƙafa yazo yace yana son Nayla.”

Abiy ya yi shiru kawai amma gabaɗaya zuciyarsa bata yi masa daɗi, sam bai ji daɗin kalaman Nayla akan tana son Omaar ba. Meye abin so a Omar don Allah? Me yake dashi da har Nayla ƴar cikin sa zata ji tana so duk wannan tarin abubuwa marasa kyaun da suke dabaibaiye shi?. Tsaki Abiy yayi ya sauke numfashi ya kulle ido amma bai ce komai ba. Mama ta ce, “Ashe daman yawan zuwa Kanon da take yi duk saboda shi ne, wallahi ƙunar abinda nan nake ji har zuciyata. Inda mutum ne na gari ma da sauƙi, amma irin wannan ɗan iskan garin meye amfanin son sa?.”

Abiy nan ma bai ce komai ba amma kalaman Mama tuna masa wasu abubuwan suke yi musamman yawan san zuwa Kano da Nayla take dashi, bai taɓa kawo haka a zuciyarsa ba amma yanzu ya kawo hakan ya kuma tabbatar da saboda shi take zuwa Kano a kai a kai tunda maƙocin Hajja. Girgiza kai ya yi kawai ya tashi ya barwa Mama wajan gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi.

Mama ta yi murmushi ta ce, “Ai indai Ina nan sai Nayla ta auri yaron nan, a gaban idonka Ina tare da kai, amma a bayan idonka ni ce zan dinga zuga Nayla akan Omar. Haba ai dole ma ta aure shi hakan shine zai saka ni farin ciki da kwnaciyar hankali a zuciyata. Ko babu komai na san zata je inda bazata taɓa farin ciki ba a rayuwarta, tunda baya sonta itace take sonsa kuma ga yanayin halayyarsa komai zai iya faruwa” ta faɗa tana murmushi cikin farin cikin cikar burita.

Nayla haka ta kwana ciwon kai saboda damuwa da kukan da tayi, da safe kasancewar Sunday ce babu aiki ta jima tana bacci sai sha biyu na rana sannan ta fito babban falo ta tarar da Jalil yana game a tv. A sanyaye ta ce, “Auta Abiy yana nan?.” Kai ya ɗaga mata ya cigaba da game ta nufi ɓangarensa.

Mama ta gani ta fito daga apartment ɗin Nayla ta kalleta ta ce, “Mama Ina kwana.” Da kallo ta bita kana ta ce, “Lafiya lau Nayla. Lafiya naga fuskarki ta kumbura? Kar ki ce min kwana ki ka yi kina kuka?.” Nayla ta sunkuyar da kai kafin ta ce, “Mama Abiy yana nan?.” Mama ta ce, “ya kwanta sai dai zuwa anjima. Zo mu je” ta faɗa tana jan hannun Nayla zuwa ɗakin ta.

Mama ta kalleta ta ce, “Nayla faɗa min kuka ki ka kwana kina yi?.” Nayla a sanyaye ta ce, “na dai yi kuka amma ba kwana nayi Ina kuka ba Mama.” Mama ta ce, “mahaifin naki ai ya fara sakkowa, shiyasa nake faɗa miki indai ina nan zan san abinda zan yi ya amince da auren ki da Omaar. Tunda yaron yanzu kince ya daina abinda yake yi ya kama sana’a hannu biyu, to meye aibu? Ai ba a tuna da abinda ya wuce abinda yake faruwa yanzu ake kallo. Yanzu kafin ya kwanta maganar mu ke yi yana tambayata da gaske kina sonsa, na ce kina sonsa mana shine ya ce yana so ya sake tabbatarwa daga bakinki, in kina sonsa sosai zai iya amincewa ki aure shi tunda kina so. Amma in bakya sonsa zai bari ki samu wanda ki ke so.”

Nayla ta kalli da sauri Mama ta ce, “Da gaske mama?.”
“Da gaske mana Nayla. Ke kin san Abiy yana matuƙar son farin cikinki, zai iya sadaukar da nasa farin cikin saboda naki farin cikin kawai. Dan haka ki daina damun kanki a hankali zai amince kawai ki bashi lokaci. Sannan in ya sake tambayarki akan Omar ki tabbatar masa da Omar shine rayuwarki, rasa Omar daidai yake da rasa ranki. Na tabbatar yana jin haka zai amince miki ɗari bisa ɗari.”

Nayla ta ce, “Amma Mama sai nake ganin kamar bazai amince ba. Ni na haƙura wallahi, daman shi ma bai san Ina sonsa ba, bai san ina yi ba gwara na auri wanda suke sona da na auri wanda nake so shi ba sona yake yi ba. Ni kawai ki daina masa maganar,in ya tambaye ni zan faɗa masa sunan ɗaya daga cikin waɗanda ya ce na zaɓi mutum daya a cikin su.”
“Kar ki aikata haka, in kika aikata haka daidai yake da kin saka ƙafa kin yi fatali da farin cikin ki ne. Na faɗa miki Abiy yana son farin cikinki, zai iya yin komai saboda farin cikin ki meyesa ki ke haka? Ko baki yarda dani ba ne?.”

Nayla kamar zata yi kuka ta ce, “Mama in ban yarda dake ba da wa zan yarda?.” Mama ta ce, “to ki kwantar da hankalinki na faɗa miki zanyi duk abinda uwa take yi dan samarwa da ɗanta farin ciki a kan ki, haihuwar ki ce kawai banyi ba, amma ni na raine ki har kika kawo yanzu. Kedai ki bani haɗin kai ko me nace miki ki yi shikenan komai zai wuce. Mahaifinki zai daina fushi dake, kema zaki samu abinda kike so ba shikenan ba?.”

Nayla ta ɗaga kai ta ce, “To Mama, na yarda dake zan kuma yi duk abinda ki ka ce. Na gode Mamana, ina sonki.” Mama ta shafa fuskarta ta ce, “ai ba ke kika ɗorawa kanki soyayyar ba, Allah ne ya ɗora miki kuma shine zai yaye miki. Tunda har Allah ya saka miki soyayyarsa a zuciyarki wataƙila alkhairi ne ga rayuwarki, kar ki ji komai ki ɗauka kamar an yi an gama ne.”

Nayla ta rungume Mama itama ta rungume tana shafa bayanta ciki sigar rarrashi. Nayala gabaɗaya jinta yake wani iri, wani ɓangare na zuciyarta ya amince da maganar Mama wani kuma zuciyarta tana rawa a kai. Ta san Mama bazata cutar da ita ba amma ta rasa dalilin da ya saka zuciyarta take rawa akan kalaman Maman ta.

Nayla bata haɗu da Abiy ba sai yamma, ta same shi a falo a zaune dashi da yaye ta da ƙanenta. Abin mamakin bai nuna mata komai ba sun gaisa kamar ko yaushe, sai taji kalaman Mama sun samu gurbi sosai a zuciyarta, kamar yadda ta ce Abiy ya sakko kenan ya sakko ɗin tunda gashi sun gaisa hankali kwance bai yi mata faɗa ba bai kuma ɗaure fuska ba. Duk da dai walwalarta ta ragu sosai amma hakan yayi mata daɗi yana lura da yadda yake ta murmsmushi amma bai ce mata komai ba.

Abiy bai sake yi mata maganar ba sai ranar talata da daddare tana zaune a falo ita da Mama da Abiy tana cin abinci kasnacewar su Auta sun kwanta saboda akwai makaranta washe gari. Abiy ya kalle ta yana lura da ita cikin kwanakin gabaɗaya komai a sanyaye take yi, sannan bata da lafiya kawai dauriya take yi saboda shi.

“Nayla!.” Abiy ya kira ta yana kallon ta. Gaban ta ya faɗi ta ɗago ta kalle shi ta ce, “Na’am Abiy.”
Ya kalle ta sosai ya ce, “Ya maganar da mu kayi akan wanda zaki aura ɗin?.” Ta kalli Mama da take kallonta ta sake kallon Abiy ta ce, “Abiy duk abinda kace.”

“A’a abinda kika ce dai, faɗa min waye zaɓin ki?.” Nayla tayi ajiyar zuciya tayi shiru bata yi magana ba. Abiy ya bita da kallo kafin ya ɗauke kai ya ce, “ke nake jira.” Ta yi shiru ta kasa furta komai gabɗaya kwarjinin Abiy ya dabaibaiyeta.
Chapter 32 · 0% Book details