Sashe 25
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Narma tana shiga a kan gado ta zube tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciya, lokaci ɗaya kanta yayi nauyi sosai saboda ciwo idanunta suka tasa saboda kuka. Sai da tayi kukan mai isarta sannan ta tashi zaune tana sauke ajiyar zuciya. A sanyaye ta ɗauki waya ta nemo number Omar da tayi saving da my Faruk ta kira. Bata da tabbacin zai ɗauka ko bazai ɗauka ba, ta yi shiru tana jiran tsammani.
Ƙit taji ta katse alamun bai ɗauka ba ta ajjiye wayar a gefe tana kallon sunansa cikin bahagon yanayi. Kamar a mafarki sai ga kiransa na shigowa ta zabura ta ɗauki wayar hannu yana rawa ta kai kunnenta. Kafin ya yi magana ta ce, "Hello...hello...my Faruk kaine ka kira ni?......Wayyo Allah! yau ya kira ni, Allah na gode maka. My Faruk Ina kewar ka Ina so na ganka..." abinda take faɗa kenan a ruɗe kana ji kasan bata cikin yanayi mai daɗi.
Omar da yake jinta bai ce komai ba ta sake cewa, "My Faruk su Dad suna son kashe ni, wai sun ɗaura min aure da wani ba kai ba, mutuwa kawai zan yi....!" Ta faɗa cikin kuka mai ban tausayi. Omar ya lumshe idanu jin abinda ta ce, maganar tayi masa daɗi kuma bata yi masa daɗi ba. Ɓangare ɗaya yaji daɗin aurenta kodan ta daina takura masa ta daina damun kanta a kansa ta san ita matar aure ce. Ɓangare ɗaya kuma bai ji daɗi ba saboda tausayinta, ya san tana sonsa, aura mata wani a wannan yanayi bazai mata daɗi ba.
Narma ta ce, "ni da kai nake so na rayu, bazan iya rayuwa da kowa ba sai kai. Don Allah ka amince nazo na zauna da kai, ni kai kaɗai nake so nayi zaman aure dashi ba wani ba. In na zauna da Ashraf mutuwa zanyi! Bana sonsa, kai nake so da kai zan rayu......!"
"Narma! Ki nutsu" ya furta a hankali cikin murya mai taushi. Numfashi taja kamar ya saka mata pause ta dakata da kukan sai ajiyar zuciya da take yi. Ya sake cewa, "Kin ce an ɗaura miki aure ko?." Kamar tana gabansa ta ɗaga kai ta ce, "eh, amma bana sonsa, ni kai...." Dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa, "Matar aure ce ke, furta kina son wani ba mijinki ba babban laifi ne. Kina jina?."
"Ina ji" ta faɗa murya na rawa sosai.
"Waye ni a wajanki?."
"Wanda nake matuƙar so, wanda nake so na rayu dashi har a aljanna."
"Na isa nace ki yi abu ki yi? Na isa na ce ki bari ki bari?."
Narma ta ce, "har ka yi yawa ma Faruk! Har ka yi yawa wallahi. Zan iya sadaukar maka da raina da rayuwata." Ya ɗan yi jimm kafin ya ce, "to ki riƙe aurenki, ki yi abinda iyayenki suke so ki zauna da mijinki..." Katse shi ta yi ta ce, "Amma bana sonsa, bana ƙaunarsa ta ya zan iya zama dashi?."
Omar ya ce, "ki koya, ki koyi sonsa zaki iya. Ina faɗa miki gaskiya matsayina na Yayanki, in na ce miki Ina kallon ki matsayin wacce nazo gidan ku a matsayin mai sonki a yanzu ƙarya nake miki, gwara na faɗa miki gaskiya ki riƙe aurenki ki daina tunanina a cikin rayuwarki. Narma Allah bai rubuta ni da ke zamu zauna a inuwa ɗaya matsayin ma'aurata ba, ki karɓi ɗaddara hannu biyu Allah ne ya tsara ba ni ko ke ba. Iyayenki da kike gani kamar basu kyauta miki ba ba laifin su bane, babu ni a cikin rabon ki Narma, babu ni a cikin ƙaddararki saboda haka ki kwantar da hankalinki yi fuskanci rayuwa."
Narma hawaye take yi, ta san gaskiya yake faɗa mata amma zuciyar baza ta iya ɗaukar kalamansa ba, zuciyarta bugawa take yi sosai ta runtse ido tana jin kalamansa kamar saukar ruwan zafi a zuciyarta, ta wani ɓangaren kamar saukar ruwan sanyi a zuciyarta.
"Wataƙila akwai Omar a ciki rayuwarki ta gaba, wataƙla babu. Ni dake babu wanda ya isa ya amsa kiran rabon da ba na shi ba. Dan haka ki nutsu, ki riƙe aurenki ki daina tunawa da kin san mai suna Omar a rayuwarki. Ina yi miki fatan alkhairi da fatan samun rayuwa mai albarka" ya sake faɗa cikin taushin murya wacce take ratsa zuciyar Narma.
Kai take girgizawa tana hawaye ta ce, "A'a Faruk, kar kace haka don Allah, bazan iya rayuwa babu kai ba, Ina sonka, ina son rayuwa dakai. Na san kaina kana jin abinda nake ji, ka amince min kawai nazo na rayu dakai ta ko wanne hali."
"Matar aure ce ke, Zancen na amince dake bai tashi ba. Kuma ni babu abinda nake ji a kanki kema ki daina ji a kaina, Ki manta dani ki kalli rayuwar aurenki zai fi miki kwanciyar hankali. Indai da gaske zan saka ki abu ki yi kamar yadda kika ce to ki riƙe aurenki, ki kuma manta dani!."
Jin tana kuka mai sauti ya saka Omar ya ce, "Ina yi miki fatan alkhairi, sai anjima" yana faɗa ya yanke wayar ta kifa kai akan wayar tana kuka sosai. Sai da ta gaji da kanta sannan ta dakata, kanta ya riƙe sosai saboda kuka ta koma sauke ajiyar zuciya. Bata san haka soyayya take ba, bata san haka ake ji a soyayya ba, bata san haka azaba da raɗaɗin soyayya yake ba da bata yi gangancin fara son Omar ba. Numfashi take saukewa a hankali a hankali cikin rashin sanin abinda zata yi.
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P015
Arewabooks@nanahaleema11.
Tana ji ana buga ƙofar bata buɗe ba sai daga baya ta tashi ta buɗe, Najwa ta gani ta kalleta ta ce, "Ya ki shirya before magrib zaku wuce." Rungume Najwa tayi tana cewa, "Bana so Najwa! Bana son Ashraf, Ni Faruk nake so!. Ya zanyi? Ya ake so nayi da raina?." Najwa hawaye ya cika mata ido amma bata yi ba ta ce, "ki yi haƙuri." Ajiyar zuciya take yi a hankali kukan ma ya daina zuwa idanunta sai kanta da ya yi nauyi sosai.
Idanu a kulle ta ce, "Nayi magana da Faruk, ya ce wai na riƙe aurena na manta dashi. Hmmm ki ji fa Najwa, taya zan iya mantawa dashi? Shi ne wanda naso kuma nake so har yanzu. Ya kasa gane irin yadda nake ji a kansa." Najwa ta ce, "Gaskiya ya faɗa miki Ya Narma, mantawa dashi ɗin shine yafi alkhairi a gare ki da kuma shi kansa. Yanzu kina da aure ya zama dole ki manta dashi, addu'a zaki dinga yi a hankali komai zai wuce." Bata ce komai ba ta bar jikin Najwa ta koma ta zauna a gefen ta dafe kanta.
Najwa da kanta ta jawo trolly bag ya fara haɗa mata kaya a ciki. Komai da ta san zata yi amfani dashi ta zuba tayi zipping bag ɗinta ta ajjiye ta fita. Bayan sallar la'asar Najwa ta sake dawowa ta tarar ta idar da sallah kalle ta ta ce, "Ya Narma ki tashi ki shirya." Kallon Najwa tayi kamar zata yi magana sai bata ce komai ba, kalaman Omar ne suke yi mata yawo a zuciyarta. Mum da Dad suka shigo ɗakin a tare, Dad ya kalle Narma a tausashe ya ce, "Daughter ki tashi ki shirya zaku wuce America." Kallon Dad tayi da idanu ta da suke a kumbure ta ce, "Dad ka san bana sonsa ka ce na bishi ko?."
Dad ya ce, "Narma mun gama wanna maganar dake, kar ki sake dawo da ita please. Ni na haife ki fa Narma, bazan taɓa yin abinda zai cutar da rayuwarki ba. Duk duniya babu wanda ya kai ni sonki, Ina sonki, Ina son inganta miki rayuwarki. Kar ki dinga kawo tunani mara kyau a zuciyarki na tabbatar da komai zai wuce nan da lokaci kaɗan." Narma tayi ajiyar zuciya ta ce, "Yanzu me zanyi?." Mum ta ce, "ki tashi ki shirya zaku wuce." Narma ta miƙe tsaye ta ce, "To zan yi, Tunda kun yi min auren dole zan tafi. Shima haka Faruk ɗina ya ce, ya ce kar na sake kiransa, na manta dashi wai ni matar aure ce" ta kalle su ta ce, "tambaya ta yake yi indai Ina sonsa nayi abinda ya ce. Tunda haka yake so kuma haka yake so zan yi" ta faɗa a sanyaye.
Tausayi ta bawa Najwa ta kawar da kai bata son yin kuka a gabanta. Duk sun ji me ta ce Mum ta kalli Dad ya ɗauke kai Narma ta shiga banɗaki.
Mum ta kalle shi ta ce, "bai daina bibiyar min yarinya ba kenan ko?." Najwa ta ce, "Ya Narma itace take bibiyarsa, ko a yanzun ma itace ta kira shi kuma tayi sa'a ya ɗauka dan baya ɗaukar wayarta. Gwara ma da ta kira shi ɗin ai, ba dan ya ce taje ɗin ba da baza ta tafi ba" Najwa ta faɗa tana fita daga ɗakin. Mum ta kalle Dad ta ce, "kaga tabbacin asiri ya yiwa Narma ko? Kana ɗaukar maganar nan wasa, Ina faɗa maka abinda ya kamata a yi kana mayar dashi wasa ko Dear?. Shikenan" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.
Narma duk tana jinsu tana daga banɗaki a haka tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da wando. Rigar tana da tasho har guiwar ta ɗauki Jessy veil ta naɗa a kanta ta zauna a gefen bata ce komai ba. Najwa ce ta shigo ta kalle ta ta ce, "Ya Narma muje" ta faɗa tana ɗaukar mata jakar. Har Najwa zata wuce sai taga charger ɗin wayarta zare ta saka a jaka ta fito daga ɗakin ita kuma tana bayan ta.
Ashraf yana tsaye a falon ƙasa suka sakko ya riƙo hannunta bata kwace hannunta ba dan bata da ƙarfi a jikinta. Mum ce ta buɗe mata hannu alamun taje jikinta, ta zara hannunta daga na Ashraf ta ƙarasa ta shiga jikin Mum ita kuma tana murmushi ta ce, "Fatan samun kwanciyar hankali da nutsuwa my love." Dad ma kallon ta yake yi bayan ta ɗago daga jikin Mum ta ƙarasa wajan Dad shima ya rungume ta ya ce, "Allah ya yi miki albarka my love, fatan samun lafiya."