Sashe 2
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowa Mum tayi bayan ta yi bacci ta kalli Sen ta ce, "ya faɗa musu inda ya kai Narma aka yi mata asiri, yayi gaggawar warware asirin kafin ya kai ga yin dama sani!" Mum ta faɗa ido na cikowa da ƙwallar tausayin Narma. Dad bai ce komai ba amma tabbas zai san abinda zai yi akan asiri nan da ya yiwa Narma, dole ma ya warware shi kafin ya rasa ƴarsa.
*Kano.*
Didi tun a daren jiya da ta ga dare ya yi babu Omar babu labarinsa hankalinta ya tashi, ta kira wayarsa yafi sau babu adadi ba a ɗauka, ta kira ta su Bashir duk a banza bata samu hakan ya ɗaga mata hankali sosai. Har sha biyu na dare ta kasa bacci, ko ya ta ɗin ji motsi zata firgita ta kalli ƙofa amma babu Omar babu alamunsa. Gashi ta san shi mutum ne da duk inda yaje komai dare a gida yake kwana, baya kwana a wani waje in ba gida ba. Gabaɗaya hankalinta ya tashi, bata da nutsuwa bacci ko kulle ido bata yi ba tana tunanin dawowar sa.
Rashin baccin da bata yi da wuri ba ya saka ta makara sallah asuba, sai shida ta farka a firgice ta fito ta shiga ɗakin Omar amma baya ciki. Salati take yi a zuciyarta, ta kira wayarsa zuwa lokacin ma wayar a kashe take. Daƙyar ta iya yin sallah dan ba nutsuwar kirki gare ta ba, tana idarwa ta sake kiran su Bashir amma suma duk a kashe.
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Allah yasa ba masu garkuwa da mutane ne...." Sai kuma bata ƙarasa ba jikinta har rawa yake kamar mazari saboda tashin hankali. Ta rasa wanne tunani ma zata yi ta ji daɗi, ta damu da rashin Omar matuƙa, inda ya saba kwana a wani waje ne ma da sauƙi, to ta san duk daren duniya Omar sai ya dawo gida hakan shine yake ɗaga mata hankali.
Taci kukan ta ta gode Allah, fuskarta tayi ja sosai ta kasa aikata komai a gidan gabaɗaya jikinta a sanyaye yake. Gashi an wayi gari juma'a bata da karsashin iya yin abincin sadaka dan ta tabbatar bata da wannan ƙwarin guiwar shiyasa ma bata yi tunanin yi ba.
Karfe sha daya na safe tana zaune a falo ta zuba uban tagumi ta jiyo sallama, ai a haukace ya fito tsakar gidan idon ta ya haɗu da na Goje ya yi wujiga-wujiga. Didi tayi ajiyar zuciya ta ce, "Alhamdu lillah! Meyasa ku ka tayar min da hankali ne Bashir? Meyasa baku kira ni kum faɗa min a can zaku kwana ba?. Ina Omar ɗin yake?." Bashir ya kalle ta ya ce, "Didi ba tare muke da Damisa ba" Didi da mamaki ta ce, "Kamar ya kenan? Ba tare ku ka tafi ba?."
"Tare muka tafi Didi."
"A Ina ya tsaya shi?." Bashir ya sauke numfashi ya ce, "Didi mahaifin yarinyar nan ne ya saka aka kama Damisa."
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ya saka aka kama Omar kuma Bashir? Akan wanne dalili? Laifin me ya aikata masa aka kama shi?. Bashir ka bani amsa, Mustapha ku nake saurare ku faɗa min!"Ta faɗa a gigice tana kallon su. Goje ya ce, "Didi bai masa laifin komai ba, kawai saboda ƴarsa tana sonsa shiyasa ya yanke wannan hukunci. Ya saka a kama shi da laifin wai yazo har gida zai kashe shi kuma zai sace masa ƴarsa. Mu kan mu damu aka kama gabaɗaya, Sanata ɗin ya saka a sake mu wai dan mu zo mu sanar daku Omar bazai dawo ba har abada."
Jiri ne ya fara ɗaukar Didi tayi saurin dafa bango tare durƙushewa a wajan tana kuka sosai. Kuka take yi wanda ya hanata magana, kuka mai sauti mai nunu da tsantsar damuwar da take ciki. Ta ce, "Bashir sai da na ce masa kar ya je, sai da nace masa kar ya je yarinyar nan tafi ƙarfinsa amma Omar da yake baya jin magana sai da yaje. Sai da nacewa Omar kar ya yi wannan gangancin amma Omar ya ƙi jin maganata. Da ya ji maganata da yanzu muna tare dashi babu abinda ya same shi, da ya ji maganata da yanzu ba a kama shi ba" magana take cikin fitar hankali tana kuka sosai hakan ya karya zuciyar Bash da Goje.
"Ki yi haƙuri Didi, zamu san yadda zamu yi ya fito, mun san manya da yawa zamu je mu saka su shige mana gaba a fito da Omar."
"Bashir babu lallai su amince, amfani kawai suke yi daku amma in kun shiga matsala baza su iya shige muku gaba dan warware ta ba. Bashir in akace Omar baya nan ya zan yi? In aka ce Omar bazai dawo ba ya zanyi?. Ta ya zan iya rayuwa bana ganin Omar? Ya rayuwata zata kasance Omar yana wani waje ana bashi wahala ni ina nan?."
Goje ya ce, "ki kwantar da hankalin ki Didi zai dawo in sha Allah, zamu san abinda zamu yi. Zamu bi duk hanyar da zamu bi dan dawo dashi. Ba ke kaɗai zaki shiga damuwa ba in baya nan, har damu Didi." Bata kula shi ba sai kuka kawai da take yi, Goje ma kukan yake yi ya fita dan fara neman mafitar dawo da Tigar ko ta hali ƙaƙa.
Didi sai da tasha kukan ta son ranta sannan ta iya tashi jiki a sanyaye ta shiga falo. Babu wanda zata faɗawa damuwarta, ta saba su biyu suke solving matsalar su basu da wasu dangi da suke warware musu matsala balle ta ce zaje ta faɗa masu. Hajja ce ta faɗo mata a rai, ta miƙe da sauri ta saka hijjabi ta fita zuwa gidan Hajja.
Hajja da take zaune ita da Salma ganin yanayin Didin duk sai suka kalle ta dan sun san ba haka ta saba shigowa ba. Wajan Hajja ta nufa ta durƙusa kusa da ita kawai ta fashe da kuka. Hajja hankalin ta ya tashi ta ce, "Aisha lafiya? Me ya faru kike kuka?." Bata daina kukan ba sai da ta gaji sannan ta kalli Hajja ta ce, "Hajja Omar."
Hajja cikin tashin hankali ta ce, "me ya same shi?." Didi cikin kuka ta faɗawa Hajja duk abinda ya faru sannan ta ce, "Hajja yana can Abuja sun kama shi, Hajja ya zanyi? Na rasa inda zan saka raina. gabaɗaya hankali a tashe yake."
Hajja ta ce, "Hasbunallahu wani'imal wakil! Amma Ummaru ya yi ganganci."
"Hajja babu yadda ban yi dashi ba amma taƙi ji, Omar in yaso yin abu ko duniya bata so in dai shi yana so sai ya yi, na bashi shawara akan haka amma yaƙi saurarena. Hajja in wani abun ya same shi ya zanyi?" Ta ƙarasa faɗa murya na rawa. Hajja ta ce, "ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah zai fito."
Didi ta ce, "ta ya zai fito Hajja? Ta ya ya Omar zai fito bayan furucin da Sanata ya yi a kansa?. Hajja Sanata ne fa ya saka aka kama shi, dawowar Omar gida abu ne mai matuƙar wahala." Hajja tayi ajiyar zuciya ta ce, "kar ki damu Aisha, zan yiwa mahaifin salma magana ko ya san Sanata ɗin. Ɗan kwangila ne wataƙila suna da wata alaqa dashi. Ki kwantar da hankalin ki mu bi komai a sannu kar ki damu." Didi ta goge idanun ta ta ce, "to Hajja. Na rasa inda zan kai kuka na shiyasa nazo gare ki." Hajja ta dafata cikin tausayi ta ce, "kar ki damu, in sha Allah yadda kika kawo min kukan ki zan zama silar share miki hawaye. Salma bata ruwa ta sha" ta faɗa tana kallon Salma. Salma ta miƙe ta kawo mata ruwa ita kanta tausayin Didi take ji.
Ruwa ta sha tana jan numfashi cikin tashin hankalin da take cikii,Hajja ta dinga rarrashin ta tana bata baki har ta ɗan nutsu sannan ta ce bara ta koma gida ta dawo. Bayan ta fita Salma tayi tsaki ta ce, "Wannan Omar da ɗaukar dala ba gammo yake, Ina shi ina soyayya da ƴar Sen Sagir banda ɗage irin na sa?. Haka kawai ya tayarwa da baiwar Allah hankali bata ji ba bata gani ba." Hajja bata ce komai ba ta san Daddy zai zo tunda juma'a ce tayi alqawarin yi masa magana in yana da hanya a fito da Omar ko dan saboda Didi ɗin.
Da yamma kuwa sai ga Daddy bayan sun gaisa da Hajja take yi masa bayani akan Omar. Daddy ya ce, "wanne Sentor ɗin kenan?." Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma meye ma ta ce sunansa?." Salma ta ce, "Daddy Sen Sagir Sani take nufi." Daddy ya ce, "Kai! Shi ya saka aka kama shi?." Hajja ta ce, "eh shine. In kana da hanya ka yi masa magana don Allah ya sako shi ko dan ƴar uwar sa da bata da kowa sai shi, ta shiga damuwa sosai Allah, kaɗai ya san halin da zata iya in akace Omar bazai dawo ba."
Daddy ya ce, "Hajja na san shi, amma bani da wata kyakykyawar mu'amala dashi gaskiya saboda mutumin bashi da kirki ko kaɗan. Bashi da kirki bai san kirki ba kuma bashi da ɗaga ƙafa kwata-kwata. Amma zan bincika a mutanena ni akwai wanda yake da mu'amala mai kyau dashi sai ayi masa magana, ko Ali zan tambaya ko shi ko Khabir. amma fitowarsa gaskiya da wahala." Hajja ta sauke numfashi ta ce, "Don Allah ka hanzarta."
"In sha Allah zan yi Hajja."
"Yauwa Allah ya yi albarka."
"Amin Hajja. Batun tafiyar ku umra yaushe ki ke ganin zaku je?." Hajja ta ce, "Duk sanda aka ce a shirye nake." Daddy ya ce, "Shikenan Hajja, zaki ji ni in sha Allah." Ta amsa tana ta addu'a yana amsawa shi da Salma. Hajja ta ce, "na san Ali ma yana hanya, wannan karon ka yi masa shigar saurin kaini Saudia. Khabir daman shi ya ce England zai kaini, na ce Khabiru nayi me a can, wai ki huta." Daddy yayi dariya ya ce, "ɗan rigima kenan." Daga nan suka yi sallama Daddy ya tafi.
[20/09, 8:29 am] +234 906 075 3382: KRB2P002
Arewabooks@nanahaleema11