← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 52

Sashe 3

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallar magriba Hajja ta tura Salma ta kira mata Didi suka dawo tare. Hajja ta bita da kallo ganin duk ta firgice ta ce, "Aysha ki kwantar da hankali ki don Allah, kalli yadda ki ka firgice lokaci ɗaya." Didi ta zauna kusa da Hajja tana murmushi kaɗan-kaɗan. Hajja ta ce, "Nayi magana da mahaifin Salma, ya ce min shi bashi da wata alaqa mai kyau da Sanata, amma akwai wanda zai yiwa magana zai same shi in Allah ya taimaka za a dace. Amma ya maimaita min bashi da kirki sai dai mu dinga addu'a kawai."

Didi tayi ajiyar zuciya cikin sanyi ta ce, "Allah ya sa Hajja.." Hajja  ta ce, "amin. Sannan ki ɗauko abinda zaki ɗauko a gidan ki taho nan ki kwana, in aka farga Omar baya nan akwai masu jin haushinsa da yawa zasu iya cewa zasu shigo gidan ku. A san bai saaba tafiya ya bar gida ba, in aka lura da baya nan za a iya samu damuwa." Didi ta ce, "To Hajja, amma babu abinda zai faru."
"A'a dai, gwara dai ki dawo nan ɗin hankalina zai fi kwanciya." Wayar Didi ce take ƙara ta duba taga AbdulHamid ne yake yi mata waya, ta kalli Hajja ta ce, "Hajja AbdulHamid ne yazo."

Hajja ta ce, "to ya shigo gidan nan sai ku tattauna, shigar sa gidan ku ke kaɗai babu daɗi." Didi ta ce, "to bara na kira shi sai yazo nan ɗin." Ta faɗa tana ɗaukar wayar ta sanar dashi inda zai zo kafin Hajja ta tura Salma ta shigo dashi. Da sallama ya shigo cikin kamalar sa ta ko yaushe, Salma tayi masa iso har falon Hajja ya shigo ya gaishe da Hajja da girmamawa ta amsa tana cewa, "Yau ai wajan uwar gidan kazo ko?." Murmushi ya yi ya ce, "Daman yau zuwan na ki ne."

Hajja ta ce, "Haba shiyasa ka sha kwalliya mana, dan wannan kwaliyya bata amarya ba ce." Murmushi ya yi yana kallon Didi da bata da walwala sosai duk fuskar ta ta canja. Hajja ta ce, "ya shirin biki? Saura kwana nawa ya rage ne?."
"Saura sati shida. Yanzu ma nazo akan batun gidan da za a je gani saboda shirye-shirye." Hajja ta ce, "kai har saura mako shida? Lallai abu yazo. Allah ya nuna mana ya tabbatar da alkhairi." Ya amsa da amin.

Hajja ta ce, "gashi tana cikin yanayi na damuwa. Omar ne aka kama shi Abuja ba tare da laifin komai ba." AbdulHamid ya ce, "Subahanallah! Yaushe hakan ya faru?."
"Jiya."
"Bata sanar dani ba, na dai damuwa a muryar ta." Hajja ta ce, "wallahi shine ya canja ta gabaɗaya."

AbdulHamid ya ce, "Ya aka yi hakan ya faru?." Labari Didi ta bashi muryarta har rawa take yi saboda damuwa, ya sauke numfashi bayan ta ya ce, "case ne na manya gaskiya tunda da kansa ya saka aka kama shi, amma a shari'ance bashi da hurumin kama Omar dan bai yi masa laifin komai ba. To matsalar itace yadda ƙasar mu take sai a hankali." Hajja ta ce, "Wannan gaskiya ne, amma zamu san abinda zamu yi in sha Allah."

AbdulHamid ya ce, "nima zan yi ƙoƙari daga ɓangarena in sha Allah. Kar ki damu kin ji?" Ya faɗa yana kallon Didi. Kai ya girgiza kai bata ce komai ba. AbudlHamid ya ce, "Amma ba ke kaɗai zaki kwana a gidan ba ko?." Ta ɗaga kai ta ce, "Hajja ta ce na zauna a nan."
"Gaskiya haka ya kamata, za a iya amfani da rashin Omar don cutar da ke." Hajja ta miƙe ta basu waje daman Salma ta shige ciki tunda ta ajjiye masa ruwa da lemo.

Rarrashin Didi ya dinga yi har sai da ya ga ta ɗan kwantar da hankalinta, maganar gidan da ta kawo shi ma basu yi ba dan ya san ba a nutse take ba sai ta dawo hankalinta sa tattauna. Bai jima sosai ba ya saka ta kira masa Hajja suka yi sallama yana godiya sannan ya tafi.

Didi ta ce, "Hajja bara na je gida na kashe kayan wuta na dawo." Hajja ta amsa mata sannan ta fita. Ba jimawa ta dawo gidan bayan ta kulle gidan ta dawo falon Hajja ta zauna amma gabaɗaya bata jin daɗi.

Sallamar Bashir ta ji daga gate ɗin Hajja, ta tashi da hanzari ta je ta ce, "Bashir ya ake ciki?." Ya kalli Didi ya ce, "Didi Ina ya bincikawa, na dawo Goje ya ce min kina gidan nan shine nazo na ji lafiya. Ko akwai wanda ya shiga gidan?."

"Babu kowa. Hajja ta ce na dawo nan na kwana ne saboda gidan babu kowa."
"Haba Didi, muna nan fa, wallahi ko kuɗa bazai taɓa ki da niyar cutarwa ba." Didi ta ce, "Gwara dai na zauna a nan ɗin Bashir. Don Allah duk abinda ake ciki ka yi min waya." Bashir ya amsa sannan ta dawo gida wajan Hajja gabaɗaya bata da nutsuwa.

Hajja ta ce, "Salma kai ta ɗakin Nayla ta huta." Salma ta raka Didi ɗakin Nayla da yake shirye tsaf sai khamshin turarenta yake yi. Murmushi tayi tunawa da Nayla, ta zauna a gefen gadon tana kallon kan mudubin Nayla da yake ajjiye da kayan kwalliya kamar a gidan take rayuwa. Murmushi tayi ta kalli Salma da ta kawo mata abinci ta ce, "Salma ni fa ba baƙuwa bace, ki daina hidima haka."
Salma tayi dariya ta ce, "na sani Didi, hutar dake nayi." Didi ta ce, "na gode. Ɗakin ƙanwata Nayla sai ƙhamshi, ga kayan kwalliya kamar tana ciki."

Salma tayi dariya ta ce, "Aljanar kwalliya kenan." Didi tayi murmushi kawai bata ce komai ba Salma ta fita ita kuma ta ɗauki abincin ta fito ta zauna kusa da Hajja tana ci suna ƴar hira kaɗan.

Washe gari.
Abuja.

       "Daddy Ina aka kai Faruk? Daddy a dokance baka da right ɗin da zaka saka a kulle shi ba tare da ya yi wani laifi ba. Yana da damar da zai kai ka ƙara court kuma dole a yi maka hukuncin aikata haka" Sai kuma ta daidaita murya ta ce, "Dad Ina yake? Don Allah ka faɗa min inda aka kai shi" ta faɗa tana zamewa a wajan tana kallon mahaifin na ta.

Shi tausayi take bashi sosai, gabaɗaya ta fita daga hankalinta ta koma wani iri kamar ba Narma ƴar gayu mai aji ba. Kallon Mum ya yi da take kallon sa kafin ya sake kallon Narma ya ce, "Narma ki nutsu." Narma cikin kuka ta ce, "bazan iya nutsuwa ba Dad, bazan iya nutsuwa ba Ina so na ganshi. Ina kewarsa, don Allah Dad kar ka cutar dashi. In aurena dashi ne baka so zan haƙura dashi amma kar ka yi masa komai don Allah Daddy, bashi da laifin komai ni ce na fara son sa."

Sen ya kalle ta ya ce, "na ce ki nutsu ko?." Zama tayi tana share hawaye ya kalle ta ya ce, "Ranar monday zaki jinginar da duk abinda ki ke yi zaki tafi London." Da sauri ta ɗago kai ta kalle shi murya na rawa ta ce, "Daddy London..? Me zan yi a can?."
"Ina so ki je ki huta hankali ki ya dawo jikinki daga baya za a san abinda za ayi."
"Dad i can't go anywhere without knowing where Faruk is. Where you have take to him?. Dad wallahi bai yi deserving wannan hukuncin ba, it's his fault for falling in love with me?. Kuma Daddy kai ka yi min alƙawari zaka bani duk wanda nake so, na kuma kawo maka shi ga sakamakon da ya biyo baya."

Dad kallon ta ya ke yi kamar bata cikin hankalinta, sai magana take yi mara kan gado kamar ba ita ba. Sai ya yi shiru bai ce mata komai ba. Narma ta ce, "don Allah Dad ka taimake ni ka bar Faruk ya tafi, ka ƙyale shi na yarda na haƙuta dashi bazan sake cewa Ina sonsa ba." Mum ta kalli Dad sai ta miƙe kawai ta bar wajan jim kaɗan sai gata ta dawo. Ba jimawa sosai sai ga wani saurayi ya shigo Mum ta taso ta riƙe Narma ya yi mata allurar bacci.

Mum ta kalli Dad ta ce, "ni na kira shi, na lura Narma ba ta cikin hankalinta. Ya gama lalata min tunanin yarinyata, ya gama cutar da ita. Na rantse da Allah na tsane shi bana sonsa, bana so ya rayu a cikin duniyar nan." Dad ya kalli Narma da tayi bacci a wajan ya kalli Mum ya ce, "sai a hankali zata dawo daidai, ita da ganin sa kuma har abada" yana gama faɗa ya fita dan ya zama dole ya canja shiri akan Omar.

Narma bacci tayi na sama da awa bakwai, dan tun safe take bacci har bayan sallar la'asar sannan ta farka da weaknesses joints. Daƙyar ta iya wanka ta fito tana kallon kanta a madubi, key ɗin mota ta ɗauka bayan ta shirya ta fita daga gida.

Kai tsaye wajan ɗan sanda da ya zo ya kama Omar ta je ta ce tana so ta ga Omar. Da kamar bazai kai ta ba amma ya ga ta dage sai ya saka aka raka ta inda aka ajjiye Omar.

Can ƙauyen Abuja ne, cikin wata unguwa da bata taɓa zuwa ba, aka buɗe mata wani wulaƙantaccen gida ta shiga ana biye da bayanta. Kallon gidan take yi tana hawaye, wai Omar ɗin ta ne a cikin nan ba tare da ya yi laifin komai ba.
Chapter 3 · 0% Book details