Sashe 6
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mum ni bana son barin Nigeria, in naje England me zan yi a can?. Ni ku barni na zauna a nan babu inda zan je" ta faɗa tana kuka tana riƙe da Mom da take riƙe da ita itama. Mum a tausashe ta ce, "zaki je can ne ki samu hutu Narma, ba zama zaki yi a can gabaɗaya ba, zaki huta ne na ɗan lokaci sannan ki dawo kin gane?."
"A'a Mum, ni a barni na zauna a nan bana so na tafi na bar Faruk a gidan da Dad ya kai shi, ban yi masa adalci ba in na tafi tunda ni ce na gayyato shi. Don Allah ku bani dama na fitar dashi sai na tafi."
Dad ya ce, "Narma! Ki yi abinda aka ce kawai." Narma ta ce, "Dad bashi da laifi fa, ni ce nace Ina sonsa har ya amince dani, kuma ni na gayyace shi nan ya amsa gayyata ta yazo. Sai da ya maimaita min babu matsala na ce masa babu saboda na yarda da alqawarin da kayi min, ban ɗauka zaka yi disappointing ɗina ba Dad. Na ɗauka kana son duk abinda nake so, na ɗauka zaka bani abinda nake so ko meye shi, amma ka kasa....ka kasa bani farin ciki Dad...ka kasa cika min burina..." ta faɗa tana kuka sosai. Dad cikin tsawa ya ce, "Narma ya isa! Kar na sake ji kin ce nayi disappointing ɗin ki
Narma ta ce, "inda falon sama zai yi magana zai bada shaida, kai ka ce ko waye kana maraba dashi, kai kace kana maraba da shi matsayin sirikinka, da yazo dan ya gaishe ka ga abinda ka yi masa. Ina sonsa, ku barni na zauna a nan in ba haka ko na je can bazan ji daɗin zaman ba."
Dad a fusace ya ce, "sai kin tafi! sai kin je England in ki yi duk abinda zaki yi. Last warning zan miki yanzu, kar na sake ji kin furta na karya miki alqawari, kar na sake ji kin ce kina sonsa kin gane!?." Kallon Dad ɗin take yi dan bata saba jin tsawa daga wajan iyayenta ba hakan ya bata mamaki ta ce, "Dad you shouted me?."
Mum ta katse Sen ta ce, "Dear stop please, ka daina sake tsorata ta don Allah. Ka bari mu ji da yanayin da take ciki mana." Shiru ya yi bai ce komai ba ta kalli Mum ta ce, "Mum zaki saka a fito dashi? Dad ya saka ana ta wahalar dashi. Zaki bari na aure shi?."
"Babu maganar aure tsakaninki dashi, in akwai a zuciyarki ya kamata ki goge dan ba abu ne da zai yu ba" Dad ya faɗa yana nuna ta da yatsa dan ta fara fusata shi. Zata yi magana ya katse ta ya ce, "kar ki ce min komai, zaku yi missing flight ku wuce ku tafi" ya faɗa yana hawa sama. Narma tana kuka Mum ta riƙe ta har bakin mota, ta shiga itama sai da ta kai su airport tana jajjadawa Najwa kula da ita, sai da taga tashin jirginsu sannan ta dawo.
Kai tsaye ɗakin Dad ta shiga ta same shi ta ce, "ya zama dole a saka Tiger ya karya asirin da ya yiwa Narma, sannan ya zama dole a samu abinda zai ɗauke mata hankali a London." Dad ya kalle ta ya ce, "na san abinda zan yi akan maganar Tiger. Maganar Narma a London kuma Ina tunanin nan da kwanaki biyu na tura mata Ashraf."
Mum da mamaki ta ce, "Ka tura mata Ashraf for what?." Dad ya ce, "Auren masa ita zan yi." Mum ta wara idanu waje ta ce, "aure fa? Auren Narma ne zai kasnace a haka?." Dad ya ce, "kina da wata hanyar ne bayan wannan? Ashraf shine boyfriend ɗinta, shi ta so kafin asirin Tiger ya kamata, in aka ɗaura auren su ya bita London zai ɗauke mata kewar Omar har ta manta dashi. Ki daina tunanin a yadda auren zai zo, ki duba yanayin da ƴarki take ciki. Ba lallai sai duniya ta san anyi auren ba, in aka ɗaura auren daga baya in ta dawo daidai sai ayi biki mai girma. Amma a yanzu ba maganar biki ake yi ba, magana ake ta ceto Narma."
Mum tayi ajiyar zuciya ta ce, "Dear Don Allah ka tabbatar da Tiger baya numfashi a duniya, ka tabbatar da ƙasa ta rufe idanunsa. Duk ta silarsa wannan abubuwa suke faruwa, don Allah a ɓatar dashi a daina jin labarinsa, hakan shine kawai zai saka na huce daga raɗaɗin abinda ya yiwa Narma." Sen ya taso ya rungume ta ya ce, "kar ki damu Dear, na san abinda zan yi akansa. Labari da tarihin Omar zai shafe a duniya gabaɗaya, don't worry."
"Saboda shi Narma ta tafi London ba dan tana so ba, saboda shi ana ƙoƙarin yi mata irin wannan auren. Ji nake kamar na kamo shi na harbe." Bayan ta yake shafawa cikin rarrashi amma shi kansa abin ya tsaya masa a zuciya, zai kuma zan abinda zai yi.
*Kano.*
Didi tun tana jiran tsammani daga Hajja har ta gaji, ba labarin ceto mata ƙaninta gashi har an yi kwanaki goma da kama Omar. Duk ta damu ta koma wani iri ƴan unguwa kaf an fahimci Omar baya nan, duk da haka babu wanda ya yi gigin yiwa Didi wani abun a san duk inda ya je tabbas ai dawo.
A ranar Bashir ya ce mata zai je Abuja ya duba prison ko an kai Omar ɗin can. Sai dai ya je ɗin ya faɗi sunan Omar matsayin wanda yazo yiwa ziyara, kaf sunayaen mutanen da suke ciki babu mai suna irin na Omar. Gabaɗaya ya damu shima a haka ya dawo Kano a ranar duk ya galabaita.
A gidan Hajja ya same ta da daddare ko abinci ta kasa ci tana jiran dawowarsa. Tana jin sallamar da ta miƙe tana kallon sa har ya shigo yana kallon ta shima. Hajja ta ce, "Bashir ka ga Omar ɗin?." Bash ya girgiza kai ya ce, "Ban gan shi ba, ko mai irin sunan sa an tabbatar da baya cikin prison ɗin."
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Shikenan sun kashe min Omar, Hajja sun kashe min shi" ta faɗa cikin kuka sosai. Hajja ta riƙeta cikin tausayi ta ce, "Haba Aisha! bai kamata ki yi wannan tunanin ba, in sha Allah Omar yana nan da ransa kuma zai dawo gare ki in sha Allah."
Didi tana kuka ta ce, "Hajja in ba basu kashe shi ba yana ina? Meyasa ba a same shi a can ba?" Ta faɗa tana sake fashewa da kuka cikin rashin mafita. Sai kuma ta kalli Bashir a firgice ta ce, "Zaka iya raka ni Abujan gobe? Ina so naje gaban Senator da kaina na bashi haƙuri akan abinda Omar ya yi masa. Zaka raka ni mu je tare?."
Hajja ta kalle ta tana jinjina girman ƙaunar da take yiwa Omar tace, "wa kika sani a Abujan da zakije? Sannan kema in ya yi miki wani abun fa?." Didi ta ce, "Hajja gwara na je, gwara naje Hajja bazan iya zama babu Omar ba. Ban san halin da yake ciki ba, ko zai yanka ni gwara naje na bashi haƙuri."
Tausayi ta bawa Hajja ta dinga rarrashinta amma ta kafe akan ita fa sai ta je Abuja. Hajja ganin ta kafe ya saka ta ce, "Shikenan Allah ya kaimu goben, zan saka a kai ki da motata sannan ku tafi Bashir ɗin." Didi ta ce, "Na gode Hajja." Hajja ta ce, "ya isa, ki daina wannan kukan shine bana so."
Hajja ta kalli Salma ta ce, "Ko zaki raka ta Abuja gobe?." Salma ganin Didi ba ita take kallo ba sai ta wara ido ta ce, "Zan je wajan Daddy gobe." Hajja ta kalle ta kawai dan daman ta san baza ta je ba, dama dai Nayla ce. Ita kuwa Salma ƙunƙuni take yi tana cewa, "Haka kawai na je nima ayi ram dani, wallahi bazan je ba ita dai taje tunda ɗan uwanta ne. Haka kawai babu dangin iya babu na Baba ga rashin mutuncin da yake yiwa mutane, naje na bada haƙurin a karɓo shi ƙarshe ya dawo yana yi min wulaƙanci. Bazan je ba wallahi."
Ranar daƙyar Didi ta iya yin bacci,asubar fari suka buga sammako suka ɗauki hanyar Abuja da fatan dacewa da kuma nasara a kan abinda zai kai su Abujan.
*Kaduna.*
Nayla ta damu sosai akan Omar, tana ƙoƙarin dannewa ne kawai saboda Mama tace ta dinga daurewa saboda Abiy, amma Allah kaɗai ta san meye a zuciyarta da kuma abinda take ji akan Omar da rashinsa da aka ce ba a yi ba. Ta fara neman hanyar da zata bi wajan ganin ta dawo da Omar, ta rasa inda zaje ta samu damar da za a iya yiwa Sen magana ya sakar mata masoyinta. Tana nan tana shiri akan tunkarar Ogan su na wajan aiki da maganar Sen ko Allah zai saka a dace.
Video call Nayla da Salma suke yi suna hira, hirar dai rabi rarrashin Nayla take yi akan abinda yake zuciyarta. Nayla ta ce, "Salma ya batun Didi kuwa? Omar ɗin ya dawo?." Salma ta yi ƙaramin ta ce, "ke wai kullum sai kin tambaye ni batun wani Omar? Ina ruwanki da dawowarsa ne?." Nayla ta daure ta ce, "Ina damuwa ne saboda Didi kawai malama."
Salma ta yi tsaki ta ce, "Har yau dai babu labari, Daddy bai san kowa da yake da alqala mai kyau da Senator ba. Allah sarki kin san me?." Nayla da ta ke ta shirin tafiya aiki ta ce, "Sai kin faɗa."
"Didi ta ɗauki hanyar zuwa Abuja dan ta bawa Sen haƙuri. Wallahi ni itace take bani tausayi ba shi ba. Ban ɗauka haka take tsananin ƙaunar Omar ba sai yanzu, gabaɗaya ta firgice in kika ganta sai ta baki tausayi. Tana son ƙanin nan nata, gashi Allah ya haɗata da ƙaddara, dan ɗan uwa irinsa ai ƙaddara ce." A sanyaye Nayla ta ce, "ita da wa ta tafi?."
"Ita da yaron sa Bashir sai Hajja da ta saka Sayyadi ya kai su."