Sashe 26
Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗagowa tayi ta kalli Yayan ta Nabil Shima ta shiga jikinsa ta rungume shi ya ce, "Allah ya dawo dake lafiya." Zare jikinta tayi ta koma kusa da Najwa ta tsaya. Dad ya ce, "Ashraf ga Narma nan please ka bita a sannu, kaga dai ba lafiya ce da ita ba sai ka yi haƙuri na ɗan lokaci saboda yanayinta. Bani da wani tunani mara kyau a kanka, na san kana sonta zaka iya kula da ita a ko wanne yanayi. Please ka bata farin ciki, ka tabbatar da ta dawo nutsuwarta." Ashraf yana murmushi ya ce, "in sha Allah Dad kamar an yi an gama." Suka amsa gabaɗaya suka fito harabar gidan suka shiga mota Najwa ma ta shiga dan zata rakata airport suka tafi.
Motar su na wucewa Mum ta dawo gida ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Sai nake ji kamar na sauke wani abu mai nauyi, Daughter zata sumu kwanciyar hankali ko ya ya ne." Dad bai ce komai ba ya murmusa kawai amma a zuciyarsa ya san basu kyautawa Narma ba, irin wannan aure da suka yi mata ba tare da shiri ba, amma in ya tuna haka shine zai saka ta samu kwanciyar hankali ta manta da Omar sai ya ji daɗi har hankalinsa ya kwanta.
•••••••••
Omar tunda ya yanke wayar wayar Narma ya jingina da kujera ya lumshe ido. Sautin kukan ta yake ji a kunnensa sai ya ji rauni ya mamaye zuciyarsa gabaɗaya. Da a ce ya san haka lamarin Narma zai zamar masa da tun farko bai bata fuskar da zata saki jiki dashi har su saba haka ba. Da ya san haka zata dinga shiga damuwa ta dalilinsa da bai tsaya ya saurareta ba, da bai bari yaji abinda yaji a kanta a lokacin baya ba. Tana bashi tausayi sosai, bai san abinda take ji a zuciyarta ba, amma ya tabbatar ko meye yana da zafi da raɗaɗi mai yawa. Ya sauke ajiyar zuciya ya buɗe idanunsa a hankali yana kallon falon cikin kewar Didi.
"Assalamu alaikum, Boss na dawo" aka faɗa ana shigowa falon. Ya kalli Tk a kasalance ya ce, "ya ake ciki?."
"An samu shagon akan titi, kuma babba ne yana yana da girma zai yi yadda ka ke so."
"An karɓa?."
"E, an karɓa. Yanzu kai mu ke jira mu ji ya za a yi." Ajiyar zuciya ya yi ya kalle shi ya ce, "a gyara shi a saka abinda za a buƙata. Ku yi lissafi duk abinda kuke ganin ya dace ayi, kar dai ku yi min hauka a ɓarnatar min da kuɗi. Zan fito zuwa anjima sai mu ga yadda abin yake."
"An gama Damisa" ya faɗa cike da girmamawa ya fita. Bai bari tunanin Narma ya dawo zuciyarsa ba ya tashi ya shiga kitchen dan samun abinda zai ci.
Kallon kitchen ɗin yake yi kafin yaja tsaki a bayyane ya ce, "Rashin Didi babbar illa ce a gareni, daman ni maraya ne na rashin iyaye yanzu na sake maraicewa. Ko me zan ci ma oho" ya faɗa yana sake kallon kitchen ɗin. Tea kawai ya haɗa ya zuba madara mai shegen yawa tare da sugar, dan shi Allah ya yi masa son madara da sugar, in zai sha shayi to fa sai yayi kauri sugar kuwa sai yayi masa yadda yake so. Da tea ɗin ya fito ya zauna yana sha yana kallon falon yana tunanin Didi.
•••••••
Nayla tunda ta koma gida gabaɗaya ta sake zama shiru babu walwala balle ta sake a zauna a falo ana hira da ita. In ka tambaya ta ce babu abinda yake damunta amma da ka kalle ta ka san tana cikin damuwa. Jin daɗin ta ma in ta fita tun safe sai yamma take dawowa, wannan ya saka bata zama gida sosai ba kasafai ake game yanayin ta ba.
Haka Nayla ta cigaba da rayuwa cikin dauriya da juriyar abinda take ji a zuciyarta. Suna waya da Didi suna gaisawa kamar yadda suka saba bata taɓa ce mata ga abinda yake damuna ba itama bata tambayarta ba sai dai a yi hira kawai a kashe wayar.
Cikin kwanakin Abiy ya yi fama da rashin lafiya shiyasa maganar masu neman auren Nayla bata tashi ba saboda baya jin daɗi. Amma abun yana zuciyarsa so yake ya warware ya kira ta yaji ta bakin ta.
Yau ta kama ranar Asabar Nayla tana gida babu aiki tana kwance a ɗaki suna waya da Twiny cikin hirar su da bata wuce guda ɗaya. Mama ce ta shigo ɗakin da sallama Nayla ta amsa tana kashe wayar tare da tashi zauna. Mama ta ƙaraso ta zauna kusa da ita ta ce, "Keda Jidda ne?." Nayla ta ce, "itace Mama." Mama ta girgiza kai ta ce, "Nayla kin san tun kafin kije Kano bikin maƙociyar Hajja mahaifinki yake maganar ki fitar da miji a cikin samarinki ko?." Gaban Nayla ya faɗi ta ɗaga kai alamun eh Mama ta ce, "ni ce na ce a ƙyale ki saboda a lokacin bakya jin daɗi kuma bakya tare da nutsuwarki. Kwana biyu kuma kinga bashi da lafiya shiyasa bai tayar da maganar ba. Amma jiya da daddare ya ce yau ki faɗa min waye zaɓinki a cikin samarin nan guda huɗu."
Zuciyar Nayla bugawa take yi matuƙa ta kalli Mama da itama ita take kallo. Mama ta ce, "Ina jin ki, wa kike ɗauka ki ke ganin zaki iya rayuwar aure dashi?." Numfashi ta sauke tare da yin ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, "Mama ni...." Sai maganar ma maƙale saboda bata san ne zata ce ba. Mama ta ce, "Ke me? Faɗi ina saurarenki."
"Mama ni ban san ne zan ce ba." Mama ta ce, "to haka zan faɗawa mahaifinki baki san ne zaki ce ba?." Nayla ta girgiza kai alamun A'a Mama ta ce, "to faɗa min, a wannan lokacin bazai ƙyale ba Nayla sai kin fitar da gwani dan burinsa a yanzu bai wuce auren ki ba. Ya ce ya gaji da ganin samari har huɗi a matsayin masu neman aurenki, wannan rashin lafiyar da yayi ko wannen su babu wanda bai zo ba kuma ya yi hidima. Har gwara shi Abbas daman ko babu soyayya ɗan uwanki ne amma sauran fa?."
Nayla tayi shiru cikin rashin sanin mafita. Ita bata san abinda zata ce ba dan dukkan su babu wanda take so babu kuma wanda take ji zata iya zama dashi a zuciyarta. Zuciyarta mutum ɗaya take so kuma bayan shi babu wanda zata iya bawa dama. Mama ta katse mata tunani ta ce, "ko na ce masa ya sake baki lokaci?." Da sauri ta ɗaga kai alamun eh ta ce, "E Mama, don Allah ki ce ya sake bani lokaci har yanzu babu wanda nake ji a cikin zuciyata. Dukkan su bana sonsu."
"Omar maƙocin Hajja kike so ko!?." Tambayar ta zo a bazata da sauri ta kalli Mama Gabanta na faɗauwa sosai, tsoro ya bayyana akan fuskarta ƙkarara dan bata san ya aka yi Mama ta san labarin ba. Mama tayi murmushi ta ce, "kina mamaki ya aka yi na san waye a zuciyarki Nayla?. Hmm Nayla kenan, kar ki manta ni fa uwa ce a gare ki." Nayla ta sunkuyar da kai cikin bugun zuciya da tsoron bayyanar sirrin zuciyarta ga mutanen gidan su.
Mama a tausashe ta ce, "A da in kin dawo daga Kano labarin Yayarsa kike yi ba shi ba, in hirarsa tazo cikin labarin kina sako shi ne kina tsaki saboda tsoro da haushi yake baki. Amma daga baya sai hirar ta zama hirarsa kawai kike yi, kina bada labarin yanayin yadda yake kyau in yana murmushi. Daga lokacin da akace an kama shi hankali ki ya tashi kika yi ruɗewar da baki san kin yi ba. Muka je Kano bikin Shayida kika kusa yin accident a mota saboda kina so kizo ki samu mahifinki da maganar kina so a fito dashi. A yadda kike yiwa Abiy bayani kowa zai fahimci rauninki a kansa ne ba akan Yayarsa ba, kowa zai fahimci kina roƙon a fito dashi ne saboda shi kike so ba dan kina tausayin Yayarsa ba. Da Abiy ya amsa har ya kira Senator a lokacin farin cikin ki ya kasa ɓoyuwa akan fuskarki. Daga lokacin da akace ya dawo a ranar ke kuma ki ka dawo gida gabaɗaya rasa nutsuwar kiki yi Nayla, har wayata kin karɓa kin kira Salma saboda bata ɗaukar kiranki ke kuma kina so ki ji ko ya dawo."
Mama ta riƙe hannunta sosai ta ce, "tun daga lokacin na saka alamar tambaya akansa a zuciyarki. Abinda ya saka na tabbatar da zargina a kanki lokacin da suka zo gidan nan, kin ruɗe gabaɗaya, duk da ciwon da kike ji wanda ya hana ki zuwa aiki a ranar nan da nan kika neme shi kika rasa. A nan na tabbatar da Omar maƙocin Hajja shine wanda kike so."
Kawai sai ta fashe da kuka ta kifa kanta a hannun Mama tana kuka sosai. Mama ta dinga shafa bayanta a hankali tana murmshshin da ita kaɗai ta san ma'anarsa. A sanyaye ta ce, "Ki yi shiru mana Nayla, ba ga ni ba? zan tsaya a ɓangarenki wajan ganin kin samu abinda ke so. Ki nutsu mu yi magana bana son yawan kukan nan naki."
Ta ɗago fuskarta ta jiƙe da hawaye ta ce, "Mama in Abiy ya ji wannan maganar fushi zai yi dani, Bazai amince da zancen nan ba kawai gwara abar maganar Mama." Mama ta shafa fuskarta ta share mata hawaye ta ce, "Faɗa min gaskiya kina son Omar so na aure ko bakya sonsa?." Nayla ta kalli Mama sai ta sunkuyar da kai ta ce, "Mama faɗar bashi da amfani."
"Ni nace ki faɗa min, zan kuma tabbatar miki da amfaninsa yanzu ko nan gaba." Nayla ta ce, "Ina sonsa Mama, wallahi Ina sonsa son da ban san yawan sa ba. Kuma...kuma....ni ban san lokacin da na fara sonsa ba, haka kawai na wayi gari naji Ina jinsa a zuciyata. Ban san me zan yi ba Mama, na rasa mafita ki taimaka min" ta faɗa a raunane tana kallon Mama.