← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 52

Sashe 45

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a Salma, Abiy baya so, ya ce min na cire Omaar daga raina. Mama ce taka bani ƙarfin guiwa akan zai amince min na cigaba da haƙuri. Ni dai na san na tafi Kano ban tambaye shi ba amma daga nan ban san me na aikata ba. Kuma Mama ce ta saka na tafi, na nuna bazan je ba tace naje zan fi samun hutu." Salma tayi ajiyar zuciya ta ce, "To ki daina kuka, tunda ke kin san baki yi komai ba ko ma meye zai bayyana in sha Allah."

Nayla ta ce, "Salma Abiy fushi yake yi dani."
"Zai daina in sha Allah."
"Ya aura min Omar, ya aurar dani ga wanda baya so, ya aurar dani ba tare da sanina ba."
"Shi Omar ɗin ya sani?."
"Wallahi ban sani ba, ban sani ba Salma. Ban san Ina zan saka kaina na ji daɗi ba." Salma ta ce, "is okay, ki daina damun kanki kinga baki da lafiya."

Ɗan buga ƙofar akayi tare da shigowa. Abiy ne ya shigo da kansa ganin Salma sai ya yi murmushi ya ce, "A'a Salma, saukar yaushe?." Salma ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta su Hajja ta amsa masa kafin ya ce, "Ya jikin Naylan?." Salma ta ce, "har yanzu da zafi a jikinta Abiy."
"Zata warware in sha Allah. Kin zo a kai amarya Kano dake kenan, ai kin kyauta." Salma ta kalli Nayla da itama ita take kallo.

Abiy ya kalli Nayla ya ce, "me yake damunki?." Maimakon ta bashi amsa sai ta fashe da kuka. Abiy ya ce, "ba kuka nace kiyi min ba, me yake damunki?." Nayla ta goge ido ta ce, "ciwon kai."
"Ki daina kuka shima zai daina." Kai ta ɗaga alamun to ya buɗe ƙofar ya fita.

Nayla ta ce, "kinji ko? Wai kinzo a tafi dani Kano ya ce, Salma na shiga uku!." Salma ta ce, "baki shiga uku ba Nayla, ko meye zaizo da sauƙi in sha Allah. Ki kwantar da hankali ki komai zai warware, ki cigaba da addu'a komai zaizo da sauƙi." Rarrashinta Salma ta dinga yi har ta ɗan saki jiki suna hira hakan ya yiwa Salma daɗi a haka har dare yayi.

           Washe gari.

Saboda rashin lafiya Nayla bata iya tashi da azumi ba duk da ta saba duk sati amma baza ta iya ba. Salma ce ta ke tsaye akanta akan cin abinci da shan magani ita kam gabaɗaya ta zama wani iri. Jawad ma ya sakko yana bibiyar lamarinta da jin ya ta kwana, ita kam gabaɗaya bata su take yi ba, fushin da mahaifinta yake yi da ita ya fi komai ɗaga mata hankali.

Suna zaune a falo Abiy ya fita ita da Mama da Salma da kuma Jawad. Mama ta ɗauki waya ta kira Didi bayan ta ɗauka sun gaisa ta ce, "Aisha Ina ta jiran kiran ki, ya maganar mu?." Didi ta ce, "kiyi haƙuri Mama, sai dare naje na duba gidan ne shiyasa. Falo ne guda biyu, babba ɗaya sai ƙarami ɗaya, sai bedrooma guda biyu."
Mama ta maimaita abinda Didi ta ce sannan ta ce, "kitchen fa?."
"Akwai kitchen da store, kitchen ɗin babu laifi yana da ɗan girma."
"To ma sha Allah, zan fara aiko da kayan in anjima, zan bawa driver number ki sai kiyi musu kwantace a kai gidan. Zan aiko da masu ɗaura kayan duk sai ki yo musu bayani."

Didi a sanyaye ta ce, "to Mama." Mama ta ce, "Sai sun zo" ta faɗa tana yanke wayar. Nayla da Salma duk suna jin abinda yake faruwa, Nayla ta miƙe ta hau sama Salma ma tabi bayanta. Jawad ya kalli Mama ya ce, "Mama don Allah meyasa kika fi mayar da hankali akan kayan ɗakin Nayla? Auren nan kowa ba so yake yi ba, amma hankalinki gabaɗaya yana ga a kai kayan Kano."

Mama ta ce, "umarnin mahaifinku ne, zan canja hakan ne?."
"Amma Mama shi kansa Abiy ɗin ya ɗan sauka saboda rashin lafiyar Nayla, amma gabaɗaya ke ta ta kayan ma kike yi." Mama ta kalle shi kamar zata yi magana sai ta fasa kawai ta tashi ta shiga ɗaki.

Nayla kuwa bayan sun shiga ɗaki kallon Salma tayi ta ce, "Wai kayan aurena ake zance Salma, wallahi komai ya fita daga raina, son Omar ɗin ma na neme shi na rasa." Salma ta ce, "ki yi haƙuri ki cigaba da jurewa. Amma sai naga kamar Mama murna take yi da auren nan. Ki yi haƙuri ina faɗar hakan a kanta, amma daga jiya zuwa yau na fahimci kamar ita so take yi."

Nayla ta ce, "meyasa zata so? Kawai umarnin Abiy take cikawa." Salma ta yi shiru bata ce komai ba amma a zuciyar ta gabaɗaya bata amince da Mama ba, gani take yi kamar da biyu take yin abinda take yi. Duk da ta san Maman bata da wani aibu da hali mara kyau, amma zuciyarta ta dasa mata ayar tambaya akanta.

••••••

Abiy kai tsaye da ya shiga Kano gidan Daddy ya nufa kamar yadda yayi masa waya ya sanar dashi yana hanya. Daddy ya karɓe shi hannu biyu da girmamawa aka tarbe shi da ruwa da kuma abinci. Ya sha dai ruwa amma bai ci komai ba yana zaune a falo shi kaɗai an barshi ya huta. Sai da ya ɗan jima da zuwa sannan Daddy da Abba da Baba suka shigo a tare gabaɗaya.

Sake gaisawa aka yi kowa yana tambayar iyalan kowa kafin Daddy ya ce, "Alhaji Abdullahi mun ji batun aure kwatsam babu shiri, hankalin mu gabaɗaya ya kasa kwanciya musamman da kace zaka zo kayi mana bayani." Abiy ya ce, "ni kaina ban shiryawa auren ba, yazo ne lokaci ɗaya dole na karɓe shi."

Abba ya ce, "Amma me ya kawo shi?." Abiy ya ce, "Nayla tana son yaron, son da take masa ne ya saka ta koma kamar ba ita ba, kullum a rashin lafiya take, kullum a cikin damuwa. Da fari ban fahimta ba, amma daga baya da aka sanar dani sai na fahimci hakan. Na kira Nayla akan hakan ta tabbatar min da tana sonsa. Ni na faɗa mata ban damu da kuɗin namiji ba, abinda nake nema a ko yaushe hali na gari da kuma inda yaro ya fito. A take da na kirata na yanke alaƙar batun yaron, na ce ta cire daga zuciyarta, sannan a cikin masu neman aurenta tabbatar da ta fitar da guda ɗaya."

Abiy ya ce, "ta amsa min kamar da gaske take, na sake maimaita abinda nace amma sai na wayi gari Nayla ta taho Kano. Duk da ban sani ba kuma bata taɓa fita wajan Kaduna ba tare da na sani ba balle tazo Kano, ko aiki zata taje sai ta faɗa min saboda haka tsarina yake a haka suka tashi. Na yi  mamaki da naji labarin bata nan amma nuna ba na share ta. Ina nan zaune sai ga wannan saƙon ya shigo wayata Nayla ta turo min" Abiy ya faɗa yana ɗauko waya ya shiga number Nayla ya miƙawa Daddy.

Sai da ya jira ya gama karantawa kaf ya bawa Abba da Baba duk suka karanta duka messasges ɗin sannan Abiy ya ce, "raina ya ɓaci gaskiya akan hakan sosai, ban kuma yi tunanin zata aikata haka ba. Nan take na yanke hukuncin aura mata shi tunda haka ta zaɓa, kuma tunda har take irin wannan furucin akansa aura mata shi shine mafita kar a zo a haifar da ɗa mara ido. Wannan dalilin ne ya saka na aura mata shi a lokacin da nake tsakiyar ɓacin rai, daga baya naji kamar ban kyauta mata ba amma na riga da na aikata."

Daddy ya girgiza kai ya ce, "Tabbas Nayla bata kyauta ba, ko waye a matsayinka dole ransa ya ɓaci ya aikata fiye da abinda ka aikata saboda abinda ta aikata. Amma Alhaji Abdullah anyi aikin gaggawa, Nayla yarinya ce ƙarama, soyayya zata iya sakawa tayi wannan furucin ba tare da ta sani ba. Wataƙila da ka sake bata dama da hakan bai faru ba."

Abiy ya ce, "Eh to ba nace ba, ni a wajena hakan da nayi shine daidai tunda shi ta zaɓa take ganin zata iya zama dashi, ni a wajena na bata shi a matsayin wanda take son kuma zaɓinta." Baba ya ce, "ni babban abinda yake damuna akan auren nan ba komai ba ne face halin yaron, inda ace mutum na gari ne kamar kowa sai mu yi fatan Allah ya sanya alkhairi tunda kowa yasan matar mutum kabarinsa. Amma kowa ya san sunansa ba ta hanyar kirki ba, in na tuna hakan sai naji komai Nayla zata aikata bata cancanci a yanke mata wannan hukunci ba gaskiya, Alhaji Abdullahi."

Abba ya ce, "Shi yaron ya san da auren?." Abiy ya ce, "ban sani ba ko yanzu ya sani." Ya girgiza kai ya ce, "Mahaifinta ne kai kana da ikon yanke hukunci a kanta fiye da kowa, amma duk da haka baza mu fasa faɗa maka gaskiya ba, koda ba Nayla ka yiwa haka ba in muka ji labari zamu faɗa maka tunda an zama ƴan uwa. Ba dan muna yayyen mahaifiyarta muke faɗar baka kyauta ba, muna faɗa maka ne a matsayin ɗan uwan mu. Gaskiya ka yanke hukunci cikin fushi da ɓacin rai, in da an bi wata hanyar ba wannan ba da wataƙila hakan bai faru ba."

Abiy yayi ajiyar zuciya ya ce, "Haka Allah ya shirya, amma har zuciyata a yanzu bana jin ban kyautawa Nayla ba." Daddy ya ce, "Shikenan Alhaji. Amma yana da kyau a zauna da yaron aji shi yana da ra'ayin zama da ita, in yana dashi shikenan tunda tana sonsa sai mu ce Allah ya basu zaman lafiya, in kuma bashi da ra'ayi zata sha wahala a zama dashi gaskiya. Kuma ga yanayin da muke ciki a wannan zamani na cututtukan da ake ɗauka, ana gwajen-gwajen jini yanzu kafin aure dan tabbatar da lafiyar su shida ita, haka za'a kaita ba tare da a san matakin jininsa da abinda yake ciki ba?."
Chapter 45 · 0% Book details