← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 52

Sashe 13

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sen ya taɓe fuska ya ce, "Allah ya kiyaye, Jahili ne fa ko secondary school bai gama ba. Ina zai iya kaiwa a rayuwa babu ilimi?." Abiy ya ce , "ni dai ayi min alfarma a bani shi." Sen ya yi shiru yana tunani, bazai iya ƙin yiwa Abiy alfarma ba saboda mutuncin da yake tsakanin su. Amma in ya tuna wulaƙancin da Omar ya yi masa sai yaji bazai iya bada shi ba.

Senator ya ce, "Shikenan, za a ƙyale shi gobe. Amma saboda kai ne kawai babu yadda zan yi maka, amma wallahi da sai ya ƙare rayuwarsa haka." Abiy ya yi dariya ya ce, "godiya nake mai girma Senator kuma sirikin Gov, future Kano state gov in sha Allah." Dariya suka yi aka share zancen suka cigaba da hira har bayan sallar la'asar kafin kowa ya watse.

Kasancewar ranar ne dinner ɗin Shayida su Nayla suna gida su ukun a falo suna ta jan Nayla da hira amma ta kasa sakewa. Abiy ne ya shigo falon duk suka miƙe tsaye ya kalle su da murmushi suka gaishe shi ya amsa kafin ya kalli Nayla ya ce, "Mamana kina lafiya kuwa?." Nayla ta ce, "lafiya lau Abiy, ciwon kai ne tun na jiya har yanzu."
"Kwana biyu ciwon kai yana damunki sosai, ki je asibiti mana."
"Wallahi stress ne aiki na kawai Abiy, da nayi bacci na tashi sai na dawo daidai."

Abiy ya yi dariya ya ce, "kaga sabuwar ma'aikaciya." Tayi dariya Abiy ya zauna yana cewa, "ƙarfe nawa zaku tafi Kaduna gobe? Ni sai jibi monday zan dawo in sha Allah ." Nayla ta ce, "Duk lokacin ka ce Abiy."
"Saboda aikinki dole a koma gobe gaskiya, zamu gani zuwa azahar sai ku tafi in Allah ya kaimu."

Bata yi magana ba ya kalle ta ya ce, "Maganar ɗan daban yaron nan." Ai da sauri ta ɗago tana kallonsa a lokacin Mama tazo ta zauna a wajan. Abiy ya ce, "Mun yi magana da Senator..." ya faɗa yana duba waya wacce saƙon text ya shigo. Shiru ya yi bai yi magana ba yana duba wayar. Nayla ji take kamar ta ƙwace wayar daga hannunsa saboda ya kai ga faɗa mata abinda zai ce.

Abiy ya ajjiye wayar ya ce, "mun yi magana ya kuma amince zai ƙyale shi, gobe ma ya ce zai sake shi ya dawo gida in sha Allah." Wata irin ajiyar doguwar zuciya Nayla tayi, ta lumshe idanu tana jin wani irin daɗi na ratsa zuciyarta. Abiy ya bita da kallon mamaki ganin yadda farin ciki ya bayyana a tare da ita kamar itace Yayar ta sa. A hankali ta buɗe ido suka haɗa ido da Abiy da yake kallonta, da sauri ta sunkuyar da kai amma murmushi take yi. Abiy ya ce, "ko dai kema ƙanwarsa ce ne Nayla? Wannan ajiyar zuciya haka kamar Jawad aka kama za a saki?."

Murmushin yaƙe tayi ta ce, "Abiy kawai Ina murna ne in na tuna yadda Didi zata yi murna." Abiy ya zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma kafin ya ce, "kin tabbata?." Sai taji tsoro ya shige ta da tunanin Allah yasa bai gane wani abun ba. Ta sake sunkuyar da kai tace, "Eh Abiy."

"To ya yi. Ki sanar mata gobe zai dawo in sha Allah." Da farin ciki ta amsa shi kuma ya tashi ya shiga ciki Mama ma tabi bayansa. Nayla na shiga ɗaki sai gata ta fito da key ɗin motar Mama, Salma da Jidda suka kalle ta kafin su magana ta ce, "Gidan Hajja zan je, in zaku je kuzo mu tafi." Salma ta karɓi key ɗin hannunta tace, "bani baza ki sake ƙoƙarin kashe mu ba." Bata ma ji ba tayi gaba burinta kawai taje ta faɗawa Didi. Salma ce ta ja motar suka tafi gidan Hajja.

Nayla na shiga ta tarar da Didi ita da AbdulHamid suna tsaye da alama sallama yake yi mata. A guje ta faɗa jikin Didi ta ce, "Didi Abiy ya yi magana da Senator ya tabbatar masa da gobe zai dawo, gobe zai dawo Didi" ta faɗa da murna sosai. Didi cikin farin ciki ta ce, "da gaske ki ke? Da gaske ki ke Nayla?."
"Da gaske nake Didi." Didi ta ce, "Alhamdulillah! Allah na gode maka, Allah na gode maka" ta faɗa tana sake rungume Nayla da take dara saboda murna.

"Na gode Nayla, na gode Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya baki miji na gari." Ciki suka shiga dan Didi ta manta da AbdulHamid da yake wajan. Sai da suka shiga falon Hajja Salma ta ce, "Amin Didi. Dan wallahi itace jiya ta samu Abiy tana kuka kamar zata mutu saboda a fito da Omar, yadda muka bar gidan nan jiya baki ga gudun da ta dinga yi damu a mota ba saboda kawai take ta samu Abiy. Cikin ikon Allah tana faɗawa masa ya kira shi a waya ya ɗauka, yau suka haɗu ya yi masa maganar ya kuma amince" Salma ta faɗa tana kallon Didin da ta san aikin Nayla ne yadda ko Omar ɗin ya fito ya san ita tayi masa hanya ya fito.

Didi ta sake riƙe Nayla tana godiya tana hawaye tana cewa, "na gode Nayla, Allah ya bani abinda zan saka miki Nayla. Na gode sosai." Hajja ta ce, "itama ai ta saka alkhairin da ya yi mata ne Aisha, kin manta abinda ya yi mata?." Didi ta ce, "ban manta ba Hajja, amma wannan taimakon da tayi min ai baza ki haɗa shi da wancan ba. Ta ceci rayuwata ta ceci ta Omar, bani da abinda zan saka mata saka addu'a."

Hajja tayi dariya dan ko ita ta ji daɗin labarin dawowar Omar. Didi ta ce, "Nayla mu je na yiwa Abiy godiya, mu je yanzu in yana gida." Hajja ta ce, "A'a Aisha, ki bari ya dawo sai ku je ku same shi tare." Didi ta ce, "Amma ya kamata na je yanzu kafin ya dawo ko?." Nayla ta ce, "to sai mu je in anjima, ko kuma ki yi masa waya."

A nan suka baje ana ta hira da nishaɗi Didi ji take kamar ta mayar da Nayla ciki saboda son da take yi mata. Sai bayan i'sha suka tafi saboda dinner da zasu je, tare da Didi aka je ta yiwa Abiy godiya ya ce babu komai. Drivern Hajja ne ya dawo da Didi su kuma suka fara shirin dinner. Ko a wajan dinner kowa ya lura da walwalar da Nayla take yi, su dai su Salma fatan samun sasssuci akan abinda yake damunta suke yi mata.

Washe gari ranar lahadi ƙarfe goma na safe ta fita daga gida zuwa gidan Hajja. Ta samu Didi ma bata nan ta shiga gida tana aikace-aikace Saboda dawowar Omaar. Salma ce ta shigo tana cewa, "shine ko ki jira ni kika taho bayan kin san Jidda tana gidan ta." Nayla ta ce, "to ba gashi kin zo ba. Matsa min naje gidan Didi." Salma ta ce, "ba da wuri Abiy ya ce zaku koma ba ne? Yana ta faɗa ya ce kin san zaku tafi Kaduna ki ka fito yawo."
"Kin ga Ina zuwa" ta faɗa tana fita ta shiga gidan Didi Salma na biye da ita.

Lokacin da suka shiga Didi share ɗakin Omar take yi, jin sallamar Nayla ya saka Didi ta ce, "Nayla gani nan, shigo." Nayla gabanta ya faɗi matuƙa, ta kalli Salma da take tsaye sai Salma tayi tsaki ta shiga ɗakin.

Nayla ta shiga ɗakin a sanyaye da sallama gabanta yana faɗuwa, ɗaki ne babba mai girma dan yafi na Didi girma. Babu tarkace a ɗakin babbar katifa ce mai girma da tudu, sai wardrobe mai guda shida a gefe, sai mirror mai irin wardrobe ɗin a gefe wanda abubuwan da suke kansa basu wuce guda biyar ba.

Didi ganin Nayla sai ta yi murmushi ta ce, "Nayla har kin fito?."
"Wallahi na fito Didi. Kin san fa yau zamu wuce Kaduna." Didi ta ce, "wallahi duk sanda ki ka zo bana so ki dinga zancen zaki koma Kaduna ɗin nan, bana jin daɗi ko kaɗan.." Nayla tayi dariya tana cigaba da kallon ɗakin da sai ƙhamshi turare yake yi mai sanyi.

Didi ta ce, "Ina gyara ɗakin mutumin naki, in ba haka ba in yazo da faɗa zamu fara kin san baya ƙaunar ƙura ko kaɗan. Zai iya zama wajan da aka zubar da kaya amma bazai iya zama a waje mai ƙura ba. Shiyasa yake gyara ɗakinsa ko yaushe, dan shi baya jin gyaran ɗaki." Salma ta girgiza kai ta ce, "Ga ɗakin nan tsaf dashi kamar ba na maza ba, har so nake na shigo dan naga ƙazantar da take ciki ashe ɗan gayu ne."

Didi ta yi dariya ta ce, "Ai baya shiri da waje kaca-kaca, kinga tsintsiyarsa a ajjiye ga dustbin"
Didi ta faɗa tana nunawa Salma amma Nayla ce ke gani. Salma ta ce, "shikenan ya huta, ko ya yi aure babu ruwansa da sai an gyara masa ɗaki."

Nayla sai murmushi take yi tana kallon ɗakin tana jin farin ciki a zuciyarta. Fita suka yi zuwa falon Didi bayan ta gama gyarawa har da fesa airfreshner. A falon suka zauna suna ta hira Nayla sai kallon ƙofa take yi amma babu alamun Omar ko kaɗan.

Duk ta damu ga rana tana yi lokacin tafiyar su yana gabatowa. Suna zaune har azahar tayi Omaar bai dawo ba, a lokacin kiran Abiy ya shigo wayarta tana ɗauka bai jima yana magana ba ya kashe, Nayla ta kalli Salma da Didi ta ce, "Didi zan je gida zan haɗa kayana zan wuce, sai dai na ce sai na dawo wani lokaci. Wataƙila ma sai bikinki" ta faɗa tana kallon Didi.
Chapter 13 · 0% Book details