← Book details Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 52

Sashe 27

Kiran Rabo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta girgiza kai ta ce, "to naji, nutsu mu yi magana." Nayla tayi ajiyar zuciya Mama ta ce, "kuma zaki iya aurensa a yanayin da yake ciki?." Nayla ta sauke jiyar zuciya t ce, "Mama bana kawo hakan a zuciyata gaskiya."
"Ina tambayarki, in kika samu dama zaki aure shi?."
"Mama ai bazan samu ba ma." Mama tayi murmushi ta ce, "ki amsa min tambayata mana, in kika samu dama zaki iya auren shi?." Nayla ta ɗaga kai alamun eh tana kulle idanunta.

Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan share hawayenki zan taya ki da addu'a, sannan zan san yadda zan yi Abiy ya amince da aurenki da Oamar." Da sauri ta kalli Mama cikin tsoro Mama ta ɗaga mata kai ta ce, "kar ki damu, zan tabbatar da kin samu abinda kike so kedai ki bani haɗin kai kar ki bani kunya. In mahaifinki ya ji maganar ya tambayeki kar ki ce masa a'a, ki faɗa masa abinda yake zuciyarki, mahaifinki yana sonki kuma na tabbatar da zai amince da abinda kike so. Sannan duk abinda nace kiyi, ta haka ne zaki samu cikar burinki."

Nayla kallon Mama kawai take yi amma a zuciyarta tana jin kamar hakan bazai yu ba. A sanyaye ta ce, "Mama hakan zai yu kuwa? Ni da zaki bar maganar kawai zan haƙura na ɗauki mutum ɗaya a cikin wanda Abiy ya ce na aure shi."

"Haka zaki zauna da wanda bakya so? Gangar jikinki fa kawai ya aura zuciyarki na tare da Omar. Baza ki iya yi masa biyyaya ba saboda ba shi kike so ba, ke kin san auren wanda baka so kuwa? Ko me mijinki zai miki bazai burge ki ba, tunanin Omar kawai zaki dinga yi kina ɗaukarwa kanki zunubi." Nayla ta ce, "To Mama ya zanyi? Abiy bazai amince ba."

Mama ta ce, "zai amince. Kin san mahaifinki ba kuɗi ne a gabansa ba, bai saka a zuciyarsa lallai sai kun auri masu kuɗi ba, tunda kina aikin ki kuma kina da shago wannan bazai dame shi ba. Kuma in ya so zai iya mayar da Omar yadda yake so, yana da dukiyar da zata azurta Omar. To mahaifinki ba haka yake so ba, ba gidan kuɗi yake burin aurar daku ba, a riƙe masa yarinya kawai shi yake buri da ra'ayi."

Nayla ta girgiz kai ta ce, "ni dai Mama tsoro nake ji." Mama ta ce, "ki daina jin tsoro ina tare dake, Ke dai kiyi duk abinda na ce zaki mallaki Omaar in sha Allah." Nayla ta ce, "Mama ɗan daba ne fa, taya Abiy zai amince?."
"Da ya ke ɗan daba ai, ba naji kuna waya da Salma tana tabbatar miki har shago ya buɗe na sana'a ba?." Nayla ta ɗaga kai ta ce, "eh Mama."
"To kar ki damu, labarinsa na baya ya wuce labarin yanzu ake yi. Kedai ki kwantar da hankalinki, wannan kukan ne bana so na ga kina yi, bana so na ganki cikin tashin hankali. In mahaifiyarki na raye na tabbatar zata yi duk abinda zata yi wajan ganin farin cikin ki, to nima haka take a wajena. Kar ki damu zan san abinda zan yi dan ganin kin yi farin ciki."

Faɗawa jikin Mama tayi ta rungume ta yana hawaye, Mama tayi murmushi tana shafa bayanta tana murmushin da ita kaɗai ta san manufarsa, dan wannan dama ce da ta jima tana nema yanzu tazo mata cikin sauƙi. Ta ɗago ta daga jikinta ta shafa fuskarta ta ce, "ki kwantar da hankalinki, Ina tare dake a ko yaushe." Nayla tayi murmushi cikin farin cikin da take ji a zuciyarta ta ce, "Na gode Mama." Mama taja hancinta ta miƙe ta fita ta bar Nayla na murmushi ita kaɗai kamar zararriya.

Mama tana fita daga ɗakin tayi dariya ta ce, "Nayla kenan, na samu dama a hannuna ba tare da na sha wahala ba zan aikata duk abinda zan aikata. Zan tabbatar da na yi abinda nake so cikin sauƙi ba tare da tashin hankali ba. Mu je zuwa" ta faɗa tana murmushi ta bar ƙofar ɗakin zuwa ɓangaren Abiy.
[23/09, 7:33 pm] +234 810 686 6659: KRB2P016

Da sallama Mama ta shiga ɓangaren Abiy yana zaune yana duba littafi a hannunsa, ya kalle ya amsa yana cigaba da duba littafin. Zama tayi ta ce, “A kawo kunun gyaɗar?.” Abiy ya ce, “A’a barshi sai anjima. Ya kuka yi da Nayla?.” Mama tayi ajiyar zuciya ta gyara zama ta ce, “yanzu muka gama magana da ita.” Abiy ya kalle ta ya ce, “to Ina jinki.” Mama ta ce, “Abiy ka ƙara mata lokaci saboda yanzu….” Ya katse Mama ya ce, “kamar ya na ƙara mata lokaci, wanne irin lokaci yake so na ƙara mata?. Auren ne bata so ko me?.”

Mama ta ce, “A’a ba haka bane…” Nan ma ya katse ta ya ce, “to yane? Faɗa min waye zaɓin taa cikin mutane huɗu?.” Mama ta kalle shi ta ce, “babu wanda take so a cikin su.” Abiy ya ajjiye littafin hannunsa ya kalli Mama da mamaki ya ce, “babu wanda take so a cikin fa ki ka ce? duka mutane huɗun babu wanda ya yi mata?.” Mama ta ɗaga kai ta ce, “babu, shiyasa nace maka tana buƙatar lokaci.”

“Wannan ma ai shirmen banza ne da wofi, dan tsabar rainin hankali samari har huɗu ta ce babu wanda take so a ciki dan ta raina ni ta mayar dani ƙaramin mutum?. Mtsw!” Yaja ƙarmain tsaki yana ɗaukar waya ya saka a kunne ya ce, “Nayla zo falon sama ki same ni.”

Nayla da ta samu kiran Abiy gabanta ya faɗi tsoro ya mamaye zuciyarta kar taje Mama ta faɗa masa halin da ake ciki. A sanyaye ta nufi ƙofar da zata kai ta falon sa na sama, ta shiga da sallama ya amsa yana kallon ta. Yanayin fuskarsa da take a ɗaure ya saka ƙirjinta cigaba da bugawa, ta taka a sanyaye ta shiga ta zauna a akan carpet ta ce, “Abiy gani.” Ya kalle ta ya ce, “Naji saƙonki akan samarin da suke naman aurenki, ki ka ce babu wanda kike so a cikin su?.”

Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba. Abiy ya ce, “ke nake saurare.” Nayla ta yi gyara zama nan ma bata ce komai ba. Abiy ya ce, “magana nake miki, da gaske babu wanda kike so a cikin su?.”

Ta ɗaga kai alamun eh, yayi tsaki a ɗan fusace ya ce, “magana zaki yi min!.” Murya a sanyaye ta ce, “E Abiy.”
“To wa kike so?.” Gabanta ya faɗi ta sauke kanta ƙasa bata ce komai ba. Abiy ya sake cewa, “In ina tambayarki kina yi min shiru ranki ne zai ɓaci. In bakya sonsu wa ki ke so?.”

Nayla ta ce, “Babu kowa Abiy.” Abiy ya ce, “to ki tabbatar da kin samu wanda zaki so a cikin kwana biyu, na baki nan da jibi kizo ki faɗa min wa kika ɗauka a cikin su in ba haka ba zan aura miki duk wanda naga dama. Na gaji da wannan shirmen naki, gabaɗaya kin canja kin koma wata shiru-shiru, da kin dawo daga aiki kika shiga ɗakin bakya fitowa. An tambaye ki damuwarki kinƙi faɗa, likita ya ce kina da damuwa amma kin ƙi faɗar abinda yake damunki. Dan kinga na ƙyale ki shine kuma zaki kawo min iskanci? To baki isa ba, nan da jibi ki tabbatar da ko ma waye kin zaɓa an sanar dani in ba haka ba kuma ranki zai ɓaci wallahi. Na gaji da lallaɓaki, yau ciwon kai, gobe zazzaɓi, jibi ciwon ƙirji. Dan kin raina mu kuma kin kalle mu kince baki da damuwa.”

Nayla jin Abiy yana faɗa abinda ba sosai yake yi ba sai tayi sanyi ta ce, “Kayi haƙuri Abiy.” Abiy ya ce, “Nayi yanzu, amma ki sani jibi bazan yi haƙurin ba.”
“To Abiy.”
“Tashi ki bani waje.” Ta miƙe a sanyaye ta fita cikin rashin sanin abinda zata yi.

Ya kalli Mama ya ce, “ke kike goya mata baya take abinda take so, ki faɗa mata wannan karan bazan ɗaga mata ƙafa ba wallahi, na gaji da wannan yazo tace bata so dole ta zaɓi ɗaya daga a cikin waɗanan huɗun in ba haka ba ni zan aurar da ita ga wanda nake so.” Mama ta ce, “in sha Allah hakan bazai faru ba, zan mata magana in sha Allah.”
“Ya fi muku” ya faɗa yana ɗaukar littafin da ya ajjiye yana cigaba da dubawa.

•••••••

Narma tunda lokacin da suka sauka a Texas cikin ƙasar America tana yadda take bata canja ba, ko yaushe tana cikin ɗaki a zaune tana aukin tunani ko magana ba ta haɗata da Ashraf. Shi kuwa yana sane ya ƙyaleta dan ta ɗan nutsu amma yaga abin nata ya yi yawa haƙurinsa ya fara ƙarewa, ko magana bata yi masa balle ya saka ran wani abun daban.

Kamar ko yaushe tana sanye da ƙaramar riga iyakar ta guiwa mai siririn hannu tana kallon taga, kasancewar lokacin snow ne ko Ina a garin ya lulluɓe da ƙanƙara sanyi yayi yawa sai da taimakon wood stove da take ɗumama ɗaki. Shigowa Ashraf yayi ya kalle ta tun daga gashin kanta da yake a buɗe har ƙafar ta da take sanye da room slippers.

Abinda ya saba ji a kanta yaji yana jansa zuwa gareta, a hankali yake takawa inda take har yazo daf da ita ya leƙe kansa ta kafaɗarta yana kallon window ɗin da take kallo. Hannunsa ya saka ya riko cikinta ya jawo ƙugunta ya haɗa shi da jikinsa yana kallon gefen fuskarta. “My love tunanin me kike yi?” Ya faɗa a kunnenta yana kallon fuskarta. Bata motsa ba dan Omar ɗinta take tunani har lokacin zuciyarta ta gaza karɓar Ashraf a matsayin mijinta, Omar ɗin dai shi ne a zuciyarta.
Chapter 27 · 0% Book details